← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 32

Sashe 32

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yanzu nasan gaskiyyar cewar ni ba Wan wannan gida ba ne, ban da ala™a ta kusa ko ta nesa daku, dukkanin abinda kuka yi min na gode, Allah Yasaka muku da alheri, kuma ina neman yafiyarku bisa ga haka. Duk wani abu naku da yake wajena na haWe su na ajiye, zan tafi na je na yi rayuwa babu kowa babu komai, domin ita ce rayuwar da takamace ni, ba iya ha™™in Nana bane akaina, akwai manya ha™™i da yawa a kaina, na raba zumunci, na ™ulla shari kala kala, duk a bisa huWubar wannan mutumin da yake kwance, ya kaini waje da yawa na shaida zir akan abina ban gani ba, kuma bansani ba, ta ina rayuwa zata bar mu? Ina neman afuwarku dan Allah, wannan shine ganinku da ni na ™arshe a rayuwa ku yafe ni.

Gaba Waya jikin kowa ya yi sanyi, hawaye suka wanke fuskokin mutane, Mama ta ce. 

Sardauna ba ni na haife ka ba, amma ni ce na raine ka wajena ka girima ka taso, ko baka da ala™a da wannan ahalin ni kana da ala™a da ni, sabida nono na ka sha, dan haka ba zaka je ko ina ba kana tare da ni, tabbas ka aikata abubuwa da yawa amma rayuwa ta gaya ma gaskiyya kuma ka yi tuba irin tuban da Allah Yake so, dan Allah Sardauna ka zauna tare da ni.

Ya girgiza kai, ya ce.

Mama, kin soni, son da ko uwar da ta haife ni shi za ta yi min, kinyi ™o™ari akaina baki taSa nuna min ™yama ba ko wani abu, amma na kasa miki sakayya mai kyau, bazan iya ci gaba da zama dake ba ina kallonki ina tuna mugayen abubuwan da na yi miki, tabbas a yanzu lokaci ne da zan girbi abinda na shuka.

Ba yanda ba ayi da Sardauna ba amma ya ce shi tafiya zai yi, ta dole aka ™yale shi ya tafi. Haka muka koma gida gaba Waya jikinmu ya yi sanyi ™alau, washe gari da safe kuma aka tashi da labarin mutuwar Big Daddy, zuciyarsa ta buga. 

Bayan sati guda da mutuwar Big Daddy aka fara raba dukkanin wani abu na family da yake wajenshi, komai aka raba shi sai babban kamfinsu guda Waya shine aka bari aka ci gaba da juya shi, raywa kenan duk abinda ya daWe yana ™ullawa ya ™are, duniyar kuma ya tafi ya barta. 

Bayan Shekara biyar. 

Rayuwa ta sauya abubuwa da yawa sun faru, a cikin shekara biyar Allah Ya azurce ni da haihuwar yara maza guda biyu, mai sunan Alhaji ne farko wanda muke kiran shi Abhi, sai bayan shekara uku na haifi wani namijin da aka sanya sanya masa sunan mahaifin Turaki, wanda a yanzu yake da shekara biyu, Abhi kuma shekarar biyar, sai su Twins shekara takwas takwas. Aimam sai da ya yi shekara bakwai yana jinya sannan Allah Ya Wauki ransa, mutuwar Aiman ta yi matu™ar taSa Laila, wanda ta dinga abubuwa tana surutai har da cewa ni na kashe mata shi har sai da Turaki ya sake sakinta, wanda da ™yar na sa shi ya yi dawo da ita, ya nuna mata cewar alfarmata ke ri™e da ita a gidan, wanda a lokacin ta yarda da hakan, ta yarda alfarmata ke ri™e da ita tun da ita a yanzu babu Wa ba wani abu, ta dole ta fara biyayya a gareni, ni kuma na yarda a a raina Turaki jarumi ne a cikin jarumai, na yarda da shi fiye da zato, na yarda da shi da dukkan rayuwata. A zuwa wannan lokacin Gidauniyar mu ta kafu ta yi ™arfi sosai da sosai, akaf arewacin nigeria babu inda ba a san da Mr s Abubakar Turaki ba, shine sunan da nake amfani da shi a ko ina, har da kafafen sada zumunta da nake da tarihin mabiya, na mai da Hajiya aikin Hajji da kuWi na kaina, na kuma kai Yaya Radiya da Yaya Rumaisa Umara hara sau biyu, Ra is da Yaya Ridwan kam duk da kansu sukaje kuma suka kai Hajiya da sauran yan gidan. Haka kasuwancina na buWe manyan shagona a garuruwa daban daban, ciki har da kano da Abuja, kudaWe nake samu ta hanyar kasuwancin gashi har empowerment matar gwamna ta Wora ni akai na nawa mata jari, bisa irin ™o™ari da gidauniyarmu take yi.

