← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 40

Sashe 11

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🅿️11
📝A washe garin ranar asabar Yasir yana dawo wa daga masallacin sallar asuba yaga kiran Abban su ya shigo wayar shi,cikin azama yayi picking a ranshi yana tunanin ko lafiya".
Cikin girmama wa ya gaishe shi Dady bayan ya amsa ya dora da "Magaji yau ka zo Ina san magana da Kai"
"To Abba insha Allah ganinan shigowa". Katse Kiran yayi yana sauke numfashi domin kuwa yasan da ya ji irin wannan Kiran yasan fada ne zai sha,da wannan tinanin ya shige part din shi.

Dan Farrah kuwa tunda tayi sallah ta koma ta yi kwanciyar ta.

Karfe 10:00 daidai ya fito cikin Shirin shi na yadin cufta brown color ya dora hular shi takalmin shi black,Yana daura agogo a tsintsiyar hannun shi ya nufi part din Momy da sallama dauke a bakin shi.

Ba kowa a falon sai sanyin iskar A/C da yake kadawa.zama yayi saboda ya ji kaman motsin mutum a kiching.Momy ce ta fito tana kokarin jera break a Kan dinning,bayan ta gama karasowa falon tayi,kasa ya sauko Yana ce wa "Momy Ina kwana".
Ba yabo ba fallasa ta amsa mai,hakan yasa ya sha jinin jikin shi.cikin sanyin jiki ya mike,"Momy bari inje GRA Abbah yake kirana."ka yi break Mana kafin ka tafi"?
"Naga lokaci ya kure bari kawai na je a can zanyi".

"Tau ka gaishe su" cewar Momy a zuciyar ta tana ce wa ni bazan kara yima magana ba zan ga iya gudun ruwan ka.

Cikin sanyin jiki ya nufi gidan iyayen nashi,a hankali yake tukin har ya karasa gidan.

Mai gadi ya bude mashi ya yi parking din motar shi wurin da aka tana da dan adana motoci,Yana fitowa ya ga Jabir Yana fitowa da ga site din su ya nufo cikin gidan.Ba tare da ya kula shi ba ya shiga cikin shima ya wuce cikin gidan.A falon ya yadda su gaba dayan su suna break,Dan haka cikin sallama ya karasa Sallamar kawai suka amsa dan haka shima ya ja kujera ya zauna,Dan yasan dokar gidan ce idan ana cin abinci ba'ayin magana.

Bayan sun kammala break din Dady ya fara mikewa shima yabi bayan sa zuwa babban falon nasa,Bisa kafet din da yayima falon kawanya ya yima kansa masauki tare da tonkwashe kafafuwan sa.gyaran murya Dady yayi tare da Kiran sunan sa "Magaji nasan kasan dalilin da ya saka nayi Kiran ka ko?, Ba sai na Kara maimaita wa ba dan haka maganar da mukayi da Kai Ina ta kwana?.

Shiru yayi yana Kara sadda kanshi kasa.
"Da Kai nake magana kayiman shiru?.
"Am ehmm Dady Dan Allah ka Karaman wani dan lokaci insha Allah zan kawo".

"Ai na saba jin wanan kalmar da ga bakin ka ba tun yau ba,to wallahi ka saurare ni da kyau wannan shi ne magana ta karshe da zan yima akan lamarin kayi aure,yanzu kai ko kunya baka ji shekarar ka kusan nawa, Amma kana zaune ,Kuma idan ka koma aiki gobe na Kara ganin keyar ka a garinnan wallahi zaka gamu da fishi na,kafi son kayi ta yawo yau kana nan gobe kana abuja ko?.
Ya dora da,"sannan the last one jiya duk rashin mutumcin da kayiwa Yan uwan ka ya dawo Kan kunne na,Dan haka ka kyauta".

Shi dai har zuwa wannan lokacin bai ce kala ba.Dady kuwa ta inda ya shiga batanan yake fita ba,sai da yayi mai tas sosai ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba.A karshe ya dora da Kuma ka saurari hukuncin da zamu yanke da dan uwana ya dawo,ta shi ka bani wuri.

