← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 32

Sashe 10

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani ma aikaci ya faWa, tsayawa muka yi baki Wayanmu, a lokacin aka fito da Bilkisu tana wani irin kakari, ga jini yana zuba daga jikinta me Woyi.

Wannan ku Wauke ta ku kaita asibiti, an cire ta daga case Win gaba Waya.

A take Hajiya Zinariya ta ce.

Ai wallahi a a, Bilkisun Win ita ce fa take amso ™wayar, kawai akai ta ta yi jinya an yanke mana hukuncin mu anan.

Kin tabbata ita ce?

Wani ya tambyae ta, ta gyaWa kai.

Na tabbatata ita ce.

Shikenan you can go, idan wani abu ya sameta dai zamu nemeka, idan kuma ta mi™e shikenan tin da ka sake ta har saki uku, ka raba komai tsakaninku, Allah Ya saka ma.

Babban jami in ya faWa, ita kuma aka sa ta a wata mota aka yi asbiti da ita, a motar muka koma shiru ba wanda ya ce komai sai sautin kukan Sardauna kawai, yanayi yana jan hanci abun tausayi.

Turaki.

Sardauna ya faWa, Turaki ya kalle shi ya ce.

Na am.

Dagaske ne abinda Bilkisu ta faWa? Na tuna ranar da aka je wannan zaman Momy ta ce halin uwata na yi, wai barewa ba ta yi gudu Wanta ya yi rarrafe, tun a tasowa ta na san ni ba Wan Mommy ba ne, akwai lokacin da muka je bikin a danginta na ji suna zagi na, suna cemata sannunta da ri™e Wan ri™o, na yi tunanin Daddy mahaifina ne, mahaifiyata ta rasu shine na zauna a hannu kishiyarta, shi ya sa a lokacin ma da ta ce barewa ba ta yi gudu Wan ta ya yi rarrafe ba na yi tunanin abinda take nufi kenan, amma a yanzu kalman Bilkisu sun tsaya min a rai, dan Allah ka faWa min gaskiyyar komai.

Sardauna, nima banda masaniya akan komai, amma ka tambaye su Big Daddy zasu iya sanar da kai, ko su granny, amma mene amfanin binciken? Idan ma ba haka ba ne idan kasani me zai canja? Zaka je ka nemi iyayenka na asali ne? Ko zaka bar gidan Ta Ambo? Sardauna abinda ya wuce ya wuce, ka fuskanci abinda zai zo maka gaba, rayuwar ka ka gina ta akan ginin son zuciya da son rai, ka tsani kowa ka raina kowa, a yanzu sauran lokacin da kake da shi ka yi amfani da shi ka gyara abinda ya rage maka, cuta ce aka ce jikinka, ya kamata ka mai da hankali ga lafiyarka, ka gyara komai, ka shimfiWa sabuwar rayuwa da ragowar lokacin da ya rage maka, binciken da zaka yi ba lallai ya haifar maka da Wa mai ido ba, sai dai ya dawo da kai baya a tsarim rayuwarka, ba ka da sauran lokacin Satawa Sardauna.

Amma nasan asalina Turaki, nasan iyayena.

Ba zan hanaka ba, amma ina shawartarka da ka bar abinda ya wuce ya wuce, ka fuskanci abinda ke gaba kawai.

A haka muka ™arasa gida, lokacin sha biyu ma ta kusa, ba mu yi wata magana ba muka kwanta. Washe gari da safe ma haka ba mu sami damar yin wata maganar ba ya shirya ya fita, nima na shirya twins na kai su inda nake kaisu na wuce asibiti. Babban labarin dake tashi a asibitin shine na wata mara lafiya da aka kawo ta yi kara duka hannyenta biyu da ™afarta Waya, sannan ta na fama da cutar ™uraje a jikinta ta na wannan halin a Waure amma faWi take asosa mata a sosa mata, ga jini dake zuba daga jikinta kuma a haka shari a ake yi da ita, zancem sai ya Wuwa yake cikin asibitim ko ina yaWa shi ake yi, ga case Wim nasu ya bazu a social media cewar an kama mata masu zaman a gidan kansu suna maWigo da siyar da ™waya. Hotonan su sun zagaye media ga cutar da suke Wauke da ita har da dukan da Sardauna ya yi wa Bilkisu akam cutar da ta kwaso, komai ya zagaye media, mutane da suka dinga yawo sa hotonan su an aure ya sune suke yawo da zancen sakin da kuma cutar da ta shafa masa, cikin lokuta kaWan komai ya bazu a duniya, mutane sai kirana suke amma bana Wagawa, kiran Yaya Rumaisa da ya shigo yanzu, shine kawai kiran da na Waga, ina Wagawa ta ce.

Ke abinda ke faruwa da tsohon mijinki da matarsa gaskiyya ne?

Kamar tana kallo na na Waga kai, sannan na ce.

Gaskiyya ne Yaya, jiya muna wajen aka yi dukan da sakin, wai Bilkisu yar maWigo ce ga kuma siyar da ™waya, yanzu ta shafu musu cuta.

Ai Allah shi ™ara, ™arshen mace amana kenan, kamar yanzu duniya ta yi ta yawo da hotonansu na soyayya da na aure, har aka yi ta zaginki, yau gashi duniya tana yawo da videon saku da duka, duniya tana zaginsu, sai ga shi a yanzu wata ta Wauko hotonan aurensu da yanzu tana magana akai, har take cewa ™arshen cin amana kenan, dan a yanzu zance ya fita fes na cewa Bilkisu ™awarki ce kuma ke kika nema mata auren Sardauna, har sakin da ya yi miki a ranar auren yanzu ya fita, ga hotonan ku na na taron twins sai yawo suke a media kowa yana miki fatan alheri, ko a haka aka tsaya Nana ki godewa mai sama, da ya yi miki sakayya, shima Sardauna yana nan zaiga sakamako, ni nasan ba iya wannan cutar ba ce sakamakon da zai gani.

