← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 32

Sashe 26

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To sai mene? Turaki fa namiji ne ko baki sani ba? Namiji tsamiya ne idsn yaji™u ya ishe kuwa ya sha, ni na wuce matsayin da zan zauna na yi faWa akan namiji wallahi.

Daman ta ina zaki yi faWa akan namiji? Kina juya baki ajiye masa komai ba? Dole ki ja da baya ki bawa uwar masu gida waje.

Hannu nasa na fisge rigata daga hannun wacca ta ri™e ni, aikuwa ta hantsila kamat zata faWi ™asa na matsa gefe ta buge da bango, aikuwa ta tashi ta yi kaina kamar zata dake ni, a lokacin kuma Lamrah da Ra is suka buWe ™ofar part Wina.

Wai hayaniyar mece?

Lamrah ta faWa, Ra is kuma ya ce.

Kar ki kuskura ki yi gangancin kai hannu jikinta, wallahi sai na sassaSa miki kammani idan kuma kina musu bisimillah.

Cike da rashin mutunci ta kai hannu zata dakeni, ai kuwa Ra is ya ri™e hannunya tsinka mata mari, Laila dake gefe ta ce.

Wane Wan iska ne kai da zaka shigo gidan matan aure, har ka daki mutane?

Lamrah ce ta danna wayarta ta kira lambar Turaki, sai kawai ji na yi ta ce.

Yaya Turaki idan bakayi nisa ba ka dawo, Laila da yan uwanta zasu daki Anty Nana.

Ka ji min munafuka, Laila wannan wace?

Lamrah ce fa yar gidan Daddy Isma il, kinsan duk anyi musu asiri basa gane komai.

Wai haka kike zama da ita tana yi miki rashin kunya? Gaskiyya bazata saSu ba.

To Ya za ta yi? Juya ce fa ita ba haihuwa, dolenta ta yi ha™uri dani uwar masu gida, Matar cushe uwar ya yan so.

Ai ba cikin ba ji jira ki haifeshi lafiya, ban dake Laila ba ki da hankali, mata nawa ne suke mutuwa wajen haihuwa, ciki wahala shi ma kaWai aiki ce, kizo ki haihu baki huta ba, amma kike cika baki kike neman yin rashin mutunci akai.

Sai da uwarki ce ba zata haihu lafiya ba, jaka dake.

Laila abinda kike yi kenan?

Muka ji muryar Turaki, gaba Waya ni banji buWe gate ba bare kuma shigowarshi, sai kawai ganinsa muka yi.

Darling ba haka ba ne, zagina fa ta yi.

Aina ta zage ki?

Yaya Turaki wallahi ba haka ba ne, waccan dabadan mun fito ba fa da marin ta za ta yi, a yanzu ma sai da Yaya Ra is ya mareta, kuma sai juya take ce mata.

Ke dai Lamrah kinyi asara.

Laila ta faWa tana tura baki gaba.

Laila na fuskanci har yanzu kanki rawa yake, har yanzu baki fahimci matsayi da muhimmancin matata ba ko? Dan kina ganinki da ciki ko? To kisani har kullum arxi™inta kike ci, dan haka kije na sake ki saki Waya.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(26).

Ka sake ni kuma?

Laila ta faWa a tsorace, ba ma ita ba ni kaina na tsorata, bansan cewar na kai wannan matsayin a wajen Turaki ba, bansan cewar zai iya aikata duk abinda yake faWa ba sai yanzu, a take na ji wata sassanayr soyayyar Turaki ta mamaye zuciyata.

Wata mata ce ta fito daga cikin part Win Laila, babba a ™ala zata kai shekara 35 ko fin haka, sai da ta ™are mana kalllo baki Waya sannan ta ce.

Tabbas Turaku ka cika gwarzon namiji, ka kuma cika jarumi a cikin na jarumai, ka nuna asalin girma da daraja matarka, ka nuna cewar cikin sa Laila ta samu ba wani abu ba ne da zai ruWe ka har ka hula™anta matarka, tabbas wanna shi ake kira da darajar mace. Ke Laila yanzu ya rage naki, sai ki sam cewar mijinki yana mutunta uwar gidansa, kuma akanta tsaf yake da ya rabu dake. Idan zaki kwantar da kai ki yi wa mijinki biyayya ki girmama masa uwar gida Bismillah, idan kuma baza ki yi ba kan ki, kawai ki sani cewa mijinki mutum ne na gari da yasan darajar iyalinsa, dan na tabbatar ko da kece akan daraja da mutuncinku tsaf zai yi haka, dan haka idan zaki yi biyayya lokaci ne, idan baza ki yi ba zai ™ure miki, ni da ina neman alfarma Waya wajen ka taimaka ka janye sakin nan.

A a Anty ba zan iya ba, ina son wannan sakin zamar mata jan kunne, idan har za ta gyara ta girma ma matata to sai ta dawo, idan kuma tana ganin bazata iya ba to taje kawai na ha™ura, zan iya zama da matata a haka, ko da haihuwa ko babu.

Wasu irin hawaye ne suka biyo kuncina, tabbas Turaki ya girmama ni, ya yi mini matu™ar hallarci, idan na ce Turaki ba Wan goyo da zani ba ne tabbas sai Allah Ya tuhume ni.

To kin ji dai Laila, idan zaki gyara ki gyara idan bazaki gyara ba shikenan.

Muryar Antynta ta ta katse ni, ta faWin haka ra shige ciki, Turaki ya ce.

Bara na koma, idan na dawo sai mu yi magana.

