← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 32

Sashe 2

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Big Daddy, kamar yanda na faWa tun a wancan zaman namu, Islaha tun aurenmu ba ta taSa bari ko magana na yi da ita ba, da ta ganni zata Soye, ba ta fara magana da ni ba sai da na auri Nana, shima ba magana ce ba kwai neman faWa ne, haka nake raba musu kwana da Nana, amma duk ranar kwanan Islaha a falo nake kwanciya, sabida bana samun Wakinta a buWe, abinci kafin na aure Nana ni ke yi da kaina, bayan na auri Nana ya zama ko da yaushe ita ce ke yi, babu ranar kwananta da ba na ta ba, ana haka na daina ganin ko jin motsin Islaha a cikin gidan, tun ban fargaba Nana ta farga, ta yi min magana sai na ce ta bari kwananta ya zagayo zan duba ta, kwana biyu Nana ta daina yi min zancen Islaha, idan naje Wakin Islaha kwana zan dai ji mostinta amma bazan yi ido biyu da ita ba, sai wata rana na dawo daga ofis zan Wauki file da na manta, har na fita sai na ji ina son ganinta, sai kawai na shiga part Win nata, abinda na gani yaban mamaki, wai Islaha sai tsaye ga kuma ™aton ciki a jikinta, a take na tambayeta wannan mene, kuma na waye, ta fara kuka sai da na yi mata jan ido, sannan ta ce da ni cikin Sardauna ne a tare da ita, har ma Nana ta sani ita tabata shawarar kar ta faWamin ta bari zata gaya min da kaina, a farko ban yarda ba, tin da naga ba magana suke da Nana ba, babu abinda zai sa ta rufa mata asiri, bayan ta tabbatar min da cikin Sardauna ne na ga bazan iya ba, na yanke shwarar zan kawo ta nan, na sake ta saki Waya, a lokacin kuma Nana ta dawo, ta tabbatar min ta san da zancen kuma abinda yasa bata faWan ba, tana tsoron kar na shiga Sacin rai na saki Islaha, sai dai kuma bata san na riga na saki Islaha ba, daga nan ta bada shwarar a ajiyeta wajen Sister Seemah zuwa ta haihu a bawa Sardauna Wan sa, ni kuma na mayar mata da aurenta, amma kuma Mamanta da Alisha sun matsa, sai zageni suke suna cewa na fito musu da yar su, ™arshe dai na ce musu suje tana gidan sister Seemah.

Big Daddy ya juya ya kalleni, ya ce.

Ke ta ina maganar ta shafe ki?

Bakina yana rawa na fara magana.

Ni.. ni.

Alhaji duk ka kiWima yarinyar nan, ka sanya mata tsoronka na ba gaira ba dalili.

Mama Amina ta faWa, Sister Seemah ta ce.

Eyh wallahi Dad, gani kake kaman ita ke kunna faWa a tsakaninsu, kuma ba haka ba ne.

˜walla na ji ta fara zuba a idona na yi saurin gogewa, na yi ™asa da kaina.

Islaha.

Ya kira sunanta, ta amsa da.

Na am.

FaWamin naki Sangaren.

Itama muryarta kamar za ta yi kuka ta ce.

Tun farko ni bana son Yaya Turaki, ban taSa son shi ba, ban taSa jin sonsa a raina ba, Yaya Sardauna nake so, shi nake ji a raina, kuma shi nake son aura, lokacin da na ji ya yi aure na shiga damuwa kuma na ji babu wadda na tsana kamar matarsa, ina cikin tsanarta ya zo ya same ni ya ce da ni, wai na shiga na fita nasan duk yanda zan yi na na taSata Nana a cikin yan uwa, Satawar da kowa zai tsaneta, har a sa shi ya sake ta ni kuma sai ya aure ni.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(2)

Husbunallahu wani imal wakil, duk Sardauna Win?

Mama Amina ta faWa, Big Daddy ya mi™e ya ce.

Duk ku jira ni, ina ga yau ™arshen kowacce ™arya zai ™are, kowa sai ya hallara a wajen nan.

Yana faWin haka ya fice.

*******

Bayan awa uku.

Šakin ya cika da duk wani ahali na Ta ambo da ya mallaki hankalinsa, Big Daddy ne babba da Matarsa Mama Amina, sai kuma Musa wanda yake mahaifinsu Islaha da matarsa Hajiya Falmata, sai Alhassan mahaifinsu Turaki da matarsa Mommy, sai Alhussain wanda yake a matsayin mahaifin Sardauna da matarsa Nafisa. Sai kuma ya yansu duka. Seemah babba daga gidan Big Daddy, Alisha mai biye mata daga gidan Abbah Musa, sai Sardauna daga gidan Second Daddy (sunan da ake kiran Alhussain a cikin gidan gaba Waya) sai Turaki daga gidan Frist Dad (shima sunan da ake kiran mahiafinsa kenan) sai kuma sauran yan gidan, ciki har da ni.

Big Daddy ya yi gyayan murya sannan ya fara magana.

Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maWaukakin Sarki da ya hallice mu cikin zuri ah guda Waya, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu. Ya yan uwana, abinda ya sa na tara ku anan da dukkan ahalinku shine, ina so mu warware wani zare da ya daWe yana ™ulli a tsakaninmu, wanda ni kaina na gaza gane asalin gaskiyyar zaren. Islaha ta so nan.

