← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 32

Sashe 13

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hello, salamu alaikum.

Wa alaika salam.

Na faWa murya ciki-ciki, sai kuma na ce.

Bansan na danna kiran ba.

Tom.

Kawai na ji ance, sannan aka kashe wayar. Hhhm. Na sauke ajiyar zuciya na ce.

Lallaima Turaki, ya yi abinda ya ga dama, dan yaga yana jinya shine zai zo min da wannan salon to daidai nake da shi.

Da yamma lis na sake shiryawa zan tafi asibiti, ina ™o™arin fita nagan shi ya shigo, na matsa ma ya wuce ni kuma na nufi ™ofa.

Ina zaki?

Ba tare da na juyo ba na ce.

Zanje asibiti mana, ko an sallameshi ne?

Asibiti kuma Nana?

Eyh asibiti.

To adawo lafiya, Allah Ya tsare.

Na ce. Amin. Na nufi hanyar fita, aikuwa ya yi sauri ya jawo ni.

Wai Habibty mene haka?

Me na yi? Naga kaine ka daina sona, ka zaSi zama a asibiti da Sardauna ka watsar dani, to nima ba sai na koma asibitin ba.

Lallai, baki ga abinda kika yi ba kenan?

To ai kai&

Ya wuce Habibty, amma kar a sake, na ji ba daWi.

Tom.

Ba a sallame shi ba, sun tafi babbban aisibitin Delhi na ™asar indiya, ciwon na shi sai addu a kawai.

To Allah Ya bashi lafiya, Allah Yasa kaffara ne.

Amin Habibty, na yi kewarki.

Bawani nan, Wazu wai ka kashe min waya.

To kin ce ba ni zaki kira ba, shi ya sa. Wait wai wama zaki kira?

Mijina na faWa.

Daidai lokacin twins suka fito daga Waki, suna ganinsa suka tawo da gudu suna faWin.

Papa, papa.

Ya tsugunna ya Wauke su duka, suka mi™e tsaye ya ce.

Yau dai zamune shan ice cream, amma yanzu wanka zanyi na kwanta.

Habiby ba a bacci da yamma fa.

To ni dai sai na yi, yanda nagajin nan.

Amma ana kiran magariba zan tashe ka.

Na yarda.

Ya faWa tare da shiga ciki, sai dai ya yi wanka ya ci abinci kafin ya kwanta aka yi magariba, sai bayan magariba ya kwanta. Ba shi ya tashi ba sai wajen goma saura, lokacin twins ma sunyi bacci.

Habibty bamu fita ba.

Kallonsa na yi, sannan na ce.

Sai bayan isha ka ce ai.

Yanzu ™arfe nawa?

Bakwai saura.

Yawwa, shirya twins din bari na yi wanka.

Tom.

Na faWa duka ban Wauke idona daga kan laptop Wita ba, bare ma na kalle shi.

Ya mi™e ya sauka daga kan gadon, ya Wau wayarsa ya duba.

Kai Habibty, goma saura fa.

Sai a lokacin na tsayar da laptop Win na ce.

Kai ka ce kar na tashe ka fa, zaka tashi da kanka.

Amma da kika 8 ma ai sai ki tasheni.

A a gwanda ka huta, ni ka ga yanzu zanyi nawa baccin.

Na faWa tare da kashe laptop Win, na ajiye ta gefe na kwanta.

Zaki ga bacci kuwa, bara na yi sallah. Idan na dinga tsalle a gadon sai kin farka dan kanki.

Na yi dariya na ce.

TaS, bari na tafi Wakin can.

A a dan Allah, yi baccin ki anan.

Na yi murmushi na kwanta, washe gari da safe tare muka yi aikin komai da Turaki, har na tafi asibiti na barshi gida, wai shi ba zai fita ba yau hutawa zai yi. Wajen ™arfe uku ya zo asibitin namu ya Wauke ni, wai zamuje mu fara duba kayan da zamu sanya a sabon gidanmu, haka muka yini daga wancan shagon zuwa wancan, sai bayan magariba muka dawo gida.

Bayan sati biyu.

Shirye shiryen tashinmu ya yi nisa, kullum cikin siyayya kayan sabon gida muke, mu siya wancan mu siya wancan, ga kuma tafiyar mu tana gabatowa, shirye- shirye sunyi nisa sosai. Haka shima sabon gidan aikin duk ya yi nisa, saura kaWan agama, pary Win da Turaki yake cewa ba zamu zauna ba, shima har nan ake aikin ya yi fes kamar a yanzu za a zauna, kayan gado na duk Waukan su ya yi ya kai su wani company aka yi musu ciko suka bamu sababbi, haka ma kujerun suma aka kai musu, da ba ayi niyar canjawa ba amma ganin sau™i campany yasa muka bada su aka yi cikon, hatta twins suma sai da aka yi musu sababbin kayan Waki, mussaman waWancan na yara ne, waWannan kuma da aka sanya musu ba lallai acanja musu bar sukai shekaru 20, sabida gadon ma na yan mata aka sanya musu, har da mudubi.

Cikin ™an™anin lokaci aka gama gyara sabon gida, aka sanya komai, sannan muka koma aka yi gagarumar walimar tarewar mu, gida ya amsa gida ya ci uban gida, tun daga gidan Sardauna na farko da na zauna, da part Winsa na wancan gidan da muka tashi, da part Win da muka zauna da Turaki, yau kuma ga wannan gidan shima mun dawo, Allah Ya zaunar. Rayuwar mu a sabon gida ta fara tafiya cikin farin ciki, Turaki ya ™ara ninki na kulawa da yake ba ni a wannan gidan, sai na ji kamar sabon gidan nan ya kasance wata sabuwar duniya ta farin ciki, ™aunar gidan ta cika min zuciyata.