Sardauna tun ranar da ya bar gidan Big Daddy ban sake sa shi a idona ba, na manta shi amma ba gaba Waya ba, ya zama wani tabo a rayuwata da bazai taSa goguwa ba. 

Bilkisu shekararta ukun a gidan yari aka fito da ita, bisa shiga da fita da iyayenta suka yi, sai dai ba ta yi doguwar rayuwa ba, cutar da ta shiga da ita da iya ta fito kuma ita ta yi ajalinta. 

Tsakanina da yan uwan Turaki sai son barka, ko ina ana sona ana kuma girmamani, Turaki ya zama bango a cikin familynsu yana gudanar da koamai cike da adalci.

Gidanmu kam sai godiyar Allah, kowa ya zama wani, Allah Ya amsa addu ar Alhaji duk ya Waukaka mu, ya yi mana arzi™in da muke taimakon al umma, duk gidajen dake jikin namu mun siye su mun ginawa Hajiya babban gida, yan uwan Alhaji duk sun zo suna borin kunya kamar yanda kowanne dangi  suke yi idan suka ga Allah Ya Waukaka waWan da suks watsar.

Tsakanina da al umma kam na zama wata madubi da mata da yawa suke kallo suke koyi da ita, na tara Wimbin masoya masu tarin yawa. 

A cikin gidana kuwa na zama zinariya gimbiyar dake hask zuciyar Turaki, ni ce mai faWa aji ni ce mai kula da shi da komai, wanda a ™arshe dai sai da Laila ta nemi cikon saki Wayan ta tafi, ta barni da mijina da ya yana guda huWu. 

Yau tun safe muke kicin ni da su Twins, kasancewar yau Turaki zai dawo daga tafiyar da ya yi, aiki muke ba kama ™afar yaro mu Waura wancan mu sauke wancan.

Maamah, wai ba zaayi masa avocado Win ba jiya fa da muka yi waya da shi ya ce yana so.

Wani kallo na watsa mata sannan na ce.

Sauwama ki yi masa, tun safe muna aiki har yanzu bamu gama ba amma kina ™ara Wauko mana wani daban.

Haba Maamah dan Allah.

Sai kuma ki yi.

Yaya Twins Yaya Twins.

Abhi ya shigo yana magana.

Mene?

Sauwama ta faWa tana tura baki sabida na ce ba za ayi Avacado ba, daman Sauwama ita ce mai zuciyar masifa. 

Ni bake ba.

Ya faWa.

To fita daga nan.

Ba shiri ya fita dan yasan yanzu zata lugudeshi a banza, haka muka yi ta faman aiki sai wajen karfe shida muka kammala sannam muka jera komai a dinning, kowa ya shiga ya je ya shirya. ˜arfe shid da mimti goma driver ya shigo daga Wauko Turaki, na fito cikin shirina zan tare shi amma naga su twins ma sun ragani, na watsa musu harara na ce.

Ku shige ciki ku bar min miji.

Sauwama ta yi saurin cewa.

Maamah ki shige ciki, ki bar mana Papanmu.

Wani kallo na watsa mata sannan na ce.