Ni Yaya Wallahi tausayi ma yake ban, Sardauna yaga sakamako, Yaya kinsan Sardauna ba Wan asalin familyn nan ba ne? Šan ma aikatan gidan ne suka rasu bayan an haife shi, shine aka ri™e shi a gidan fa.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(9).

Ke Nana ina kika ji wannan maganar?

Wallahi Yaya dagaske na faWa miki, kinga kuwa ai Sardauna yaga sakkayya.

Wallahi ya gani, ni kaina ya fara ban tausayi Nana, amma hakan zai zama izina ga azzaluman gaba.

In sha Allah.

Daga haka na kashe wayar, na ci gaba da aikina. A lokacin summy abokiyar zamana ta shigo ofis Win.

Nana.

Na am.

Yanzu nake ganin labarai, wannan matar tana da ala™a da ke?

Eyh ada ba, amma yanzu komai ya wuce.

Yanzu nake bibiyar labarai, gaskiyya Nana kin sha wuyar aure, Allah sarki.

Amma yanzu Summy sai dai godiyar Allah, ni har mantawa nake da wancan lokacin.

Amma Nana kinsan akwai ™aryar media, dagaske ™awarki ce kuma ke kika haWa aurensu?

Na girgiza kai, sannan na ce.

Bansantaba sai bayan na yi aure, ta zo gidan ta ce anan baya take tana so mu zama ™awaye. To kinsan amarya ba yara ba kowa zaman kaWai ce duk ya isheni, na amince mata ta fara zuwa har ta zama ™awatah, kuma bani na haWa aurensu ba, tun kafin nasanta da soyayyarsu a ™asa, tin da shi ya turo ta, kawai suny amfani da wauta tace na shiga abun na haWa auren, kinsan lokacin ina da ™ana nan shekaru ko 20 ban rufa ba.

Allah Sarki na tausaya miki Nana, Allah Yasaka miki.

Haba Summy, wace sakayya kuma? Ni yanzu ai na yafe musu tuntuni.

Hakane kuma Nana, amma dai still akwai wani abu shima ina jin shi kamar ™aryar media.

Mene?

Wai a ranar da aka Waura auren aka saki ki? Kuma wai kin shiga difreshon sabida sakin?

Na yi murmushi sannan na ce.

Ranar da aka yi auren ya sake ni, amma zuciyata ta kasa karSar hakan shine ya haifar min da cutar.

Allah Sarki Nana.

Ta faWa, ni kuma na mi™e ma fita ba yanda zuciyata bata raya min ba amma ba nakasa zuwa wajen Bilkisu haka na koma gida, sai dai babban abun mamaki shine, hirar da muka yi da Summy ashe recording ta yi, cikin ™an™anin lokaci hira ta bazu a media, ina ganin haka na kira Turaki na faWa masa, nan ya hau da ni faWa me ya sa na saki baki aka yi hirar.

Cikin kwana biyu zance ya yi trending ko ina ka duba wannan maganar ake, wasu su yi ta gidan da aka kama, wasu su yo ta dukan Bilkisu, wasu su yi ta cutar da Sardauna ya yi min, sai da ya zama idan na zo asibiti mutane zuwa suke kallona, sabida yanda zancen ya yaWu a kafafen sada zumunta, a gida kuwa Sardauna yana ta fama da jinyarsa, dan Turaki ne ma ke ™o™ari wajen sama masa magunguna na ciwon, sabida a yanzu ™uraje ne masu ruwa suka fito masa a jiki, su ka cika ko ina, duk rashin imanin ka kaga Sardauna sai ka tausaya masa, ba mata, ba ya, ga ciwo, ga ba asali, duk da shima bai da wani tabbaci akan rashin asalin nasa. Amma gaba Waya ga canja kullum cikin kuka yake, duk da ni ban taSa zuwa inda yake ba ko sau Waya. Sai da su Big Daddy ma suka ga ciwon suka haWa shi da babban likita anan nigeria, idan ba a sami sau™i ba zasu wuce ne ™asar waje.

Ranar wata lahadi da safe, muna zaune kan dinning muna breakfast, ni da Turaki da Twins Win mu wayata ta fara ringing, ina dubawa naga Yaya Rumaisa na Wauka ina faWin.

Hello Yaya.

Nana, duba wani video da na tura miki.

Tom.

Na faWa tare da kashe wayar na kunna data, ina shiga na ji labarin wai kotu ta yankewa su Bilkisu zaman gidan kaso na shekara 20, a fili na furta.

Innullahi wa inna illahir raji un.

Turaki ya ce.

Me ya faru?

Habiby ka ji wan an yakewa su Bilkisu shekaru 20 gidan yari.

Daman ai wannan ne hukuncinsu.

Amma Habiby kaman fa ba sa hannunta a abun.

Eyh tayu ba sa hannunta, domin ita matar nan da dukkam alamu sharri ta yi musu, amma idan kim tuna ha™™in rai ne fa akanta, ga wasu abubuwan da take yi, yanda ta azabtar da mijinta ai Allah bazai barta ba.

Hakane kam, Sardauma ua wahala wajen Bilkisu ba ™arya, ga ciwon da ta shafa mai. Kai Allah ya yi mana mai kyau.

Amin Habibty, dan ma a yanzu an samu sau™in cuwon, ™urajen sun daina ruwa, kuma sun daina masa zafin, sai sai ga sunan faca-faca.

Allah Sarki, Allah Ya bashi lafiya.

Amin Ya Allah Habibty.
Chapter 10 · 0% Book details