← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 32

Sashe 14

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwananmu takwas a madina muna gabatar da ibada, sannan muka je ziyara. Bayan munyi kwanaki takwas a Madina, muka daura Harami daga Miqat na Dhul-Hulaifah (Abyar Ali) mula nufi Makka a mota tafiyar a ™alla awa 4 zuwa 5.

Ko da muka je makkah, bayan mun sauka a masauki, muka wuci harami kai tsaye domin yin Šawafi, bayan mun gabatar da Wawafi muka fita daga harami muka shiga jiran kwanakin aikin Hajji, Ranar takwas ga watan Dhul-Hijjah muka daura niyyar Hajji daga hotal dinmu, motoci su kwashe mu zuwa Mina, inda muka kwana a tantuna muna ibada da sallah. Ranar 9 ga watan Dhul-Hijjah Ranar Arfa wacca take Jigon aikin hajji da safe muka fito daga Mina muka wuce filin Arfa. Anan ne muka yi ya yin addu'o'i tun daga azahar har zuwa faduwar rana. Anan na buWe duk wata bu™ata na zube, bayan faduwar rana muka wuce zuwa Muzdalifah. A nan muka yi sallar Magriba da Isha a hade, anan ne ake kwana a dandaryar kasa filin babu tantuna, sannan muka tsici tsakuwa na jifan Shaidan. Ranar 10 ga watan Dhul-Hijjah da take Ranar Sallah, da safe bayan asuba, muka koma Mina. Anan ne muka yi jafi Shaidan da tsakuwa guda 7. Bayan an yi aski/yanke gashi kuma an yi layya, sai kuma muka cire harami. Sannan muka koma Makka muka yi Dawafur Ifadah da Sa'ayi na Hajji, muka dawo Mina muka kwana. Duk wannan ibadar da su twins ake yi, ba ma su ba har da yara da basu kai shekarun su ba, iyayensu sun saki su suna ibada, zai anzo wajen Waura niya ne nake tsayawa na faWa musu abinda zasu faWa.

Ranar 11, 12, da 13 ga wata Kwanakin Tashriq ne, muka ci gaba da zama a Mina muna jifar shaidan guda uku Kuskure, Tsakiya, da Babba kowace rana da tsakuwa bakwai bakwai. A ranar 13 muka kammalawa muka dawo hotal dinmu na Makka.

Sai bayan mun dawo hotek muka fara gaisawa da yan uwa, dan wayar tawa ma acan na barta a hotel Win, sabida na mai da hankali ga ibada.

Haka muka ci gaba da gabatar da ibada, muna waya da Turaki muna video call sosai, lokacin da aka cika sati biyu da idin babbar sallah na tashi da wani irin nauyi a zuciyata, na rasa me ya sameni gaba Waya, gashi sai kiran wayar Turaki ne ba ta shiga gaba Waya, ta whatsapp na yi magana da Ra is, sallama na yi masa naga yana online, ban jira ya bani amsar sallamar ba na ce.

Kana ina?

Ina gidana mana?

Ya dawo min da amsa a take, na sake ce masa.

Kaga ina kiran Turaki ba ta shiga kwata kwata.

To Network ne babu mana.

Ya sake dawo min da amsa, kamar yana kallona na girgiza kai na ce.

A a jikina bai ba ni haka ba, dan Allah ka duba min ko lafiya.

Ke ki kwantar da hankalinki ba mutuwa ya yi ba, da ya mutu au zamuji.

Sai da na fara tura mai sticker duka, sannan na ce.

Nima banji mutuwa ba, dan Allah ka dubamin na rasa me ya sa, duk jikina babu daWi.

Ina Hajiya?

Sun tafi massallaci ita dasu twins.

To kitashi ki bi su, ki yi addu a amma bakomai wallahi.

Allah Yasa.

Na faWa tare da kashe wayar, daidai lokacin kuma naga Lamrah online itama na yi mata sallama, ina mata sallama ta kira ni whatsapp call, na Waga tare da cewa.

