← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 32

Sashe 20

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk ranar da kuka sake kuka ™arabin Turaki wallahi sai na zane ku, dan ubanku baku da wata ala™a da shi, ba ubanka ba ne shi.

Kin haWa kanki da aiki, dan ba abinda zasu gane.

Hajiya ta faWa, ni mi™e na ce.

Yau da gobe zasu gane, in sha Allah gobe zan sanya su a makaranta, nima litinin zan komai aiki.

Ai idan kika ga kina yi min yawo a gidan nan to wallahi mijinki ya sake ki, amma bazaiyu kizo kina min yawo a gida ba da aure akanki.

Ni Hajiya idan ya™i sakina, kawai zan shigar da shi ™ara.

Wace irin ™ara kuma?

Kotu mana Hajiya, al™ali zai iya raba auren.

Amma kuwa da anyi shari ar da ba a taSa sokuwa shari a irin ta ba, da mutane sun yi miki kallom jahila, sabida babu wacca ta taSa zuwa kotu raba aure akan anyi mata kishiya sai akanki, Nana karki yi abinda duniya zata zage ki mana.

Hajiya wai kinsan yanzu zuwan mu amaryar ta shi zata yi min rashin kunya, aikuwa na Wauke ta da lafiyayyen mari, wai na rabu da mijinta.

Mijinta mana, tun da a yanzu ta fiki iko akan shi, dan ita gida Waya suke zaune.

Na yi tsaki, na tuna kalaman ™arya da yaudara irin na Turaki, wai ni kaWai yake so, kai namiji mugun hallita, namiji mugun irin.

Ni dai Hajiya zan koma aikina, kuma zan shigar da ™ara kotu a raba mana auren, dan ni bazan iya zama da shi da wata matar ba, kuma tana haihuwa ni bana haihuwa, kema kinsan wannan zaman ai ba adalci a ciki, ni aure ma na yi wanda zan iya, Allah Ya bani lada.

Ki dai dage da addu a, haihuwar nan fa ba cewa aka yi bazaki yi ta ba, zaki haihu kawai ta yi jinkiri ne, amma duk kin sakawa ranki bazaki haihu ba, itama fa matar da ya aura babu tabbacin zata haihu anan kusa, kaWan daga hukuncin ubangiji dan shi ba ayi masa dole kuma kin sani.

Na yi shiru, ina tuna son zuciya da zalunci irin na Wa namiji, ko kuma na ce irin na Wan Adam, dan ba iya maza ke da son zuciya ba, ko da ace ina haihuwa Turaki yazo zai ™ara aure ba zanji daWi ba, amma kuma me ya sa a lokacin Sardauna banji komai ba? Ko da yake banso Sardauna ba a baya, kamar yanda na so Turaki, amma ya yi min wannan mummunar sakayyar, hhhm Wan Adam.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(19).

Bayan kwana uku da zuwa gidan Turaki na kwaso kayana, amma ba Turaki babu takardar saki, twins ma ranar da na Wauke sun zan kai su makaranta wata school Bus tazo Waukansu, wai Babansu ya sa su a makaranta, har makaranta naje muka yi magana da shugaban makarantar na ce a faWim kuWin zan basu sai su mayar masa amma suka ce su ba haka ba, ta dole na ™yalesu na dawo na ci gaba da zaman jiran takardar sakina amma shiru har kwana uku, dagaske dai Turaki dai dagske yake bazai sake ni ba kenan, Hajiya kuma ta dage wai babu inda zanje da aure a kaina, amma duk da haka na yi niyar gobe littinin duk abinda zai faru sai dau ya faru amma sai na fita wajen aiki, idan ma ba haka ba ni kawai zance kotu na shigar da ™ara, ina cikin wannan tunanin na ji wayata tana ™ara, na kai hannu na Wauka naga lamba ba suna, na Waga nasa handsfree aka fara magana.

Dan Allah dan Annabi idan ba kya son Turaki wallahi ni ina son sa, dan Allah ki rabu da mijina ya yi rayuwa cikin farin ciki.

Wani abu ya tsayamin a rai, Na rabu da shi? Ri™e shi na yi ko me?. Na ja tsaki na kashe wayar tare da dannawa lambar block, nu na fara gajiya da wannan yarinyar gaba Waya, wani mugun haushinta nake ji, musaaman idanta faWi kalma mijina idan ta faWa sai na ji duk duniyar ta yi min zafi, ni Turaki zai rainawa hankali kenan? Yana can yana rayuwa da yarinya shine zai zo yana yi min wannan shirmen, maza mayaudara ne ko mahaukaciya aka aura masa biyan bu™atarsa zai yi da ita indai zata ba shi abinda yake so, shine zai raina min hankali, ko da yake yarinyar ma ni banga marabarta da mahaukaciya ba, a take na tuna lokacin da Turaki ya ce zai yi duk wani abu da zai sani farin ciki, nasan so yake ya ji na ce ya sake ta sabida bani da hankali ko me? Ai dukkan yarda ta ™are a tsakanina da Turaki tun ya gwada auren wannan to babu shakka nan gaba kaWan ma zai sake auren wata, ba ma abinda zai kaini na ce ya sake ta ya yi ya zama da ita, idan ya ga dama ma ya jere mata hudu, bayan shekara Waya ya cire su ya sake zuba wasu huWun shi ya ga dama, ni dai nagama yarda da karatun maza.