Idonu na cike da hawaye na gyaWa masa kai, ba tare da na yi magana ba, yana barin wajen muka juya zamu shiga ciki, Waya cikin yan matan ta ce.

ChaS, Laila da aiki gabanki.

Lamrah ta ri™e hannuna muka shiga ciki, muna shiga na fashe da wani irin kuka kai wanke zuciya da Sacin rai, ko ™arya Turaki ya faWa a wajen can ni kam ya gama yi min abinda ya da ce.

Anty Nana dan Allah ki daina kuka, yanzu abinda Yaya Turaki ya yi ai ya biya ki, duk rashin mutuncinta da ta yi a yanzu ta biya shi, dan Allah ki yi ha™uri.

Ra is ma ya ce.

Dan Allah karki saka wannan damuwar a ranku kinji, ke ai baki da matsala tun da har mijinki zai iya sakin kishiyarki akan idonki, sabida ta yi miki rashin kunya, bayan tana Wauke da cikinsa wanda ya daWe yana nema, to tabbas wannan mijin Wan halak ne, ya cika gwarzo kuma jarumin maza, Allah Ya ™arawa Yaya Turaki arzi™i, lafiya da nisan kwana.

Cikin kuka na ce.

Amin& & Ra is ba ina kuka dan wani abu ya dameni ba, ina kuka ne na zallan farin ciki wanda yake tafiya da dukkan wani Sacin rai, tabbas Turaki ya biya ni, ya yi min abinda ba ni da wani nauyi akansa, sai dai shi ke da shi akaina, tabbas Turaki Namiji ne, gwarzo kuma madubin al ummah.

Haka Lamrah da Ra is suka ci gaba da tausar zuciyata, suna lallashi na da bani ha™uri har lokacin da su twins suka dawo, tun da suka dawo aka bar maganar, kasancewar sun da wayo da ri™e abu, kuma uwa uba suna da mugun surutu.

Sai wajen yamma su Ra is su ka tafi gida, Ra is ma da twins ya tafi gidansa akan zai dawo dasu gobe tun da yau asabar ne, bayan sun tafi na tashi na shirya na gyara gida, dan na yi al™warin ko da Laila ko babu Laila zan kasance mai bawa Turaki farin ciki a kowanne lokaci, zan kasance masa sanyin idaniya. Sai da ya dawo ma nake jin labarin wai ashe Lailan ma bata gidan, na yi ta tausarsa ina faman bashi ha™uri akan ya janye sakin ya dawo da ita, sabida tana Wauke da abinda yake so, cike da Sacin rai ya ce.

Habibty wai tana Wauke da abinda nake so, ni banganewa wannan zancen na ki ba, cikin jikinta mene? Dan tana da shi sai ta hula™anta ki? Wallahi da wannan cikin da su twins duk Waya nake jin su a raina, dan haka bazan taSa bari wani ya hula™antaki ba in sha Allah Habibty.

Sai da Laila ta yo sati biyi cif a gidansu, sannan ya dawo da ita, dan a hakan ma nina sa baki sabida kirani da ta dinya yi a waya tana bani ha™uri, tun da ya dawo da ita ban haWa ido da ita ba, part Winta ma tun da tazo gidan ban taSa shiga ba, rayuwata nake hankali kwance ina kuma samawa mijina farin ciki, babu ruwan da ita kamar ma ba a hallice ta ba a gidan, haka nake rayuwa abuna kamar babu wata hallita a gidan sai ni. ˜arar da waya ta ke yi ne ya tilasta min fitowa daga cikin kicin Win, ina zuwa na Wauke ta akan kujera na Waga.

Hello good afternoon ma, muna magana da Mr s Turaki mother of twins ne?

Yes! Nice is anything right?

Calm down please, we want see you at school right now?

Hello i don t get you, what happens to my Babies?

Plase come.

Tana faWa ta kashe wayar, hankali a matu™ar tashe na koma cikin na kashe gas Win, na Wau mayafi daga jaka na fice, a yanyin da na fita da mota kaWai ya isa ya nuna mana ina cikin zallan tashin hankali, ikon Allah kaWai ya kaini makarantarsu twins lafiya, ko gama parking banyi ba na fito, ina fitowa na nufi ofis Win principle Win hankalina a matu™ar tashe, sai dai ina shiga na ci karo da twins sun yi tsuru-tsuru, gafe kuma duk malamai ne a zaune, sai na ji wani sanyi ya ratsa ni, na yi musu sallama tare da samun waje na zauna.

Good afternoon.

Principle Win ta faWa, na amsa mata da.

Afternoon.

WaWan nan ya yanki ko?

Ta faWa cikin rashin wadatar hausa, na ce.

Eyh.

To shekaransu nawane?

Three going to four.

Ta Waga kai, sannan ta nuna min wani yaro ta ce.

Take a look, wannan yaron yana da shekara goma sa Waya ne.

Na yi saurin tare ta na ce.

Ma you can go with the english, zan gani.

Ganin hausar ta ta tana ™o™arin haifar min da ciwon kai.

Okay, wannan yaron da na nuna miki shekara shi goma sha Waya ne, amma yaranki suka yi masa duka suka zubar masa da ha™ori guda shida, bayan malamarsu ta dake su, sun ri™e mata ciki tun Wazu sai kuka take sun™i cikawa.

Na kalli twins, sun haWe rai kamar basu taSa dariya ba, sai a lokacin na kula da gefen hijabin Waya ya yage a cikinsu, Wayar kuma nata ya yi cuku-cuku alamun sun sha dambe, sai kuma ba kalli malamar tana zuane sai matse ido take, na kallesu na ce.
Chapter 26 · 0% Book details