Salam Lamrah.

Anty Nana mutanen saudiyya.

Lanrah ya gida?

Alhamdulillah, Ya ibada.

Ibada Alhamdulillah.

Allah Ya amsa mana, dan Allah ayi mana addu a.

In sha Allah Lamrah, ya gidan naku?

Lafiya ™alau wallahi, yaushe ne dawowarku?

Nan da kwana takwas, amma wallahi lamrah na ™agu na dawo gida.

Kai subhanallahi, saudiyya guda.

Bazaki gane ba ne, hankalina yana gida wallahi ji nake kamar wani abu ne yake faruwa.

Hhhhm, babu abinda yake faruwa ki kwmatar da hankalinki, ki mai da hankalinki akan ibada, kina inda addu a bata jinkiri.

Hakane Lamrah, a gaida su Mama.

Zasuji ina twins din mu? Fatan dai har da mu suka sanya a addu a ko?

Har daku kam, suna massallaci nima yanzu zan tashi.

Tom shikenan, Allah Ya karSi ibada.

Amin.

Na faWa tare da katse kiran, sai da na sake gwada number Turaki bata tafi ba, na sauke wata ajiyar zuciya mara daWi na tashi na nufi cikin massallaci, acan na yi ta addu a ina ro™on ubangiji da ya kaWe min duk wata fitina a gidana, ™arfe takwas daidai na dawo hotel, wanda yake ™arfe goma anan nigeria, sai a lokacin naga missed call Win Turaki barkatai, na Wau waya na shiga whatsapp, ina duba naga tarin message Winsa kala kala, danna alamar kira na yi ta ringing biyu ya Wauka, na ce.

Salamu alaikum.

Wa alaiki salam Habibty.

Kawai na fashe da kuka, wanda ya yi matu™ar tsorata shi, a rikice ya fara magana.

Habibty me ya faru dan Allah? Kukan me kike yi?

Cikin kukan na ce.

Haba Habiby, tun safe nake kiran wayarka ba ta shiga.

Ki yi ha™uri Habibty, yau wani aiki ne ya tsare ni, kuma wayar cikin mota na barta daman ba chaji har ta mutu, kinsan data na a buWe yake, to sai da na tashi naganta, na kuma sata a chaji na kira baki Wauka ba, nasan kina massallaci.

Amma ai da tun kafin ka fita kake min magana, amma yau ka™i, gaba Waya zuciyata babu daWi sai ji nake kamar wani abu ne zai faru, dan Allah Habiby idan wani abu ya faru ka faWa min dan Allah ko zan sami nutsuwa a zuciyata.

Ya yi shiru kusan minti biyar baice komai ba, sai da na sake cewa.

Habiby&

Na am.

Menene?

Babu komai fa Habibty, kawai ina mamakin yanda kika Waga hankalinki, kika hana kanki nutsuwa kina ™asa mai tsarki, kinsan dai duk runtse duk wuya ba zanyi wani abu da zai ba™antaki ba, bazai Sata miki ba, dan haka Habibty ki sawa ranki salama dan Allah.

Bangane ba fa.

Habibty babu abinda ya faru, dan Allah ki nutsu ki yi ibada, sauran lokaci ™alilan ya rage miki, dan Alla ki cire komai a ranki, ki kwantar da hankalinki, ki yi ibada kinji, koma menene idan kika dawo nasan zamu magance shi ko?

Me zamu magance kuma? Ni banaganewa.

Ki kwanta ki yi bacci kinji, da safe zan sake kiranki kinji.

Uhmmmmm.

Habibty.

Ya kira sunana, na amsa da.

Na am.

Ya sauke wata ajiyar zuciya, sannan ya ce.

Ki yi ha™uri, ni banyi wani abu da zau Waga miki hankali ba ko ya Sata miki rai, ina so dan Allah ki kwanta kinji, babu wani abu.