Ya faWa yana nuna mata kusa da shi, ta mi™e ta taku, a take na kai idona kan Sardauna na ga yanda ya yi matu™ar kaWuwa da ganin cikin a jikin Islaha, dan daman tin da yanzo tana zaune waje Waya ba ta ko motsa ba, idanunsa suka fito waje gaba Waya, a take ya fara fitar da zufa, na yi murmushi a raina na ce. Sardauna yau ™arya ta ™are. Sai da Islaha ta ™arasa ta zauna, sannan ya yi ™asa da kansa, Big Daddy ya ce.

A tarihin gidan nan muna zaune lafiya, yar rigimar dake tsakani ba ta taSa shafar mu ba, ba a taSa zuwa gabana an kawo ™ara ba sai akan wannan yarinyar.

Ya faWa yana nuna ni, a take na ji gabana ya faWi, bayan idon mutane ya yi kaina baki Waya, na yi ™asa da kaina a take na ji jikina ya fara karkarwa, sai da na ji Lamrah ta sannu ta dafe ni, sannan na iya nutsuwa.

Ina zaune na fara jin ™ana nan magana akan cewar matar Sardauna tana yawo bin maza da aurenta, na shiga tsananin tashin hankali da kiWima, mace mai bin maza da aurenta a cikin ahalinmu? Abun gaba Waya ya Waga min hankali, na ji duk yarinyar ta fitar min a rai. Sannan na ji kuma ana cewa wai Abubakar Turaki take bi, anan na fara shakku akan al amarin amma ban nuna ba, ana haka Sardauna yazo da zancen ™arin aure, na yi farin cikin jin haka sosai, sabida yarinyar duk ta fitar min a rai, na amince masa yaje ya yi sabon aure, bayan auren da watanni na samu labarin ya saki matarsa ta farko, na yi hamadala da cewar komai ya ™are. Yan wattani kaWan Sardauna ya sameni da zancen Turaki ya ci gaba da bin tsohuwar matarsa, har da hotona na shaida duk ya kawo min. A wannan lokacin na ji yarinyar ta ™ara fita a raina matu™a, ana haka Islaha ta tare ni da zancen tana son Abubuakar da aure, na yi murna sosai sabida a ganina zumunci ne da zai ™ara ™ulluwa cikin ahalinmu, bayan na yi magana da Abubakar aka yi aure, watanni kaWan ya zo min da zancen ™arin aure, yana so ya aure Nana tsohuwar matar Sardauna, anan na ™ara tabbatar da abinda Sardauna ya faWa a baya, na kuma dage akan ba zaayi ba, amma da yake ubangiji ya tsara za ayin, gashi anyi.

Tun a bayaj auren Yarinyar nan Nana, aka fara sintirin kawo ™ara wajena, ba a zauna ba. A yau kuma an zo da wani gagarumin abu da ya girmi tunani na, shine wai Turaki ya saki Islaha, sabida tana Wauke da cikin da bana shi ba.

A take kowa ya ya Wauki Salati, ana tafa hannu, Mommy ta ce.

Turaki! Wannan wace irin banzar magana ce marar tushe? Ya za ayi ka ce cikin dake jikin matarka bana ka ba ne?

Big Daddy ya ce.

Ki yi ha™uri, ki saurari komai mana, kowa ya yi ha™uri. Kai Abubakar me ya sa ka ce cikin dake jikin Islaha ba naka ba ne?

Turaki ya yi gyaran murya ya ce.

Kamar yanda na faWa a wancan zaman namu, a yau ma zan sake maimaitawa, tun aurena da Iskaha babu wani abu da ya taSa haWani da ita, ko da maganar fatar baki ce, sai a bayan na ™ara aure, shima ba wai magana ba ce, rashin mutunci ne kawai take kawowa, rana Waya kwatsam naganta da ciki a jikinta, ko da na tambayeta sai ta fara kuka tana bani ha™uri, zuwan Nana yasa ta sanar da ni wai cikin Sardauna ne.

Ita aina ta sani dan ubanta?

Maman Sardauna ta faWa a fusace, Big Daddy ya ce.

Dan Allah duk wanda ba a bashi izinin magana ba ya yi ha™uri, komai zai fito wannan zaman zai kawo ™arshen komai. Ke Nana.

Ya kira sunana, na Waga kai na kalleshi, ya ce.

Aina kika san cikin jikinta na Sardauna ne?

Cikin rawar murya na ce.

Ita ta faWa min, na shiga Wakinta na ganta da ciki kuma bata da lafiya, shine na fara taimakata da wasu ayyukan da zuwa asibiti, shine take faWamin kuma wai tana tsoron sanar da Turaki, shine na ce zanyi ™o™ari na faWa masa yanda zai fahimta, kuma ban samu dama na faWa masa ba har Allah Yasa ya gani.

Big Daddy ya ce.

Islaha.

Na am.

Ta amsa, ya ce.

Mene gaskiyyar waWan nan maganganun?

Ciki murya kuka ta fara magana.
Chapter 2 · 0% Book details