← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 32

Sashe 30

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu na shiga Waki na Wauko masa key na bashi ya fita, banyi garajen cewa zan bishi ba, dan nasan ma babu lallai ya ce zai tafi da ni, yana fita nasamu waje na zauna, na shiga tunanin daman yana da hawan jini? Ko da yake yawancin masu kuWin nan ba a rasa su da hawan jini, ta shi na yi na shiga kicin zan Waura girki, sai dai ina kunna gas na ji, wani irin wari ya dake hancina, wanda ya haifar min da wani irin tashin zuciya marar daWi, banyi aune ba na ji amai yana taso min, na yi ™o™arin fitowa na shiga toilet amma abu ya gagara haka na yi ta faman kwara shi anan, ina tsaka da aman na ji ana magana a falo na, ban iya amsawa ba aka shigo, duk da na yi tunanin ganin Anty Adizatu, tun da suka dawo daga kano take cemin zata zo zata zo, sai jiya da dddare take ce min yau zata shigo, har na bata location Win gidan. Da sauri ta shigo kicin Win tana faWin.

Subhanallahi Nana me ya sane ki?

Na fara girgixa ma ta kai sabida jigarta da na yi, ta dafa min baya na ci gaba da kwara aman, sai da na gama sannan ta kama ni ta kaina toilet na wanke bakina, ita ta dawo ta gyara wajen.

Sannu Nana, me yake damunki?

Cikin muryarta dake Wauke da gajiya na ce.

Wallahi lafiya nake, da shiga kicin na Waura girki shine na ji warin gas Win ya dake hancina ya haifar min da tashin zuciya.

Wani kallo naga tana yi min, wanda har sai da na ji na tsargu, sannan ta ce.

Al ada fa?

Bangane ba?

Na ce yaushe rabon ki da period?

Ni da yake wani lokacin sai ki ga ina tsallaken wata Wai Wai banayi, to ban wani fahimta ba.

Last month kinyi?

Na girgiza kai.

Kina da test strip?

Mene haka?.

Na tambayata cike da mamaki.

Abun gwada ciki.

Me zai haWa ni da shi?

Mi™ewa ta yi, sannan ta ce.

Ina zuwa, kaman wani pharmacy nagani anan bakin layinku ko?

Eyh pharmacy ne.

Na bata amsa ta fice, sai da ta fita kuma kaina ya kawo haske, yanzu idan aka ce ciki ne da ni fa? Kai Ya Allah, haka kawai na ji zuciyata ta yi sanyi, na nemi duk jirin da Sacin ran na rasa, ina nan zaune ta shigo da shi a leda ta ce.

Ungo, je ki gwada.

Ya ake gwadawa?.

Idan kika sami fitsarin kadan a cikin wani ™aramin abun da na tawo da shi daga pharmacy Win sai ki tsoma strip din, bayan kin cire  strip Win daga ledarsa, zaki tsoma alamar bakinsa inda aka yi kibiyar nan daga wajen da aka rubuta MAX a cikin fitsarin na tsayin da™i™a 5 zuwa 10. Sannan Kar ki nutsar da shi ya wuce layin MAX din. Daga nan Sai ki Wauko shi ki a ijiye shi a kan wuri madaidanci na tsawon minti 3 zuwa 5.

Tom, amma me zan gani ya zama akwai, me zan gani ya zama babu?

Wai baki sani ba? Kina nufin baki taSa amfani fa shi ba?

To haihuwar nake?

Ta matso kusa da ni, sannan ta ce.

A jikin strip Win akwai layukan nan masu kalolin ruwan hoda, kin gansu ko?

Na gyaWa ma ta kai alamar eyh, sannna ta ce.

Kinga layi biyu wannan yana nufin Akwai ciki Positive kenan, sannan ko da kinga layin na biyu ya fito da haske sosai bai nuna ja sosai ba, muddin yana da Wan dishi-dishi, to akwai cikin. Amma idan kika ga layi Waya wannan yana nufin Babu ciki Negative kenan, layi guda Waya ne kawai na saman control line ke fitowa, kin gane.

Eyh na gane, Allah Yasa ya zama possitive.

Na faWa ina tashi, ta amsa da amin.

Ina shiga toilet na yi dukkan abinda ta gwada min, cikin minti sha biyar da shiga ta na fashe da wani irin ihun murna sakamakon posstive da na gani, ina fitowa falo na dur™usa a ™asa na yi wa Allah sujjadar godiya, na fashe da wani irin kukan farin ciki, wai yau ni Nana ke Wauke da ciki, ashe zan haihu zan ga ya yana, bayan wannan uwar gwagwarmayar, bayan wannan uwar wahalal, na Waga hannuna sama na ce.

Ya Allah, ka bani masu albarka waWan da zasu zama sanyin idaniya na, Ya Allah karka bani ya yan da bazasu bi umarnin ka ba, da bazasu yi koyi da annabinka ba, Allah ka albarka ce su, Ya Allah duk wata mace dake bu™atar haihuwa ka bata masu albarka.

Haka muka yi ta farin ciki ni da Anty Adiza, kafin ta tafi ta tabbatar min da muje asibiti wannan gwajin gida ne, sannan nasanar da Turaki komai amma idan zamu iya mu Soye shi har sai ya kai wani matakim girma, sai da ta ce Turaki na tuna wai ashe Big Daddy ba shi da lafiya yana asibiti, wallahi shaf na manta, sai bayan ta tafi na kira Turaki a waya, yana Wagawa ya ce.

Habibty na yi fushi.

