← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 32

Sashe 12

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faWa tare da kashe wayar, na yi shiru na tsurawa wayar ido, ko ciwon ™wa™walwa ne yake son kama Sardauna kamar yanda ya yi min? Ko da yake ance shi surutai yake, Allah Ya sau™a™a masa na faWa tare da mi™ewa, ni zuwa asibitin nema na gaji da shi, shi ya sa na daina zuwa gaba Waya, amma idan Turaki bai dawo ba kam zanje yau zuwa dare, tashi na yi na shiga Wakinsu twins suna ta wasan mu. Suma jira muke mu koma sabon gida sai a sanyasu a makaranta tun da a yanzu sun kawo shekara uku, bayan na gama basu abinci na dawo falo na Wau wayata, na yi mamakin ganin tarin uban missed call daga yan gidanmu, haka kawai na ji gabana ya faWi sabida yawan kiran, a tsarin yan gidanmu ba sa taSa yi wa mutum kira sama da biyu amma yau wajen kira bakwai daga mutum Waya, ina cikin tunanin na ji wani kiran ya sake shigowa, ban ma tantance mai kiran ba na Wauka.

Hello.

Nana, ina kika sanya wayarki ana ta kira?

A muryar nagane Yaya Radiya ce, na ce.

Yaya na bawa twins abinci ne.

To kinji Hajja ce Allah Ya yi mata rasuwa.

Ya salam, yaushe?

Yanzu haka ma ni ina hanya.

Bari na faWa ma Turaki, yanzu zan tawo nima.

Tom.

Ta faWa tare da kashe wayar, na kiraTuraki bai Wauka ba, kawai na sanya Hijab Wina na Wauki twins na kai su gidan mai rainonsu na faWa mata kakata ce ta rasu idan na dawo yau to, idan ban dawo ba su kwana, na Wauki kuWi dubu biyar na bata, daman kuma suna da kayan abinci a gidan. Sai da na ™arasa gidan Turaki ya kira ni, hayaniyar da ya ji kasancewar glass din motar a sauke yake ne yasa shi cewa.

Habibty me ya faru? Kina ina?

Hajja kakarmu ce ta rasu.

Ya salam Allah Ya ji™anta, ™arfe nawa za ayi janaizar?

Yanzu nan za ayi.

Tom Habibty gani nan zuwa.

Ya faWa tare da kashe wayar, ni kuma na fito daga mota na shiga gidan, su Yaya Radiya da sauran yan uwa sai kuka suke, nima dai mutuwar ta taSani amma ko Wigon hawaye bana ji a idona, to ni ba wata sha™uwa a tsakaninmu, daman sabo shine babban abinda ake yiwa kuka, shi kuma sabo sha™uwa ke kawo shi, har mamakin yansa Yaya Radiya ta zauna tana ta zubar hawaye nake, haka Yaya Rumaisa ma idonta ™amas, ni yanda take rarraba idanu ma yasa na kusa fashewa da dariya. Muna zaune a gidan aka yi wa Hajja suttura aka tafi da ita, bamma san Turaki yazo ba sai da suka dawo suka shigo, bai wani jima ya koma asibitin, washe gari naje gida na Wauko twins na dawo, sai bayan addu ar uku sannan muka dawo gida, a ranar kuna na ce zanje naga Sardauna, a yanda Turaki ya ce abun na shi ma gaba yake yi, sai dai naga kamar yana Soye min ma wani abu, sai dai ganin bani da ala™a da Sardauna yasa ban damu ba da komai ba, da daddare wajen ™arfe takwas na je asibitin, Turaki ma kawai ganina ya yi asibitin, ban ™arasa shigowa ba ya ce.

Habibty me ya kawo ki?

Ganin yanda ya nuna damuwa yasa na ce.

Lafiya Habiby?

Lafiya kawai bana son kowa ya ganki anan ne.

To me ya sa?

Kawai.

Ah, Anty Nana kin dawo?

Afrah ™anwar Sardauna ta faWa, na kalle ta sannan na ce.

Eyh na dawo.

Ya ™arin ha™uri? Ki shigo mana.

Ha™uri Alhamdulillah.

Na kalli yanda Turaki ya haWe rai, na ce.

Komawa zanyi.

A a bazaki koma ba, bakisan nemanki ake yi ba? Jiya Big Daddy ya ce za a biki kanon.

Kano kuma?

Kakar taku da ta rasu ko ba a kano ba ne?

A kano ne.

Na faWa ina kallon Turaki,

Shige mana, kin wani bi ni da ido.

Ya faWa yana harara Afrah, na ce.

Tom, Afrah muje.

Afrah ta yi gaba, ni kuma na tsaya a baya.

Wai mene ya faru?

Na tambaye Turaki ™asa ™asa, ya watsa min harara sannan ya ce.

Ke kika sani, sai da na ce kar ki zo amma kika ™i, duk abinda ya faru ke kika sani.

Habiby mene zai faru?

Oho miki.

Ya faWa ya yi gaba, kamar mara laka haka nake takawa har na shiga babban Wakin da kowa ke zaune, a take ido ya yi kaina, Lamrah ta ce.

Yaushe kika dawo?

Yanzu nan.

Na faWa, duk da na rasa gane kan zancen baki Waya, nan fa kowa ya yi min sannu da dawowa, na ce.

Ya mai jikin?

Mai jiki da sau™i, dan Allah tashi ki shiga ki ganshi, kullum ba shi da aiki sai kiran sunanki.

Sunana kuma?

Na faWa ina mi™ewa, Turaki ya biyo bayana muka shiga, Sardauna na kwance akan gado idonsa a rufe, a hankali na taka inda yake na zauna akan kujerar dake gefe Turaki ya ce.

