← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 32

Sashe 8

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harabar gidanmu ta cika ta batse da mutane, yan uwa da abokan arzi™i ta ko ina, wajen ya tsaru yanda event planner Win suka yi ™o™ari akan haka, ko ina na wulga yan uwana ne, da yan uwan Turaki, ™awayena da abokansa. Ni da shi muna zaune sai twins suma a zaune, abokan Turaki sai kuWi suke zubawa, wannan ya fito ya ce ya bawa Twins 2million, wannan ya ce 5million, har da wanda ya basu 15Million shine yafi kowa, sai kuma masu basu gold, haka aka yi ta abu, tun ina lissafa miliyoyi har na gaji na daina, abinci anci, an sha, Twins sun ga sabuwar rayuwa kowanne su sai farin ciki yake. Haka ka aka tashi daga taro kowa ya watsa muka zauna ni da Turaki muka fara tattaunawa akan abinda abokansa su ka yi, na ce.

Habiby, abokanka haka suke daman?

Ai Habibty mun saba, duk wanda aka yiwa haihuwa haka muke yi, yanzu ko wasu aka ™ara haifa haka zaayi musu, amma na farko sunfi mora.

Na girgiza kai na ce.

ChaS.

Habibty yanzu kuWin ya kusa 60million, ina tunanin ko asiya musu filaye na 20/20 million, ragowar kuma abawa Yaya Ridwan.

Ai ba zai amsa ba, zai ga kamar mun nuna ba ya yanmu ba ne.

To Habibty me za mu yi da su? Idan muka cire musu 40M a ciki, ai yawadatar.

To Habiby ko za a biya musu Umarar azumi shi da matarsa, ace da kuWin da aka samu ne.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(7).

Cikin kwana biyu Turaki ya siyawa Twins manya manyan filaye guda biyu na kimanin miliyan 20 kowacce Wayansu, sannan kuma ya fara ™o™arin biyawa Yaya Ridwan da matarsa Umarar azumi, Twins basu bamu wahala ba wajen zama damu, sun saba da mu cikin ™an™anin lokaci, sun kuma shiga ran mu duka. Suna kirana da Maamah, suna kiran Turaki da Papah, ranar da naje dasu gidansu Turaki basu sami wata tsangwama ba, kowa ya karSe su hannu biyu, kuma na ji daWin hakan sosai. Cikin ™an™anin lokaci aka sama musu mai kula da su, inda aike kai su gidan idan zan fita, idan na dawo kuma na biya na Wauko su.

Mun fara shimfiWa rayuwa cikin farin ciki, hankali kwance. A Sangaren Sardauna dai Islaha ba ta dawo ba, sabida Hajiya Falmata ta dage kan Islaha baza ta dawo ba, har sai Sardauna ya Wau mataki akan Bilkisu, abinda ya gagare shi kenan, a yanzu maganar ma ta mutu har wajen su Big Daddy, a raina na ce. Idan Bilkisu ba ta yi haka ba ai ba ta cika mai bin malamai ba. Shiru magana kowa ya manta da ita, ta ci gaba da rayuwa da Sardauna cikin faWa, kullum cikin tashin hankali gashi yawo ta ci gaba ba zama, abun nata ma ya fara gaba dan sai ta kwana acan ma inda ta tafi yawon, ta mayar da Sardauna sallau, ba abinda ya isa ya yi mata, sai dai mita su yi ta Waga murya. Nikam na mai da hankali kan kula da ya yana da kuma aikina, shine abinda ke gabana yanzu, sai kuma kula da Turaki.

Lokacin da aka sanar da Yaya Ridwan da matarsa zancen tafiyar Umarar azumi har da ™wallarsu ta jin daWi, haka ma Hajiya sai a lokacin aka sanar da ita zuwan mu aikin Hajji, in sha Allah. Cikin ikon Allah watan azumi ya gabato, Turaki zai tafi goma ga azumi ya dawo biyu ga Sallah, su Yaya Ridwan kuma zasu tafi farkon azumi ne. Shirye shiryen azumi sun yi nisa, na ro™i Turaki akan ya barni na sami masu aiki da zasu dinga min kunu da ™osai na sadaka, idan anyi sai a Wauka a fita da shi can ayi sadaka, ba tare da ya yi wani musu ba ya amince, har ya bada wasu kuWaWen shima a matsayin na shi gudumawar, nasa aka sama min masu aiki mutum uku.

Cikin ikon Allah aka fara azumi ranar talata, a ranar mu ka yi abincin sadakar mu aka fita da shi ya ™are tas, washe gari mu ka ™ara yawan shi sabida matar ta ce min akwai mutane marasa ™arfi da yawa daga wajen unguwar. Ranar azumi na huWu Yaya Ridwan da matarsa suka ta shi, ranar azumi na shida Yaya Rumaisa ma da mijinta suka ta shi, wannan shekara sai ta zama shekara mafi farin ciki ga yan gidanmu, har mutum biyu sun tafi saudiyya kuma ana saka ran nida Hajiya zamuje aikin Hajji.

Ranar da aka yi azumi na goma Turaki ya tashi, gida ya zama daga ni sai Twins, har da kukansu da muka dawo, aka ci gaba da abin sadaka har azumi ya ™are aka yi sallah Turaki ya dawo, tun tafiyar Turaki na yi ™o™ari wajen Wauke kai daga al amarin Sardauna da Bilkisu, kamar basa gidan haka na mayar da su, kuma suma sun rage abinda suke yi, dan shima Sardauna ya tafi saudiyya ™arshen azumi.

