← Book details Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 40

Sashe 24

Zamaninmu Mafarkin Gobe Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🅿️37
📝 *WASHE GARI*
Tun gab da asuba ta farka jin jinkinta alamar zazzabi ga kanta Yana faman Sara mata,wanka ta shiga tare da dauro Arwalla ta kabbara sallah tana Kai kukanta wurin zaljalali akan ya zaba mata abin da yafi alkhairi a rayuwar ta.saida ta ji an tayar da sallah kafin ta yi tata,bayan ta idar dakyar ta rarrafa zuwa Kan gadonta ta konta tana jin zafin zazzabin Yana karuwa.

Sai karfe Tara Momy ta shiga dakinta bayan ta kammala break,Dan ta tayar da ita.Gani tayi tana bacci,a hankali ta fara tayar da ita.
Dakyar ta bude idanunta saboda nauyin da kanta yayi."Momy kaina ciwo yake yi"tana dafe barin goshinta da hannu.

Jin jikinta tayi yayi zafi,"Subahanallahi Farrah zazzabin ne?tashi kiyi break sai kisha magunguna"kamata tayi ta kaita toilet ita Kuma ta nufi kiching.
Bayan ta fito bakin gadon ta zauna ta buga uban tagumi tana tinanin meke Shirin faruwa da rayuwar ta ne?ta kasa gane inda matsalar take.
Momy ce ta turo kofar dakin da tire a hunnunta ajewa tayi Kan kafet tana yimata sannu,tea ta hada mata mai kauri ta Mika mata bayan ta dan Sha ta ballo magungunan kamar yadda ta gani a rubuce ta Mika mata.tana Sha ta fara kokarin yin amai,Amma Allah ya taimake ta Bata yiba,Dan haka Momy ta Kara gyara mata filo ta konta.bargo ta rufeta da shi tana tattare kayan ta fita da su.ita ko rufe idanunta tayi tana jin haushin Ya Yasir,Dan tasan yau Aunty Husnah zata wuce Abuja shikenan ya ja mata Dan tasan Dady ba zai Bari a tafi da ita ba.

~~~~~~~~~~
"Gaskiya boka gagara ni bazan yarda ba ace na baka kudi amma aiki yaki ci,Dan wannnan shi ne burin da take raina naga ya rabu da ita hankalin shi ya dawo gare ni".

Cikin amon muryar shi marar dadin saurare ya ce "A wannan karon zamuyi nasara a kansu,Amma hanyar da zamu bi ita ce :yanzu haka tana konce Bata da lafiya zamuyi amfani da wannan damar ta hanyar tura ALJANI ya Kara rikita rashin lafiyar daganan sai a sanya tsanar shi a zuciyar ta ta birki ce mai har sai ya saketa,Dan shi Yana da yawan yin addu'o'i shiyasa yake neman gagarar mu,Amma ki kontar da hankalinki".

"Yauwa boka yanzu muka ji magana"cewar khairiyya da take gefenta.

Kudi suka Kara masu yawa suka ajemai suka bar wurin cikin farinciki.

**************
Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un shi ne kalmar da ta fito daga bakin shi lokacin da ya farka daga baccin da ya dauke shi tun bayan ya dawo daga sallar Asuba.
Sosai ya ji gaban shi ya fadi tinawa da yayi da mafarkin da yayi na ganin Farrah a cikin wani mawuyacin hali,Yana ta kokarin taimakon ta Amma sai yaga wata yarinya ta shiga tsakanin su.
Saukowa yayi ya shiga Wonka Yana gamawa ya dora arwallah tare da shiyawa,duk cikin sauri yake Shirin Dan burin shi ya je yaga ya lafiyar Beby take.

Part din ya shiga da sallama dauke a bakin shi.Su Momy suka amsa bayan ya zauna Yana gaishe su yake tambayar jikin Farrah,amsa mai tayi da sauki Dan ita Aunty Husnah sama-sama ta amsa saboda ta ji haushi ga shi nan ya jawowa yarinya cuta ba gaira daga cizon soyayyay ita ya zamar mata na wahala.