"A hankali ya furta Allah ya huci zuciyar ka"Yana mikewa,wurin motar shi ya nufa ko sallama bai yiwa Ummah ba ya figi motar shi da mugun gudu ya fita da ga gidan.

--------------------------
A bangaran Farrah tunda ta fito ta yi break ta koma bedroom dinta,dan haka Momy ta kyale ta bata ce mata komai ba saboda tasan tana bukatar hutu da dogon nazari.

Sosai Jabir ya ji dadi,Dan yana shigowa Auta umar (Abba)ya labarta mai zuwan Yaya Yasir amma besan fadan me akayi mai ba yaga dai ya fita daga gidan ranshi a bace."Hmm Allah yasa idan ya tafi yayi shekara bai zo garinnan ba ni nasan kafin nan insha Allah anyi bikina da matar ka ga shikenan,Dan ni wallahi ban yarda da shi ba Yana takura mana, Auta umar yayi ta dariya.

*************
Yasir Yana fitowa da gudu darect wayar abokin shi ya Kira Bishir ya tambaye shi su hadu a wurin wani shakata wa.Haka ko aka yi Yana zuwa shima ya karaso.

Yasir shiru yayi ba tare da ya ce komai ba sai huci da yake faman yi kaman Wanda yayi gudun tsere.Da Bishir yaga shirun yayi yawa ya ce "wallahi kaifa dan iska ne yaushe zaka Kira ni Kuma ka saka ni a gaba kana kallo na,tell me me yake faruwa"?.
Sai a sannan ya samu damar magana "Dan Allah ka bani shawara me ya kamata inyi,wallah i so suke su raba ni da ita ,duk cikin kwanakin nan Ina cikin tashin hankali".

"Hmmm Yasir kenan wallahi ka bani mamaki,Ai dole zaka rasa nutuwar ka,kaida kanka kasan dole zata rinka tosran ka hmmm sai ta tona maka asiri a wurin su Dady a sannan zaka gane kuranka",haba haba ka dawo cikin hayyacin ka Mana".

Sosai ya nutsu Yana kallan abokin nashi.

"Amma Bishir kasan nayi ma bayanin ba laifina bane sharrin zuciya ne,to wallahi yanzu kwata-kwata tsorona take yi,Amma abu daya yasa nake jin karfin gyuwa ina hango soyaya ta a cikin kwayar idanun ta duk da ita kuruciya ta sanya ta kasa fahimtar haka".

"Ok ita ma ai duk a cikin kuruciyar ne ta kasa manta yanda ka rinka mammatse ta," ya karasa fada Yana nuna shi da hannu,cikin dariya ya Kara ce wa "wallahi freind Kai dan rainin hankali ne ,idan na fahimce ka shiyasa kake tunanin tana tare da wasu samarin ko? To Ina mai baka shawara da ka kyauta ta zato gare ta ka daina zarginta,Duk da muna cikin wani zamani mai wuyar sha'ani amma akwai yanmatan da ba ruwan su harga Allah Dan baza'a taru a zama daya ba.m".

Yasir ya kule sosai cikin jin haushi ya ce "ban San wulakanci Bishir ban ce ka tasa ni a gaba ba kana yiman dariya,shawara nake bukata ko nayi tafiya t".

"Hmmmm to sorry man ba ni na kashe zomon ba rataya aka bani".

"Please kana ji na farko dai saika cire zargin da kake yimata idan ba haka ba duk randa ta gano ana zargin ta to wallahi duk randa Allah ya kaddar auran ku zata gwara ka sosai,na biyu dole sai ka rage wannan shegen kishin naka marar amfani ,sannan saika daina takurama ta.idan kabi wannan insha Allah Ina ganin zakayi nasara".

"Wallahi matsala ta kishi,tabbas kishin ta yake sanya ni yin wasu abubuwan,Amma Insha Allah zan yi kokarin ganin na rinka control din kaina ".

"Ba matsala bari na koma kasuwa zamuyi magana ta waya".
"Ok Alright nagode"

Da ga haka suka rabu ya wuce gida.