Ga wani irin son Turaki da yake ™ara kama zuciyata, nutsuwa ta shegi ne da kwanciyar hankali, bani da wata damuwa a yanzu, ga soyayyar dangin miji. Babu gidan da basayi na babu gidan basa so na, har da gidansu Islaha ma, dan ciwon Sardauna da kuma al amarin Bilkisu ya yi matu™ar ta da musu hankali. Tun daga nan suka kama hanyar gaskiyya, haka Hajiyar Sardauna, daman ita ba mai hayaniya ba ce, kawai dai bata zumunci da Maman Turaki da Mama Amina, shima kuma ta janye a yanzu suna gaisawa. Islaha ta karSi ™addara kuma a yanzu ta shirya idan Sardauna ya dawo zata aure shi a haka, dan duk abinda ya faru har yanzu zuciyarta bata daina son sa ba, sai ma tausayinsa da take ji, dan lokaci zuwa lokaci takan yi magana da ni ta ce, na yafewa Sardauna dan Allah, sai na ce mata bakomai Allah Ya yafe mu baki Waya, danni daman tun kafin yanzu na yafewa Sardauna, dan ban ri™e shi a zuciyata ba, mussaman lokacin da na ji shi ba asalin Wan wannan gidan ba ne, na wanke zuciyata na ci gaba da rayuwa hankali a kwnace babu wata damuwa, ga mutuwar yar sa ga kuma ciwon da ya samu, sannan kuma ciwon da ya samu na ™wa™walwa wanda sanadiyarsa aka fitar da shi waje.

Na sami nutsuwa da kwanciyar hankali, ga kyakywar kulawa daga mijina wanda take Webemin dukkan damuwar da take shirin damuna ta rashin haihuwa, kwata kwata Turaki baya bani damar damuwa akan wannan abun. Ranar da muka cika sati biyu a sabon gida, ji nake kamar na shekara cikin wannan gidan. Mun fara zuwa bita ni da Hajja, banda twins tun da su me suke ganewa ma bare ace za a kaisu bita. Sai da lokacin tafiya ya zo sai na ji gaba Waya bana son yin nisa da Turaki, sai nake jin kamar idan na tafi saudiya kafin na dawo wani abun zai same shi, gaba Waya sai na daina marmarin tafiyar ma. Haka kawai zan sha a gaba nai ta kallonsa, yau ma kamar ko yaushe kallonsa nake yi, sai da ya gaji da kallon ya ce.

Habibty kallon fa?

Na girgiza kai, sannan na ce.

Nifa bana son na yi nisa da kai Habiby, ji nake kamar wani abu zai sameka idan na tafi.

Ya yi murmushi ya taso daga kujerar da yake ya dawo kusa dani.

Habibty babu abinda zai same ni sai alheiri, kawai kewa ce, kinsan ba mu taSa nisa ba, mussana irin wannan wajen wata guda zaki yi.

Kaima da zaka tafi haka ka ji?

Eyh Habibty, naji kewar ku sosai da sosai.

Habiby dan Allah karka yi wani abun idan na tafi, kar ka dinga fita kana yin dare, ni dai gaba Waya na rasa me ke damuna.

Tom Habibty, ki nustu ki kwantar da hankalinki dan Allah, ibada fa zaki yi, ibada mafi muhimmanci a rayuwarki, karki sa wani abu, kar sheWan ya rusa miki ibada fa.

Tom Habiby in sha Allah, Allah Ya tsare min kai.

Amin Habibty.

Haka na yi ta fama da fargaba da rashin nutsuwar zuci, ana zaune sai na ce masa. Yau saura kwana biyar tafiyarmu. Ya kalleni ya yi murmushi, da na sake masa maganar sia cewa ya yi.

Habibty ko dai na biyo ku?

Na girgiza kai na ce.

Ai lokaci ya ™ure Habiby, amma ba inda zan sake zuwa ni kaWai ba tare da kai ba, gaskiyya.

Nima bazan sake gangancin tura ki wani wajen ke kaWai ba, Allah Yasa dai ki iya ibadar nan Habibty.

Na yi murmushi, sannan na ce.

Zan iya mana.

Allah Yasa ayi ibada karSaSSiya Habibty.

Amin Habibyna.

Haka na yi ta fama har Allah ya kawo mu ranar tafiyarmu, tun daren jiya nake kuka, ni da gaba Waya zuciyata babu nutsuwa a ciki, sai nake jin kamar ma ni ce zan mutu acan idan naje, gaba Waya na kasa zama na nutsu.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(12).

A filin jirgi ma dai haka na kasa nutsuwa, hannuna na cikin na Turaki, yan gidanmu da sauran yan uwa sun cika airport, amma ni dai hankalina gaba Wayansa yana kan Turaki, har aka zo lokacin da aka fara tantance alhazai kafin tafiya filin jirgi, Hajiya bakin ta a washe zata koma aikin Hajji ita ta ri™e twins muka shiga cikin jirgi, jirgin kai tsaye madina zai nufa hakan yasa ba musa harami ba, tafiyar awa huWu da rabi ta sauke mu a Filin Jirgin Sama na Yariman Masarautar Mohammed bin Abdulaziz da ke Madina, muna sauka mu ka bi layin tantancewa shima kusan awa Waya da rabi sannan suka sake mu, tun da muka sauka a madina na ji wata nutsuwa ta shige ni, wani sanyin da farin ciki suka lulluSe ni, muna gamawa da masu tantancewa wasu manyan motoci na Kamfanonin sufuri na aikin Hajji karkashin hukumomin aikin Hajji na jihar jigawa suka Wauke mu, bayan an gama yi mana duk abinda ya dace.
Chapter 13 · 0% Book details