← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 32

Sashe 18

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana wai mene haka? Ke kina tunanin akwai wani kuWi ko wani abu na duniya da zamu so da yar uwarmu? Nana muma fa matane mun san komai, munsan raWaWi da dukkan zafin kishi, amma baki tsaya kin saurari Turaki ba kamar yanda muka saurareshi, kuma a lokacin sai da muka ce dashi idan kin amince zaki zauna da shi haka muke so, idan baki zauna ba haka Allah Ya yi, amma zamu nusar dake cewar zama da auren yafi zama babu auren, amma wallahi bamu zaSi abin duniya sama dake ba Nana.

To ni bazan zauna ba ya sake ni kawai, kinsan irin al™warin da ya dinga yi min? Yana cewa zai zauna da ni ko babu haihuwa, ni kaWai ce a zuciyarsa, ni kaWai yake so ashe duk ™arya ne. Ni Soye Soyen da ™aryace ™aryacen da ya yi min sunfi ™ona raina, haba baya sonta ya tare da ita, a baya son nata ya yi mata part daidai da nawa, a baya son nata zaki ga ta haihu, maza munafukai ne, duk halinsu Waya wallahi, natsani Turaki ko sunansa bana son tunawa, SARTSEN da Turaki ya yi min yafi wanda Sardauna ya yi min a rayuwa.

A a Nana babu haWi wallahi, kawai a yanzu kina cikin zafin zuciya ne, amma idan kika nustu kika sami sau™i komai zai daidaitar miki in sha Allah Nana, mu dai yan uwanki ne, kisani a ko wanne lokaci muna tare da ke, kuma zamu kasance tare dake, kuma zamu tsaya miki mu baku dukkan ™warin gwiwa da ™arfi a dukkan hukuncin da kika yanke.

Zuciyata ta yi rauni, jikina ya yi sanyi sosai da sosai, na ce.

Na gode Yaya.

Bakomai Nana, ki ci abincin kinji.

KarSar abincin na yi na fara ci, duk da bakin babu wani daWi babu WanWano haka na dinga tusa abincin kamar in shan magani, a haka na ci abincin sosai, ima cikin cin abinci Yaya Ridwan ya shigo ya kalleni, ya kira sunana.

Nana!

Na Waga kai na kalleshi, shima kallona yake sannan ya ce.

Turaki ya ce ba sake ki ba, da gaske ne ko a a?

Bai sake ni ba, amma na ha™ura da aurensa kawai ku ce ya sake ni.

Kina ganin sakin yafi?

Eyh yafi.

Shikenan, gashinan a waje idan ya shigo sai ki faWa masa, duk yanda kuka yanke.

Ya faWa tare da fita, Yaya Radiya ma ta Wauki plate Win ta fita, yana shigowa twins suka yi kansa suna faWin.

Papa.

Ya rungumesu ya ce.

Twins Win papa.

Papa Good morning.

Morning daughters.

Maamah Papa.

Suka faWa suna nuna min shi, na watsa musu uwar harara na ce.

To ba ubanku ba ne, ku matsa daga kusa da shi.

Na faWa ina janyo su, ya ri™e su yana faWin.

Haba Habibty, mene haka?

Banza na yi da shi na ci gaba da jan ya yana, su kuma suna wani manne masa kamar cingam, sai da na daka musu wata uwar tsawa na ce.

Dan ubanku ku cika shi, baku da wata ala™a da shi ta kusa ko ta na nesa, ba ubanku ba ne kuma ba mijin uwarku ba ne.

Ba shiri ya cika su ya matso kusa da ni, na mi™i ina shirin matsawa ya kama hannu.

Habibty dan Allah ki saurareni, mene amfanin wannan duka, me ya sa kike haka ki tsaya ki fahimce ni ki yi min adalci dan Allah.

Na fara ™o™arin fisge jikina ina son mi™ewa, ni ko magana sa shi ma bana so, kallon fuskarsa ma bana so, gaba Waya kamar annu sanya min soyayyar Turaki a zuciyata zuwa zazzafar ™iyayyarsa, na ci gaba da mutsu mutsu na ina son ™wacewa.

Wai bazaki ji ni ba?

Na gyaWa mai sa kai kawai, dan bazan iya magana da shi ba.

Habibty karku hukunta nu ta hanyar ™aurace min, ki yi min ko wanne hukunci ne dan Allah, amma karki haramtamin kanki, karki haramtamin ganinki, idan babu ke ban san idan zan kama ba, bansaniba.

Ji na yi inama zan iya yin magana da shi, na ce masa Yakama ko ina, da na faWa masa maganganun da bazai iya Wauka a kunnesa ba, da na faWa masa zallan ™iyayyarsa da nake ji a zuciyata, amma tabbas shiru na shine alheri a gareshi, ya cika ni ya sake ni kawai, domin bana son sa ko Wis a cikin zuciyata.

Ki yi magana dan Allah, ki ce wani abu Habibty, idan baki yi magana ba shirun zai azabatar da ni, shirun ki azaba ne agareni dan Allah.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(17).

Da ™yar na iya buWe baki na ce.

Ka cika ni Turaki, ka sake ni dan Allah.

Ya girgiza kai ya ce.

Dan Allah a a Habibty bazan iya ba, bazan iya rayuwa babu ke ba, ki ce farin cikina, ke ce dukkan rayuwata dan Allah.

Turaki na gaji da waWan nan kalaman yaudarar naka, nagaji da wannan kalaman naka na ™arya wallahi nagaji, bazan iya Waukan son zuciya irin naka ba, ka sake ni kawai dan Allah.