Sardauna.

Da sauri ya buWe idonsa ya ce.

Turaki dan Allah ka kawo min Nana, wallahi zuciyata zafi take min, ka taimakamin naga Nana ko zanji sau™i a zuciyata.

A hankali Turaki ya ce.

Ga Nanan anan.

Da sauri ya buWe ido ya ce.

Nana, Nana, Nana.

Ya tashi ya kamo hannuna ya ri™e da ™arfi, na fara ™o™arin ™wace hannuna amma Sardauna ya ri™e katamau. Idona na kai ga Turaki, naga yanda ya haWe rai, fuskarsa ta yi wani ja, haka idanunsa. Na ce.

Sardauna, cika ni mana.

Ya ™ara ri™e ni katamau, ya ce.

Nana, ina sonki dan Allah, Nana ki ce kina sona, zuciyata zafi Nana.

Na kau da kaina gefe, ina ™o™arin ™wace hannu na ce.

Sardauna hannuna zafi, Habiby kazo ka ce ya sake ni.

Tsa™i ya ja ya mi™e ya fice, a raina na ce. Innullahi wa inna illahir raji un, ni Nana naga masifa.

Nana dan Allah.

Tom Sardauna, ka nustu ka cika ni ka ji.

Sardauna dai ya gagara cikani, ba yanda banyi ba amma abu ya ci tura, har sai da na fara ihun neman ceto, da sauri su Lamrah suka shigo suna faWin.

Me ya faru?

Hannuna na nuna musu da Sardauna ya matse, duk suka fara cewa.

Ka cika ta mana.

Kira min Turaki dan Allah.

Afrah ta fito tana faWin.

Yaya Turaki ya ri™e mata hannu fa.

Ba shiri su Mama Amina suka shigo, ganin yanda Sardauna ya ri™e min hannun katamau yasa suka fara ™o™arin ™wace ni, da ™yar aka fusge hannuna daga jikin Sardauna. Ana ™wacewa na mi™e na fice ina haki sai kace wacca ta yi tseren gudu, ina fita na ga Turaki ya haWe rai, na nufo shi ya yi gaba ya ™yale ni, nima na bi bayan shi na tadda shi a mota, har muka isa gida bai ce dani ci kanki ba, duk yanda na so na yi magana da shi amma ya™i, da na matsa masa ma ya hau faWa, ta inda yake shiga bata nan yake shiga ba.

Kinji daWi ko ya ri™e miki hannu, shine daman abinda kike so to ya ri™e.

Haba Habiby, ya za ayi na so ya ri™e min hannu? Kana ganin fa yanda aka yi da shi.

Tun da ya farka yake kiran sunanki, yake wasu maganganu wai yana sonki, kinji zafin da nake ji? Na faWa musu rasuwar Hajja, na ce musu akano ne, amma daga dawowarki shine kin kwashi ™afa kin tafi, daman hankalinki yana kansa ko? To gashinan kingan shi ya ganki, ya ce yana sonki, ya taSa miki hannu, sai kuma me ya rage? Ko so kike kema ki ce kina son sa? Daman ba yau kika saba faWa ba.

Haba Turaki! Me na yi duk da zaka dinga faWan waWan nan maganganun? Nasan halin da yake ciki? Komai fa Soye min kake? Dan shi naje wajen? Na je ne fa dan ka ci abinci, kwana nawa bana ganinka, nasani kana ci ko baka ci, shine naje amma kake min wannan abun, dan ya ce yana sona to sai me? Sai aka yi me? Ni son sa nake? Me ya sa kake min haka ne?

Ni kike faWawa waWan nan maganganun? Ni kike wa magana da tsawa haka?

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(11).

Ni ba wani abu da na faWa maka, kaine gaba Waya ka rufe ido, ta inda kake shiga bata nan kake fita ba, da ace tun a farko ka faWa min komai ai da bazan je ba, amma ka rufe komai, nasan me yake faruwa?

To yanzu ai kinje kingane sai kuma me?

Hhhhm.

Na faWa tare da ficewa daga Wakin na koma wani Wakin, gaba Waya Turaki ba shi da uziri akan al amarin Sardauna, ni da ba son sardauna nake ba, ba wani abu ba, ko magana ba yi nake da shi ba, amma gaba Waya ba iya yin uzuri akan abubuwan da suka haWani da shi, ni gwanda ma mu tashi mu bar gidan kowa ya huta, bani da wata ala™a da zata sake haWani da shi. A daren ba nemi Turaki ba shima kuma bai nemeni ba, washe gari ma da sassafe ya shirya ya fita, duk da haka ni ban wani damu ba, yanda yake fushi nima haka nake yin nawa fushin, har rana ba muyi waya ba, ™arshe ma asibitin ya kwana, wannan ita ce rana ta farko tun auren mu da muka taSa yini tun safe har dare har kwana ma wani bai nemi wani ba, amma dai still haka na jure na ce naji na gani, dan banyi komai ba bazan Wauki laifi ba wallahi, mu yi ta fushin har atashi duniya, sai dai tun kwana na Waya, da na biyu na ji bazan iya ba kwata kwata, ina zaune a Waki na rasa me yake min daWi, gashi tun da ya zo sau Waya bai sake zuwa ba, waya ta na Wauka na danna lambarsa, sai dai har ta gama kukanta bai Wauka ba, takaici ya isheni da haushin kaina, me ma ya sa na kira shi, ba fushi muke ba mu yi ta yi.

Wajen minti 20 sannan ya kira ni, kamar ba zan Wauka ba dai na Wauka, na kuma yi shiru bayan na Wauka.
Chapter 12 · 0% Book details