Tom.

Na faWa tare da kashe wayar, a lokacin kuma twins da Hajiya suka shigo, su sai lokacin suka dawo, Hajiya ce ta yi min wani kallo.

Wai ke mene haka? Kukan me kike yi? Šazu ma haka na ganki wata kala.

Babu komai Hajiya.

Koma mene ni dai na faWa miki, ki mayar da hankali akan gajeren lokacin da ya rage miki a wannan ™asar, bamu da tabbacin sake dawowa, bamu da shi. Tayu wata shekarar duka bama raye, tayu bamu samu damar zuwa ba ne, yanzu ma ba wayon ba dabararmu ba ne ya kawo mu, Allah ne ya kawo mu, dan haka ki mai da hankali ki yi ibada, ki ro™i Allah Ya baki zuri a idan ya baki ki ro™i shi ya baki na gari, idan ya baki ya yi miki tarbiyarsu, ki ro™i shi ya baki lafiya, arzi™i da ilimin da zaku amfanar da al ummar annabi, amma ba wai ki zauna kina kuka akan abun duniya ba, akan wani kishi na banza marar amfani ba, nasan duk abinda kike jin yana damunki bazai wuce kishi ba, wanda shaiWan yake so ya kitsa miki, sabida karki yi ibada. To tun wuri ki mi™e, ki cire komai a ranki ki yi ibadarki na faWa miki.

Tana gama faWin haka ta nufi firji ta buWe, twins suka yo kaina suna faWin.

Maamah, ina papa.

Na ce.

Yana gida, muma mun kusa komawa, kuxo ku kwanta.

Na tashi na canja musu kaya, bayan nasu sunyi alawala na kwanatar da su, Hajiya bata sake ce min komai ba ta tada sallolinta, ni kuma na kwanta ina ta faman tunani a zuciyata, na sa™a wancan na kwance wancan, duk tambayata me ya kawo kishi cikin raina, bayan babu wani abu da ka ayi da zai kawo shi.

Legenspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(13).

Washe gari haka na tashi still dai raina ba daWi, ina yin karin kummalo na nufi massallaci na fara sallah, ina addu o da ro™on ubangiji da ya sanyaya min zuciyata, ya kuma bani zuri ah ta gari, sai da na yini a massallaaci sannan na dawo hotel Winmu, duk da ina son na fara shiga siyayya ta kayan da zanyi na tsaraba, tun daman ina da kuWin a ajiye, wayata na duba naga missed call Win Turaki, ban kira shi ba sai na yi masa message a whatsapp na ce.

Naje massallaci ne, yanzu na dawo.

A take ya yi min reply da.

Habibty kin tashi lafiya?

Na ce.

Alhamdulillah, ka fita?

Ya yi min reply da

Ina gida.

Na ce masa.

Tom, yanzu zamuje kasuwa mu fara siyayya, suara kwana biyar mu dawo.

Allah Ya dawo min daku lafiya, idan anjima zmauyi waya.

Na ce.

Tom shikenan.

Na faWa tare da tashi na shiga bayi na yi wanka na fito na shirya na Wau twins muka nufi kasuwa, ba mu yi wata siyayya ba mussaman da naga kayan basu da wani bambamci da nan nigeria mussamman idan ka haWa da kuWin jirgi, haka na tawo gida ba tare da na yi siyayar da na yi niya ba, ina zuwa naga Hajiya bata nan ta tafi massallaci, ina zama na yi sallar la asar na yi wa Turaki magana, nasan lokacin bakwai ta kusa a nigeria.

Bai amsamin ba ya kira ni a waya, yana kira na Waga muka gaisa ya ce.

Duk na ™agu ku dawo, na yi matu™ar kewarki.

Na yi murmushi, sannan na ce.

Ni kaina na yi matu™ar kewarka Habiby, ji nake kaman na yi tsuntsu na dawo nigeria.
Chapter 14 · 0% Book details