Ganin yadda suka yi biris da shi yasa ya nufi dakin ba tare da ya Kara ce masu komai ba...A rufe ya riketa Dan haka ya zauna kusa da ita Yana Dora hannun shi saman goshinta jin ba zafi sosai sai zufar da take yi.karfin fanka ya Kara mata,Yana janye bargon da aka rufeta.sosai ya ji tausayinta ya zarga zuciyar shi da bargon jikin shi.Dan karamin bakinta yake kallo ganin yadda take motsashi gwanin sha'awa.jiyayi gaban shi ya Kara faduwa Dan haka ya fara karanto addu'o'i Yana tofa mata cikin kwarewa da sanin haruffan larabci. A kalla ya dau tsawon 20 minutes kafin ya fita daga dakin bai tsaya a falon ba kawai ya wuce part din shi.

Wata muguwar dariya ya fara saida gaba dayan dajin ya amsa saboda karfin muryar shi,tsagaitawa yayi Yana wasu irin surutai masu kama da yare "Ai ko ya tabowa kansa tunda har ya konaka,sai na kaskantar da shi,idan ko har hakan Bata samu ba to sai dai ka koma jikin Bilkisu Dan tun farko na fada mata"Yana kaiwa nan ya kara kwashewa da wata mahaukaciyar dariya kafin naga a karo na biyu.

Kasancewar ranar lahadi ne ba aiki Dan haka yasa Jabir shiyawa cikin wata shadda kalar sky blue dinkin zamani,yayi kyau sosai bai saka hula ba sai kanshi da ya gyara.karfe hudu na yamma ya nufi Barhim dan ya gaisa da Farrah Dan ya Kira Momy take cemai ai Bata jin dadi.

🤦 *ZAMANINMU* 🤦
( _HATTARA YAN_ _MATA_ )

*NA*
*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*

_______________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*

*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI*

*NOT EDITED* 🤗

🅿️38
📝Yana fita daga gidan su ya dauki hanyar Barhim baka jin komai a cikin motar sai kira'ar karatun kur'ani mai girma da yake sauraro,sai wani mayan kanshin turare da ya cika motar,sosai yake jin nutsuwa tana Kara sauke mai,Dan haka ba abinda yake Kara nanatawa a zuciyar shi sai tasbihi tare da godiya ga Allah da ya hallicce shi a cikin Al'ummar musulmi,ga ni'imomi da ya nufeshi da su masu tarin yawa,cikin ikon Allah da haka ya karasa duk da shi ba ma'abocin gudu ne ba kamar yasir🤣

Bayan ya wuce babban gate yana karasawa ciki Suka gaisa da Baba Auwalu, inda yayi parking fitowa yayi Yana taba Dan karamin sajen shi da ga Sha gyara.

Yasir ya hango Yana kokarin shiga part din shi,ganin ya Dan yi mai nisa Koda ya bishi kafin ya tadda shi ya riga ya shige,Dan haka kawai yadan daga murya Yana "Ya Yasir! Ya Yasir!"gani yayi bai waigo ba sai sai gani yayi ya shige ciki.

Shima Jabir kyale shi yayi ya nufi cikin gidan,A zuciyar shi Yana tinanin may be bai ji Kiran ba.

Ba kowa a Falon hakan yasa ya zauna Yana faman Danna wayar shi da alama chat yake yi ji nayi Yana cewa "Ai wallahi salisu ka Bari,shiyasa na gudu fa Dan nasan da kawu Yakubu ya farga da irin girman jikin da nayi to Yana iya dauramin aure a ranar shiyasa na biyo su Dady na fece gida,ni Kuma gaskiya tinda na rasa Farrah to Aure ba yanzu ba Dan Ina jin kewar ta har yanzu a kasan zuciya ta"ya karasa voice din muryar shi cikin rauni da alamar damuwa.