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
~DAGA ALKALAMIN~ ~AUTAH~

*PLEASE* *COMMENT AND SHARE* 👏 .

[3/1, 6:29 AM] Hayat: *🤦‍♂️ZAMANINMU🤦‍♂️*

_(HATTARA YAN MATA)_

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*NOT EDITING* 🤗

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*ZIKIRI LOKACIN FITA* *DAGA GIDA*

*_Bismillahi tawakkaltu_* *__alallahi_* *_walahaula_*_ *_walakuwwata illabillah_* .

*FASSARA*
*Da sunan Allah (nake* *fita),na dogara ga* *Allah,Kuma babu* *dabara,babu karfi sai* *da* *Allah* .

*ZIKIRI LOKACIN SHIGA* *GIDA*

*_Bismillahi walajna,wa_* *_bismillahi_ _karajna_* , *_wa'alallahi rabbana_* .

*FASSARA*
*Da sunan Allah muka* *shiga, Kuma da sunansa* *muka fita,* *Kuma ga Allah kadai* *ubangijinmu muka* *dogara* .
(Mutum zai iya Kara karanta kulhuwallahu kafa daya, domin neman tsari da ga talauci).

BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM

🅿️14
📝Yasir tunda ya fito daga toilet Kan bed dinshi ya kwanta da towel daure a kugun shi.ba bacci yakeyi ba eyes balls dinshi a rufe suke,sosai ya lula duniyar tunani a wani bangaran na zuciyar Shi Yana Addu'ar Allah yasa Beby ta zama mallakin shi.Yana cikin wannan tinanin ya ji Kiran sallar la'asar,Mikewa yayi ya dauro Arwalla tare da shiryawa sky blue na shadda ya saka dinkin yayi mai kyau saboda riga karama ce daidai guywar shi hannun mai link n,kanshi ba hula sau mai santsi da ya taje ta kwanta luf gwanin sha'awa.cikin azama ya wuce masallaci danya sauke farali.

-----------------------

Dady Bishir Yana isowa GRA derect gidan Dan uwan shi ya nufa,mai gadi ya bude mai ya shiga bayan sun gaisa cikin girmamawa,ya nufi hanyar da zata sada shi da falon gidan.A daidai kofar kofar sukayi kicibis,Abbah shida Jabir sun fito zasu je masallaci."A a Dan uwa Kaine tafe da yammacin nan,yanzu muke maganar da Jabir cewar "da mun fito daga sallah zai kaini gidan naka"Ashe kana tafe".cewar Abbah Yana kallan dan uwan nashi cikin so da kaunar juna.

"Wallahi kasa daurewa nayi kawai sai na fito,Amma mu je masallacin mu dawo sai mu tattana".

A haka suka wuce cikin nutsuwa da San junan su Jabir kuwa Yana gefen su.

**************
Farrah baiwar Allah ta dade a cikin toilet tana sharbar kuka,saida ta gaji saboda yanda ta ji kanta Yana saramata da karfi,kamin ta nufi jikin sink fara wanke fuskarta tayi kafin ta gyara jikin ta dan tana fashin sallah.sai a sannan ta tina ko abinci bata ci ba sakamakon kugin da ta ji cikin ta nayi alamar Yana bukatar abinci.Doguwar riga kadai ta zira ta dora dan siririn mayafin saman kanta.

A hankali ta nufi kiching din,cikin sanda dan kar kowa ya ganta tayi sa'a kuwa dan har ta shige ba Wanda ya ganta.Dambun shinkafa ne ta gani da miyar kabeji,Dan kadan ta sanya cikin plate ta dora nama akai bata tsaya daukar lemu ba dan tana da shi a fridge dinta.Cikin sanda ta samu ta shige dakinta,key ta murza a jikin kofar ta fara cin abincin ta cikin nutsuwa kamar wadda bata da damuwar komai a ranta.dan ita har ga Allah damuwa bata hanata ba cikinta hakkin sa.(kamar ni kike Farrah idan ma baka ci ba,to fa damuwar duniya dai kullun karuwa take yi😂😜).
Chapter 11 · 0% Book details