Kuna hauka amma, wannan ai babu mai rabani da shi.

Sai a lokacin ya ce.

Har mutuwa kuwa Habibty na, ina sonki har abada.

Mu baka son mu ko?

Abhi ya faWa, Turaki ya ce.

Ya zaayi na ™i Abhi na, kawai dai ita son nata na mussamman ne.

To Allah Ya ™ara soyayya, ya barmu tare har abada.

Na yi saurin cewa Amin, ba tare da na tantance wacce ta yi maganar ba cikinsu twins.

Wani irin daWi na ji a raina, na tabbatar a yanzu duniya ta gama ba ni duk wani abu da nake bu™ata, sai nake jin kamar babu wata mace dake da matsayina. 

Ya Allah ka tabbatarmin da Turaki a matsayin mijina har Aljannah.

Amin Habibty.

"A cikin wannan rayuwar da na ratsa, na koyi abu guda Waya, kuma na koyar da abu guda Waya.

Me na koya?

Na koyi cewa dukkan abin da ka shuka, shi zaka girbe. Alkairi ba ya faWuwa ™asa banza, haka shi ma mugunta ba ta haifar Wa mai ido.

Me kuma na koyar?

Na koyar da cewa, komai tsananin duhu, zafi, da matsin rayuwa, muddin ka mi™a al'amarinka ga Ubangiji, to tabbas komai zai wuce ya zama tarihi. Babu daren da ba zai waye ba.

Alhamdulillah.

Nan na kawo ™arshen labarin littafin SARTSE. Godiya ta tabbata ga Allah MaWaukakin Sarki, Mai kowa Mai komai, wanda IkonSa ne ya nuna mini wannan rana. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammad (SAW), tare da iyalansa da sahabbansa baki Waya.

Na fara posting Win wannan littafi a ranar 8 ga watan Mayu, 2026, kuma cikin ikon Allah na kammala shi a yau 28 ga watan Yuni, 2026.

Alhamdulillah! Bayan duk wani faWi-tashi, daWi da ™una, gashi tafiyar SARTSE ta zo muku cike da ya™ini da fatan alheri. Cikin nuna tsantsan farin ciki, ina mai tabbatar muku da cewa fatana bai yanke ba, kuma kyakkyawan tsammanin da na yi muku bai tashi a banza ba. Na gode sosai, na gode da yadda kuka karSi wahalar da na Wauki tsawon lokaci ina sassa™a ta domin ku. Allah Ya saka muku da alheri, Ubangiji Ya haWa mu a Aljanar Firdausi baki Waya, Amin.

Bayan haka, kalmomin baki na ba za su taSa iya bayyana irin soyayya da girmamawa da nake muku ba, masoyana na dandalin ArewaBooks da kuma WhatsApp.

Kullum idan na tashi rubutu, kalaman ku na ™arfafa gwiwa, likes Winku, da reviews Winku  sune suke zame mini fitilar da ke haske mini duhun daren tunani. Ba ku san darajar tattaunawar da muke yi a WhatsApp ba; kowane comment, kowace dariya, da kowane sharhi da kuke yi a kan sassan littafin nan, jini ne da ke gudu a jikina wanda yake ba ni ™arfin ci gaba da rubutu ko da na gaji.

SARTSE ba zai taSa zama abin da yake ba a yau idan babu ku. Kun zama kwarin gwiwata, kun zama babban jigo na nasarata. Ganin yadda kuke bibiyata, kuna jirana, kuna nuna damuwarku a kan kowace haruffa da na rubuta, means a lot to me yana da matukar daraja a zuciyata.

Ina muku alkawarin cewa muddin akwai rai da lafiya, Sayyid Legendspen ba zai fasa kawo muku labarai masu taSa zuciya ba. Na gode da kuka kasance tare da ni tun daga farko har zuwa ™arshe.

Sai mun haWu a littafi na gaba! Mu huta lafiya.

Legendspen

08129553971
Chapter 32 · 0% Book details