Daidai lokacin Farrah ta farka daga baccin wahalar ciwo da ya dauketa.jin kamar maganar mutum a Falo yasa ta leko Dan ji tayi muryar kamar ta namiji.

Kan kujera ta ganshi,bayan shi kadai take hangowa saboda shi Yana passing din tv ne ita ko kofarta na barin dama ta bayan kukerar,haka yasa shi bai ganta ba.

Kuri tayi da idonta tana hango sumar kanshi mai kyau da sheki.a zuciyarta tana jin yanzu da shi ne aka aura mata da suna nan suna kwasar soyayya,Amma an tashi an lika mata wancan mai irin ta Yan india.da sauri ta furta Astagfirullah tana mai komawa cikin dakin domin ta rama sallar da aka biyota.

Duk abinda take yi Jabir Yana hangota ta jikin tv saboda hasken gurin,Kuma a kashe take shiyasa,Ajiyar zuciya ya sauke tare da kokarin yakitar da tinanin da zuciyar shi take son bijiro mai da shi.

Ba tare data dau tsawon lokaci ba ta kammala har Wonka tayi kafin ta saka doguwar rigar atamfa ta dora hijaf akai,turare kawai ta fesa Dan ko mai Bata tsaya murzawa ba ta nufo falon.

Yana jin alamar takunta ta nufo inda yake,ya dago kanshi Yana dubanta gani yayi fuskarta tayi fayau kamar an jata,sai idanunta da suka fada alamar ta ji jiki.

Saida ya ji ta zauna a kurerar dake gefen shi kafin ya tina da magana yake yi a waya, wata yar office din su ce ta kirashi akan maganar wasu takaddu da za'a kawo mai a gobe litinin.

Katse kiran yayi Yana cewa "sorry I will call you letter "yana aje wayar jikin hannun kujerar.

Kallanta yayi sosai Yana Kara jin wani abu Yana yima shi yawo a kasan zuciyar shi.

"Sannu ya jikin naki"shi ne abinda ya iya furtawa Yana kallan fuskarta ganin yadda duk ta rame.

"Yauwa Ina yini "tana kallan shi ta kasan idonta.

"Lafiya Lau,ya jikin naki?"

"Alhmdl yayi sauki,kunbirin ya saki"tana juya hannun.

"Ok a hannu ne kenan,meye ta cije ki haka naga wurin yayi ja"?

Jim ta dan yi kafin ta ce "bigewa nayi ne jikin kofar toilet"a ranta tana ai bazan iya sanar ma cewar wancan katon ne ya cije ni ba,haba ai da kunya ma.

"Ok Allah ya kiyaye gaba"

"Amen ya Allah"tana sadda kanta kasa,Dan har yanzu kunyar shi take ji,tunda tasan zuwa yanzu yasan da maganar kaddararen auren da aka lika mata.

Shiru suka yi dukan su,kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi.suna a wannan Yana yin Yasir ya turo kofar falon.
Gaba dayan su suka juya,tana ganin shi tsam ta mike ta wuce dakinta.shiko Jabir cewa yayi "A Yaya ka fito?lokacin da na shigo Ina ta magana magana baka jini ba ka shiga part dinka".

"Ok" ya ce Yana zama bisa kujera.

"Jiya Momy take fadaman Auntyn tamu Bata da lafiya,shiyasa na zo dubata,Amma nasa da sauki"

Yasir shiru yayi Dan wani haushin kanen nashi ya ji Yana Kara kama shi,Dan rainin hankali ya zo ya tsare matar shi Yana kalle mai ita,yanzu Kuma Dan yagan shi ya bige da wani dubata ya zo yi.

"Ok ai daka Bari shikenan ,Dan taji sauki"Yana danna remote control a hannun shi.

Jabir tsayawa yayi Yana kallan shi a zuciyar shi mamaki yake yi,A maimakon ace shi ne yake nuna kishi akan fin karfin da aka yimai,Amma sai ga shi Wanda yayi nasara yake nuna haka.
Chapter 24 · 0% Book details