← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 32

Sashe 24

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kya faWi duk abinda kike so mana, tun da kin gama da miji, an kai suna wajen malamai an mallakeshi.

Banyi niyar bata amsa ba daman, na ja bakina na yi shiru, sai dai na ji Turaki ya ce.

Ai duk malamin da ya mallake mata ni, to taimako na ya yi.

Habiby duk ba wannan ba, ga amarya ka kawo na karSa hannu biyu, Allah ya zaunar, Allah Ya kaWe duk wata fitina, ni dai a matsayina na uwar gida, na bawa amarya kyautar ango har na tsawon wata guda, sabida ran amarya ya yi haske bisa ga Sata mata rai da aka yi, ni dai ina so mu zauna lafiya, kowa ya mutunta Wan uwansa.

Ina faWin haka na mi™e zan tafi, ya yi saurin ri™e hannuna, fuskarsa babu alamar wasa ya ce.

Koma ki zauna.

Na koma na zauna, ya kalle ni sosai sannan ya ce.

Da yake niWin abun wasa ne shine za a bayar da ni? To ban badu ba. Kwanakin da addini ya tanadar na amarya zanyi, sannan na dawo na raba muku kwana fa™at.

Hhhhhm.

Ta faWa tare da mi™ewa ta fice, tana fita ya watsa min wata uwar harara.

Ji wani abu da kika yi, kinsan da yanda zanyi kwanakin nan wajenta shine sabida ki nuna mata ba so na kike ba wai kin bata ni na wata Waya.

Eyh mana wata Waya, aci amarci lafiya ango mijin amarya.

Hhhhm.

Shima ya faWa ya fice, yana fita na ji wani zafi ya ziyarce ni, raina ya shiga Saci a take na fara jan wani tsaki da bansan dalilinsa ba, zuciyata ta shiga raya min munafuncin Wa namiji, na kusa minti talatin anan kafin na tashi na shiga cikin Waki, nan ma na daWe zaune duk raina a jagule, kafin bacci ya Wauke ni. Washe gari da safe iya cikina na yi abinci karyawa, dan banga dalilin da zai sani na ciyar da wata ™atuwa ba, duk da Turaki ya shogo da asuba amma ban wani ba shu fuska munyi magana ba, haka ya gama borin kunyarsa ya koma, yana fita na ja tsaki. Yanzu ma wani tsakin na ™ara ja bayan na tuna yanda yake wani sunkuyar da kai.

Habibty tsakin me kike?

Na ji ya faWa, ba tare da na juyo ba na ce.

Bana jin daWi.

Kai Habibty nine?

Me ka yi min? Kai me ma ya kawo ka nan?

Haba Habibty ki jiyo ki kalleni mana, abinda kike yi min fa bana jin daWi.

Uhmm.

Na faWa tare da ci gaba da aikina, yana tsaye yana ta surutai na gama haWa abincin na na juye a plate na Wau kofi na fita, ya biyo bayana yana magana.

Wai Habibty ba zaki saurareni ba, ina abincin nawa?

Yana wajen amaryarka mana, ni kake tsammanin na yi maka girki ne kai da ita? Ko ba zata iya girkin ba ne?

Wai mene haka dan Allah?

Banza na yi da shi na zauna kan dinning na fara cin abincina, har na kammala yana zaune yana kallona, ina gamawa na Wauke plate Win na nayar kicin na shiga Waki na yi wanka na shirya fita ofis, lokacin da na fito baya nan ya fita, na ja tsaki na ce.

Maza duk haka kuke.

Ina ™o™arin shiga mota na ga ya fito, tsayawa na yi ganin kamar matarsa tasa tana le™e ta taga.

Habibty da wuri yau?

Eyh.

Me ya sa zaki fita da wuri?

To me zanyi a gidan? Ai kana da amarya zata iya yi maka wanka ta shirya ko?

Wai Habibty mene haka? Kince fa abar maganar amma kina ta dawo da ita.

Hhhhm to ni dai zan tafi, zanje makarantarsu twins na faWa musu anyi sunyi relocating zuwa nan, sannan zanje na kwaso musu kayansu na can.

Tom Allah Ya tsare.

Amin.

Na faWa tare da shiga mota na nufi wajen aiki, ko acan duk na rasa abinda ke mun daWi, ina nan amma hankalina da tunani suna gida, ina faman tunanin me Turaki suke yi da amaryarsa, agogon wayata na duba naga sha biyu da kwata. Nasan Babbar likita bata da mutane yanzu, dan haka na tashi na nufi ofis Winta, na yi sa a kuwa ita kaWai ce a cikin ofis Win, bayan mun gaisa ta ce.

Nana akwai wata damuwa ne?

A a babu.

To ya me gidan? Har yanzu haihuwar shiru ko? Ki yi ha™uri tana nan tafe.

Ai yanzu ma babu wannan matsalal, tun da ya riga da ya ™ara aure.

Ya ™ara aure kuma, yaushe?

An kwana biyu.

Allah sarki, ki yi ha™uri kinji Allah Yana ji yana gani, kuma zai baki haihuwa anan kusa in sha Allah, a yanzu sai kinyi ha™uri kin ci gaba da bashi kulawa, mussaman yanzu da yake da wata kuma ana sa ran za a sami abinda ake so daga wajenta.

Mommy ni ai haushinsa nake ji, ko magana bana iya tsayawa na yi da shi, sai na ji raina duk yana Saci.