Haka aka yi bikin sallah cikin farin ciki, a lokacin bikin sallah matar Ra is ta sauka inda ta sami Wa namiji, an sha taron suna anyi farin ciki, inda aka yi wa Alhaji takwara aka sanyawa babyn sunan Alhaji, ranar suna na a gajiye tilas na dawo, ga Turaku ya maida hankali akan gina sabon gidan da zamu koma, wajen ™arfe tara na dare na dawo gidan, ina sauka a mota na ga yan sanda a harabar gidan namu, da sauri na tura su Twins cikin part Win mu, yan sanda suka ™araso inda nake.

Ranki ya daWe barka da dawowa.

Barka dai, wa kuke nema haka?

Na faWa fuskata da alamar tsoro, danni a rayuwata ma magana bata taSa haWamu da yan sanda ba.

Muna neman matar gidan nan ne?

Ni ce matar dake zuane a wannan part Win.

Na faWa ina nuna part Winmu, sanna na ce.

Matar dake zaune a wancan part Win kuma, tana ciki ko bata nan ni ban sani ba, wacce kuke nema?

Bilkisu.

Na nuna musu part Win na ce.

Ita ce me nan, ni sunana Nana.

Ai mun buga tun Wazu ba a buWe ba.

Eyh da yake ba zama take yi ba, babu tabbacin ta nan, sai dai kujirata tun da ba kwana take a can ba.

A a idan ba ta zo ba zamu tafi dake.

Na yi musu wani kallo, sannan na ce.

Akan wane dsalili kenan?

Akan dalilin neman ta dake ayi, kun Soye me laifi.

Ina ba a gidan na zo na sameku ba? Ta ina zan Soye ta to? Ku jira ko ita ko mijinta wani na zuwa.

Mu DSS ne, muna bincike ne akanta, sabida an zargin ta da harkar dillanci ™waya.

Dillancin ™waya kuma?

Nai maimaita a tsorace, sannan na ce.

Ita Bilkisun? Lallai.

Eyh ita, to kinga wannan case din babbane. Idan babu ita za a iya tafiya dake?

Malam ni a wa? Kishiyata ce ko me? Nifa bani da wata aka™a da ita, mijina da mijinta ke da ala™a, dan haka ni bani da wani ala™a da ita.

Duk haka, kinsan inda za a same ta.

Tare muke yawon ko me? Ni zan shiga ciki, kuna nan tsaye mijinta zai shigo, zaku ganshi wani ja kamar ™osai.

Ina faWin haka na shige ciki, ina mamakin yanda mutanen nan suke neman shafa min kashi awaki, ina shiga na kira Turaki a waya, yana Wagawa na ce.

Habiby da matsala gida.

Me ya faru Habibty?

Jami an DSS ne a gidanmu, wai zasu tafi dani sabida suna neman Bilkisu basu ganta ba.

To ke awa? Kar su kuskura, ki faWa musu na ce idan suka tafi dake duk sai na yi shari a da su, gani nan zuwa.

Daidai lokacin na ji ana buga min ™ofa, aikuwa na yi kamar ba na ji na™i buWewa, suna tsaka da bugun na ji Turaki yana ce musu.

Bayin Allah lafiya?

Sai a lokacin na taso na buWe ™ofar, ina ganin shi na ce.

Sai bugu suke min, na nuna musu part Win Bilkisu amma sunki ha™ura.

Ina tambayar ku lafiya, kunzo kuna tayarwa da matata hankali kuma kunyi shiru.

Mu jami an DSS ne, munzo ne muna neman Bilkisu.

Ga can, nan ne part Winta, mijinta da ita duk basa nan, dan haka kar ku zo nan ku Waga mana hankali.

A tsarin ™a idar aiki idan akan wannan case Win ne ana kama waWan da ke kusa da mai laifi.

Wanda ke kusa da ita ai bai wuce iyayenta ba ko mijinta, mu da zama ya haWa mu kuma mene a tsakanin mu?

Ka yi ha™uri yallaSai, amma dole zamu tafi da wani cikinku.

Babu wanda zaku tafi da shi, nina jami i ne.

Turaki ya faWa yana Wauko musu id card Winsa, sannan ya ce.

Akan wannan abun zan iya shigar da ™arar ku, bama ku kaWai ba, har da hukumar ku.

Shiru suka yi, a daidai lokacin kuma Sardauna ya dawo, Turaki ya ce.

Ga mijinta nan.

Yana faWin haka ya kama hannuna muka shige, muna shiga ya ce.

Wane lefe ne ta yi?

Wai dilal ™waya ce.

˜waya kuma? Ita Bilkisun?

Na gyaWa kai, sannan na ce.

Ita fa, ni na rasa gane kan matar nan, mugayen ayyukunta sunyi yawa, mene haWin ta da dillanci ™awaya tana mace, tana matar aure dan Allah?

Sardauna idan baiyi wasa ba, Bilkisu sai ta ja masa rayuwa a gidan yari,

Bugu ™ofar mu aka fara yi, hakan ya sa Turaki ya fita ni kuma na bi bayansa.

Turaku ka ji wai tafiya zasuyi da ni, ka yi musu magana dan Allah.

Sai da Turaki ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya ce.

Ba shine kuke nema ba, matarsa ce.

Mun sani, amma ai ta™i dawowa.

Shima ta gagare shi, bai isa ya sa ta ko yahana ta ba, amma ku yi ha™uri ku ™yaleshi, idan ta dawo zai kawo ta.

To, amma muna so ya bi mu can ya sa hannu.

Kuje zan kawo shi yanzu.

Turaki ya faWa, sannan ya kalle ni ya ce.

Habibty, mi™omin key Wina.
Chapter 8 · 0% Book details