Habibty bazan iya ba, bazan sake ba wallahi.

Wallahi sai ka sake ni kaji ma na rantse.

Haba Habibty me ya sa zaki yi min haka, ki yi min kowanme irin hukunci ne amma banda wannan, bazan iya Wauka ba wallahi, ko kusa ko alama bazan iya rayuwa babu ke ba, bazan iya ba, ke nake so ke kaWai ke ce nake so, ke ce a raina.

Ni kaWai kake so ka aureta? Ko iya ya ya kake si ta haifa ma? A baka son nata ka yi mata part tun a gina gidan? A baka son nata ka ajiye ta a gidanka ka tare da ita? A baka son nata zata haifa ma ya ya, namiji ne fa kai Turaki ™anin ajali, ko Islaha ma da kanka ka ce bata baka fuska ba amma ka je wajenta, shine yanzu za ka raina min hankali, zaka zo ka ce zaka yaudare ni da wasu kalaman na ™arya? Ai ™aryarka na gama Wauka, na Wauki waccan zan Wauka, ka ce da ni zaka rayu da ni, zaka mutu dani da haihuwa ko ba haihuwa, amma duk ka kasa, wallahi ka cutar dani ka azabtar da ni Allah Yasaka min, amma wallahi Turaki ki kaWai ka yi saura a duniya na ha™ura da kai, na ha™ura da aurenka.

Wallahi Habibty ba son ta nake ba.

Na Waga masa hannu cikin fushi na ce.

Dakata Turaki, nagaji da jin waWan nan maganganun wai ba sonta kake ba, idan baka sonta shi wanda ya aura ma ai yana sonta, kuma baya sona, to Turaki na bar muku ahalinku, ai ba dole sai na rayu cikinku ba, ko da dole? Wallahi Turaki ganinka ma bana son na yi, ka yaudareni.

Habibty ban yaudareki ba wallahi, ki yi ha™uri.

Ka sake ni saki uku, sannan ka tashi ka fita zama da kai nagama har abada, duk halinku Waya, maza mugaye ne ku kanku kawai kuka sani.

Haba Nana, wallahi ban kanmu muka sani ba, munsan kowa, nasan abinda ya faru ba a kyauta miki ba, an cutar dake, amma dan Allah k saurareni ba abinda ba shi da mafita, wallahi a shirye nake da na yi duk wani abu da kike so wanda zai sanya ki farin ciki wallahi. Kece nake so ke Waya babu wata, a yau da gobe da jibi har abada Nana, dan girman Allah karki hukunta ni ta hanyar cewa na rabu da ke, wallahi bazan iya ba.

Ai daman bazaka iya ba.

Na tare shi cikin fusata, sabida jin yanda kalamansa suke neman raunatar da banzar zuciya irin tawa, su maza da sun sami raunin mace shikenan ta kaWe, ta bushe.

A son zuciya irin naka sai ka ™ara min kishiya kuma ka ce na ci gaba da zama da kai, wai kana sona, ni kaWai ce a ranka, as how? Idan nu kaWai ce a ranka zaka zauna da ita tun tafiyata, kana bata ci, kana bata sha, kana bata dukkan lokacinka, kai burinka ta haifa ma ya ya, to sai mene wai a ciki? Ni bana haihuwa haka Allah Ya yi dani, bani na Waurawa kaina ba Allah ne ya Waura min, ta sanadiyar Wan uwanka me son zuciya, amna ko haka baku gani ba, da shi Big Daddy da ya aura ma, idonku ya rufe ku sami jika to Allah Ya bada masu albarka, au daWinta ba ita mata bane basa haihuwa, akwai maza da yawa da basa haihuwa, zanje na nema cikinsu mu yi auren mu babu wani tashin hankali ba hayaniya, ba ™iyayya daga yan uwa miji, me na yi masa da yatsaneni haka? Wani laifi na taSa masa bayan ma duk kune kuka yi min laifi, amma ya tsaneni kuma ya yi al™warin ba zan zauna a gidan mijina ni kaWai ba, to daWinta shima ya haifi ya yamata gasu Seemah da Lamrah nan, bana fatan ha™™ina ya bi su tunda basu yi min komai ba, amma tabbas idan ina da ha™™i akan Big Daddy sai Allah Ya yi min sakayya, sabida wani girma da Allah Ya bashi a cikin ku sai ya ce ga yanda yake so ayi, wannan mulkin mallakane ko me? To ni bazan iya ci gaba da zama a ™arkashin mulkinsa ba, wallahi ko sabida Big Daddy dole na ha™ura da kai, nagaji da wannan wahala rayuwa, gaba Waya aure wahala ce a gareni, damuwa ce, dame zanji, ko da lalura da aka ™a™abamin ta isheni, ta isa ta sani a damuwa. Ina son naji daWi a rayuwata nima, ina so nasan cewa ni macece mai yanci, na gode maka sosai da ka yi namijin ko™ari wajen tabbatar min da farin ciki, amma a wannan gaSar tabbas bazan ha™ura ba, nagama aure da kai Turaki, ga amarya can Allah Ya baku zuri a ta gari Wayyaba.

Wallahi bazan iya rabuwa dake ba, zanyi komai da na saki farin ciki, zan ha™ura da komai da na rayu dake ne, ko da kuwa ya yan da kike tunani ne, zanje na yi abinda nima bazan haihu ba shikenan ko? Sai mu yi ta zama ba ya yan, twins sun ishemu.
Chapter 18 · 0% Book details