Hakane daman wannan shine kishin Nana, amma ya™i zaki yi da shi dan tabbas idan kika ci gaba da banzatar da shi tofa zata ™wace miki shi, kuma wannan idan kissa kike nufi ai ba haka ake yi ba, a gabanta ki ja shi a jiki, ki nuna mata ke kike da iko da shi, a bayan idonta kuma sai ki yi duk fushin da zaki yi da shi, shima kuma ba wai dogon fushi ba ko faWar maganganu, haka dai Wan nuna i don t care, kingane.

Nagane Mommy, Allah Ya saka da alheri.

Amin amin daughter, stay strong kinji? Komai da kika gani zai wuce zai zama labari, kamar yanda rayuwarki da tsohon mijinki ta zama labari, wannan jinkirin haihuwar shima zai zama labari, i promised.

In sha Allah Mommy, na gode.

Na faWa tare da tashu na fito, ban wani jima a ofis na na tashi zuwa makarantar su twins, na basu sabom address Win mu sabida zuwa Waukansu da dawowa da su, principle Win ma ya ce wai da address Win aka yi musu rijista tun farko, daga nan na wuce gidan Hajiya na Wauko musu kaya, ban wani jima gidan Hajiya ba na dawo nawa gidan.

Ina parking Win mota ta na ga an buWe part Winta a fito, a raina na yi tunanin ganin Turaki sai kuma naga ita ce da kanta, na buWe mota ta na fito ina jan akwatin su twins zuwa part Win na, babbar ™ofar mu Waya ce amma babu wanda zai shiga part Win wani ko ya ga abinda ke cikin na wani, kowa rayuwar shi kaWai ce, wata yar iskar tafiya naga tana yi, ta wani da™ire tana cije baki tana kallona, kamar wata mai koyan tafiya, na yi wani murmushi mai ban haushi na sa key zan buWe part Wina.

Wash, ni matar cushe uwar ya yan so.

Ta faWa bayan ta zo gab da inda nake, na yi kamar ban ji ta ba na buWe ™ofar da key, a iya bakin wajen na sanya akwatin sannan na juya janyo Waya.

Allah ka sauke ni lafiya, na haifewa Baby Turaki ya ya kyawawa.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(24)

Nan ma dai na yi banza da ita kamar banji ta ba, na koma na janyo Waya akwatin na shigo da ita, ina ™o™arin shiga kuma ta ce.

Allah karka sa na zama su o o mu ci mu kasayar, mu bar miji da asarar kuWin magani, da suna muna kan ganin likita, bayan munsan ba haihuwar zamuyi ba.

Wani abu mai zafi ne ya tsaya min a raina, na juyo a fusace zuwa inda take, nasa hannu na Wauke ta da wani lafiyayyen mari, wanda na tabbatar sai da ta ga taurari a idonta.

Idan kina cin ™asa ki kiyaye ta shuri, duk ™aryar hauka da jahilci da zaki yi ki yi abunki amma karki kuskura ki ce zaki sani, ni ba sa ar ki ba ce ba tsarar ki ba ce, haihuwa kuma dan Allah idan kin fara karki daina, ki zama tinkiya.

Daga haka na shige ciki, nasa mukulli na kule ™ofa ta, ina shiga na haWa kai da gwiwa na fara rusa kuka, lallai Turaki daga kwana Waya wajen amarya shine zaka je ka saki baki ka fara faWa mata abubuwan da za ta yi min gori kenan, tun da dai idan ba shi ba, babu wanda zai faWa mata, kuma ita ba duba take ba, bare ta buga ™asa ta gani, ta inda Turaki zai fara kenan, to ya dawo ni duk bazan Wauki wannan ba wallahi. Kamar daga sama na ji horn Win motarsa, ina zaune na ji kuma ya fara buga min ™ofa.

Tashi na yi na buWe, ina buWewa na gashi tsaye, ita kuma tana bayanshi, shigowa ya yi ta sake biyo bayansa, sai da suka karaso tsakiyar falon sannan ya ce.

Habibty ta ce kin mare ta.

Eyh.

Me ta yi?

Iya marin kika iya faWa masa? Baki faWin abinda ya ja marin ba? Ni babu ruwana da matarka, ta yi rayuwarta na yi tawa, duk habaici da ™ananan maganganunta basu dame ni ba, amma ba zan Wauke gorin akan haihuwa ba, shine kawai.

What! Ita haihuwar take ko kin sami ciki ne? To idan har kina da ciki ba nawa ba ne.

Ni cewa na yi ciki ne da ni? Cewa na yi in Allah Yayarda sai na haifa ma ya ya kyawawa, shine ta mareni.

To ina ruwana dan ta haifa mai ya ya kyawawa? Ni babu abinda ya dame ni, amma muddin zaka je ka ci gaba da gaya mata matsalal dake jikina shine abinda ba zan taSa yafe maka ba Turaki har abada wallahi.

Bangane matsalal dake jikin ki ba, me ta ce na faWa mata.

Ka tambayeta mana, aina tasan ina yi maka asarar kuWi a asibiti? Wai ina kan magani Hhhm.

Laila, aina muka yi wannan zancen? Nifa bazaki zo ki haifar min da matsala ba a cikin gidana wallahi, muddin kika ce haka zaki yi a shirye nake na rabu dake, na faWa miki.

Turaki wannan wane irin rashin adalci kake min? An mare ni kuma kazo kana ce min wani abu daban? Anya zaka iya adalci a cikin gidan nan.
Chapter 24 · 0% Book details