Sorry Habiby, kana fita Anty Adiza tazo kuma zuwanta da wani kyakyawan albishir, wallahi duk shine ya sa na sha afa, Ya jikin nasa?

To da Sau™i za a ce, amma likitocin sun tabbatar da Big Daddy ba zai ™ara tafiya ba, kuma manyan likitocin ne har guda uku da ™asar waje, kinsan ashe shi gwamnati ta yi canciling visa Win shi ba shi da damar sake fita wata ™asar.

Ayyah Allah Ya bashi lafiya, zaka dawo yau ne?

Eyh zan dawo me ya faru?

A a bakomai sai ka dawo.

Yanzu ma Laila ta kira ni wai yau zata dawo.W

To Allah Ya dawo da ita lafiya.

Amin Habibty, ai yanzu ina jin ba za a sami matsala ba, sabida naga yanda jikinta ya fara sanyi da jinyar Aiman.

Allah Sarki Aiman, Allah Ya bashi lafiya.

Amin Habibty.

Jin ™arar shigowar sa™o na yi a wayata, hakan yasa na ce da Turaki.

Tom Habiby sai ka dawo, Allah Ya bashi lafiya.

Ya amsa da amin tare da kashe wayar, sai da na duba wayar na ga ashe sa™on ma ta email aka turo shi, na shiga na duba na ga wai message ne daga wata babbar ™ungiyar NGO s dake da babban rashe a ™asar Chaina, sun turumin sa™on ne suna son na zama babbar wakiliyar su anan nigeria, ™ungiya ce da ke tallafawa mata marasa haihuwa, da kuWaWe, abinci, likitoci da zasu dinga duba su, sannan kuma suna tainakawa mata nakasassu, da kuWaWe, sutura, da likitocin da zasu dinga duba su, a ta™aice dai suna son na zama shugabar gidauniyar anan nigeria, banyi musu reply ba na ce sai Turaki ya zo ya yi min ™arin bayani, duk da dsi banji ma sha awar yi ba, sabida bana son na Waurawa raina abinda zai wahalal da ni. 

Ina zaune na rasa abinda zanyi, na kira Hajiya mun gaisa, na kira Yaya Rumaisa da Yaya Radiya, na kira Yaya Ridwan na kira Ra is, duka mun gaisa kowa sai ya tambayeni me ya faru sun ji muryata raWau, sai da kawai na yi dariya na ce bakomai. Ana idar da sallah magariba na ji shigowar yan uwan Laila, ba shiri na tashi na koma ciki, sabida kar ma na ji me suke cewa bare raina ya Saci. Har suka yi suka gama ina ciki ban ji me suka ce ba, su twins ma na hanasu fita compund su yi wasa na ce duk su yi a Waki, ba dan ran su ya so ba suka yi anan, wajen ™arfe takwas Turaki ya dawo, kana ganinsa ka san a gajiye yake, sannu na yi masa sannan ba shiga na haWa masa ruwan wanka, bayan ya yi ya ci abinci na tanbaye shi jikin Big daddy ya ce.

Habibty wai kin san yana halin wannan jinyar yake magana akan ki, wai ki yi masa alfarama ki yafe masa, ashe abinda ya ja faWuwar ta shi Lamrah ce ta ce masa mugun halin sa yaja musu ba™in jini sun™i auruwa, sannan ta faWa masa kin hana ™aninki aurenta, sabida mugun halinsa. Mama Amina ma ta ce Allah Ya isa abinda ya yi wa ya aynsa, ™arshe ma ta bar masa gidan shine abinda ya faru ya ka shi ga faWuwar, daman kowa ya gaji da halinsa ina jin Hajiya Falmata wai Allah Yasa ya mutu, ko zai bawa mazajen su damar da zasu juta kasuwanci suma, shima duk ya haWa ya ri™e komai.

Duk jikina ya yi sanyi, na ce.

Habiby ba wai dan wani abu na hana Ra is auren Lamrah ba, kawai ina tsoron halin mahaifinta ne kaga yanda ni kaina nake fama da shi.

Hakane Habibty, amma ayi afuwa yanzu a halin da yake ciki ma me zai iya? Ki yi ha™uri dan Allah.

Amaryarka ta dawo fa, sannan ina so gobe zanje asibiti naga likita dan Allah bana jin daWi.

Tom sai muje na kaiki, bari na je wajen amarya.

Tom Alhaji.

Legendspen

08129553971.

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(31)

RUFEWA.

Tun da Turaki ya fita na tashi na shiga Wakin sh twins na tarar har sunyi bacci, na gyara musu kwanciyarsu na lulluSe su, na koma Waki na kwanta, daman ban saka ran dawowar sa ba sai da safe. Washe gari ma Turaki bai shigo ba har su twins suka tafi makaranta, sai wajen tara ya shigo bayan mun gaisa na nuna masa email din da aka yi min jiya, bayan ya gama karantawa sannan ya ce.

Habibty wannan babbar dama ce a gareki, aikin NGO s da Chaina kinsan wannan ba ™aramin aiki ba ne, kuma za a sami ci gaba da sau™in abubuwa da yawa a ™asar nan, masu fama da waWan nan cuttukan zasu sami sau™i da rangwami, in dai har wannan aikin ba zai kawo miki cikas a aikin da kuma shagonki ba to ina bayanki, amma ki yi shawara da yan gidanku.

Yan gidan mu kuma? Akwai wanda zanyi shawara da shi da ya wuce kai ne?

Nufina ki sanar da su suma, ni dai ina goyan bayan yin wannan aikin Habibty sosai da sosai.
Chapter 30 · 0% Book details