Kwantawa na yi na fara hasaso rayuwata, tun daga lokacin da na fara haWuwa da Sardauna, Sacewa ganina da ya yi, da irin wahalal da na sha, sannan zuwa sa na biyu bayan mun dawo daga makaranta, da kuma haWuwar mu da shi da Hajiya ta aike ni, irin soyayyar da ya nuna min har ta kai ga na aure shi, irin Soyayyiyar azabtarwa da ya yi min, wauta da na nuna a rayuwar auren har da zuwa gidansu Bilkisu, sai kuma na yi shiru a fili na ce.

Yanzu duk suna ina? Bilkisu ta girbi abinda ta shuka, Islaha ma ta girba, shima Sardaunan yana kan girba.

Sai kuma hawaye ya fara zuba a fuskata, cikin kuka na fara cewa.

Na Wauka da ™uncin da na shiga a gidan Sardauna na gama, na yi tunanin aure na da Turaki buWewar dauwamammen farin ciki ne a rayuwata, amma ashe ba haka ba ne? Ni dai bana son rayuwata ta ™ara shan wahala, ina son hutu, ina son sau™i a rayuwa, ina son na ji daWi ko ya ne, Allah na tuba.

Na kifa kaina da katakon gado na ci gaba da raira kuka na, ina yi ina sharSar hawaye ina ta tuna abubuwa marasa daWi da yawa a rayuwata, ™alubale da na sha tun haihuwata nake shan wahala wajen Hajja kakata, na girma na zo na faWa tarkon Sardauna, haka na yi ta kuka na babu mai ce min Nana daina, har bacci ya Wauke ni.

Washe gari da safe na tashi na yi aikina na gida, bayan na shirya su twins sun tafi makaranta, nima na hau nawa shirin tafiya ofis Win, Hajiya na kallona bata ce min komai ba har nagama shirina, na zo yi mata sallama.

Nana, wai kina ganin hakan ya dace? A addinan ce fa hakan bai kamata ba, idan da aurensa akanki bai kamata ki fita ko ina ba, ba tare da kin nemi izini wajensa ba.

Nasani Hajiya, amma zanje kotu ne na shigar da ™ara.

Nana bazaki ji shawara ba ko?

Hajiya ki yi ha™uri dan Allah.

Na faWa tare da ficewa, sai da na fara zuwa kotu na nemi lawyer ma shigar da ™ara ta akan ina so mijina ya sake ni, akan dalilin na daina son sa kuma bazan iya zama da shi ba, daga nan na wuce wajen aiki. Nan ma ban wani jima ba na tashi na dawo gida, sai dai ko da aka kai takardar sammaci wai Turaki baya ™asar ma baki Waya, na shiga tashin hankali sosai, me Turaki yake nufi? So yake ya barni na yi ta gantali da aurensa a kaina ko me? Haka na yi ta zaman Sacin rai, sabida kar nasami matsala da wajen aikin yasa Hajiya ta barni na ci gaba da zuwa, ana wannan yanayin na yi wata biyu cif a zaune a gida da auren Turaki akaina, ina zaune ni ba mai aure ba, ni ba marar aure ba. Sai da aka yi wata uku sannam aka nemeni a kotu akan wanda na shigar da ™arar sa ya dawo gari kotu tana nemana, domin yin zaman farko. Ba kunya ranar da za ayi zaman farko na shirya tsaf, ban nemi kowa a gidanmu ba na shirya na tafi kotu, kafin ™arasowar al™ali ina zuane daga gefe Turaki yana zaune a gefe sai kallona yake, ni kuwa na Wauke kaina, kamar ma bansa an hallice shi a wajen ba, sai dai abinda yake ta yi min yawo a zuciya shine yana can amaryar tasa ta sami ciki, idan kuma na tuna da ciki sai na ji na sake tsanar shi, sabida muguwar ™arya irin tasa. Mu da muka zo kotu za a yi shari ah ™arfe goma ba a fara ba sai ™arfe sha Waya da rabi, ina shiga Wakin shari ar na ji gabana yana wani faWuwa, na ji gaba Waya jikina ya yi evening. wai yau ni ce zan tsaya gaban al™ali ina shari ah da Turaki? Duk abinda Turaki ya yi min bai kai na Sardauna ba, amma ban iya tsayawa da Sardauna ba sai Turaki, anya babu son zuciya nima a lamarina, anya kuwa akwai hallaci? Anya na yi tunani na mai kyau, na yi shawara da inda ya kamata, a take hawaye suka fara zubo min a fuska, bazan iya ba wallahi, bazan iya tsayawa da Turaki na yi shari a da shi ba, na fasa. A hankali na fara zame jikina ina yin baya, na dawo na sami wani benci na zauna na kifa kaina da gwiwa na fara rusa kuka mai taSa, zuciya kawai ni Turaki ya sake ni, amma babu zuwa gaban al™ali, Turaki har yanzu Wawainiya yake da iyayena da ya yana da yan uwana, duk da nagama auren sa bai kamata na tsaya gaban al™ali da shi ba, bai kamata na yi irin wannan rabuwar da shi ba, muryar barrister na naji yana cewa.

Ranki ya daWe.

Na Waga rinannu idanuna na kalleshi, ya ce.

Mai shari a yana nemanki.

Na girgiza ma sa kai, ya matso kusa da ni ya ce.

Mene bangane ba, ya yi miki barazana ne?

Na ce.
Chapter 20 · 0% Book details