← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 32

Sashe 25

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai na faWa miki matata bata da matsala, duk waata matsala daga wajenki ne, kuma gashi an fara samu, sannan na faWa miki wannan shine abinda bazan iya Wauka ba wallahi.

Ni dai banza na yi dasu, suka gama abinda zasu faWa bance musu komai ba, ™arshe yazo yana banu ha™uri, tun daga wanann ranar bansake sata a idona ba, kuma nima ban nemeta ba. Sai da Turaki ya yi sati guda wajenta, sannan ya fara raba mana kwana, na cire raina na Wauke ta a lissafina kwata kwata, har mantawa nake tana gidan sabida gaba Waya bana bi ta kanta, lokacin da Turaki yake gunta shima mantawa nake da shi sai lokacin da ya dawo wajena, kwata kwata ban sami wani sauye daga wajensa ba na kulawar da yake ba ni, mussaman da na Wauke idona daga kanta, sai hakan ya zama wata kafar shan iska agareni, na ri™e yara na hannu biyu ina kula da su, na kuma dage da addu a na daina kwanciya irin da kamar kasa, idan na kwanta sai safiya. Na mai da hankali na dage matu™a da ibada da ro™on ubangiji.

Yau tun safe Lamrah ta kira ni zata zo, kasancewar yau weekend ne ina gida twins kuma suna tahafiz, ba wani aiki na yi nazo azo a gani ba, amma na gyara gidan sosai. Sannan na shirya yin wainar fulawa, na haWa komai na ajiye ina jira tazo mu yi tare, sabida wainar fulawa tafi daWi ana soyawa ana ci. Sai dai zuwanta ita da Ra is ya tsayar min da duk wani zumuWi da nake yi, Ra is wai ya manta yana da aure ne? Kuma ni har cikin zuciyata ma bana son mu amala sa da Lamrah, bawai dan tana da wani mugun hali ba ko wani abu, kawai mahaifinta ba mutum arzi™i ba ne.

Kin wani tsare mu da idona, ki bamu hanya mu shigo.

Ra is ya faWa, sim sim na matsa musu hanya suka shigo cikin falon.

Baby wai baki faWa mata tare zamu zo ba?

Lamrah ta gyaWa masa kai, ni kam da naga bazan iya shiru ba na ce.

Baby aina? Ra is baka taSa kawo min matarka gidana ba, amma ka iya biyo Lamrah ku tawo, har kana wani kiranta da Baby, to kasani zaren ba kalal yadin ba ne.

To matata zuwanta nawa? Ni zan kawo ta da kaina? Kuma ma ko mene ai na kawo amaryata ba shikenan ba.

Kai ka sani marar kunya.

Anty Nana ina wuni?

Eyh dole ki ce anty bayan kusan abinda kuke ™ullawa, ke kina tunanin Big Daddy zai barki ki aure Ra is ne? Ni kaina yana ke fama da shi bare kuma Ra is? Kar ku fara Waurawa ranku abinda bazai yu ba, shawara.

Mu dai munji mun gani ko?

Ra is ya faWa.

Ai sai ku yi, ke kuma ki tashi ki shiga ki soya mana wainar, dan banza iya ba.

Dariya ta yi sannan ta tashi ta nufi kicin Win, Ra is ya mi™e zai bita na ce.

Kai Namamajo.

Dariya ya yi ya zauna, ni kuma na tashi na shiga kicin Win, sai da na haWa mata komai ta fara soyawa, sannan na fito falon. Kasancewar nasan kicin Win yana Wan ciki ciki yasa na ce da Ra is.

Kai baka da hankali wai? Kasan sharrin baban yarinyar nan? To duk wata matsala da nake fama da ita gidan nan shi ya ™ullata, baya son talaka ko kaWan, bazai taSa baka yar sa ba ™arshe ya ci maka mutunci, muma ya ci namu.

Wallahi Yaya ni ba sonta nake ba, kawai naga abinda take yi min ne, baki ga yanda take sona ba wallahi, tun bana kula ta har na fara jin tausayinta, shi ya sa na fara biye mata, amma nasanar da ita magana Waya daga wajen mahaifinta da ita za ayi amfani, yana cewa a a na ha™ura, yanzu ma baki ga magiyar da ta yi min ba na kawo ta nan.

Legenspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(25)

Allah Sarki, Ai mutuniyar kirki ce wallahi, haka ma Mama Amina akwai son jama a, da ace babu matsalal Big Daddy ni kaina zan so maka ita, amma tabbas amincewar Big Daddy aiki ne ja.

To Yaya Nana a dage a sanya mu a addu a, ina twins?

Suna Tahafiz, nan ba da jimawa ba zaka gansu.

Na faWa tare da tashi na koma kicin Win, a lokacin da na koma na tarar da ita har ta yi wainar sosai ma, bayan na duba na gani na ce.

Ai wannan ma ta isa ko?

Eyh nima haka na gani, sai dai ko za a yiwa Yaya Turaki da su twins.

Turaki yau acan yake, sai dai su twins suma sai Waya da rabi zasu dawo, idan sun dawo a soya musu ko?

To shikenan.

Ta faWa tare da kashe gas Win muka fito falon mu ka fara ci, muna ci muna hira Turaki ya shigo na yi mamakin ganin shi a gida, dan ni tun safe bai shigo min nan ba, na yi tunanin ba ya nan ma.

Ah kana nan ashe? Barka da safiya.

Ra is ya faWa yana mi™awa Turaki hannu, murmushi ya yi masa sannan ya ce.

Ina nan, ai yayar taka ta watsar da ni yanzu, idan banzo ba fa bazata neme ni ba.

Lamrah ce ta ce.

Yaya ina kwana?

Lafiya ™alau Lamrah, yau duk kune a gidan?

Eyh wallahi, ya amarya?

Ai baki shiga kin ganta ba, ta ina zaki tambaye ni?

Zan shiga ai.

Cikin Waki ya shiga ba tare da ya amsa mata ba, nima na mi™e na bashi, ina shiga ya ce.

Habibty kinsan me?.

Sai ka faWa.

Laila fa ciki ne da ita.

Ji na yi maganar ta shige wani girin gin, amma na dake na ce.

Kai ma sha Allah, abin nema ya samu, Allah Ubangiji ya raba lafiya, ya yi masa albarka.

Amin Habibty.

Ya amsa, farin cikin dana gani ya gaza Soyuwa a fuskarshi, sai yasa naji jikina ya yi sanyi. A raina na ce. Allah Sarki ni, Allah ka duba ni.

Habibty karki damu kinji, in sha Allah kema naki suna nan tafe, suna hanya in sha Allah.

Na yi wani iri murmushin da ni kaina bansa fasaarar shi ba, na ce.

Ai ni ko ban samu haihuwa ba Allah ya sallameni, ya bani twins kaima kuma ya bawa Laila.

Hakane Habibty, amma ina son na wajenki sosai, in Allah Ya yarda suna hanya.

Allah Ya yarda, bari naje wajensu ko?

Tom, nima bari na shirya anan na fita, yan uwanta ne suka zo.

To shikenan bari na haWa ma ruwan wanka.

Na faWa tare da shiga banWakin, ina shiga banWakin na fashe da kuka, da sauri na kunna famfo ruwa ya fara zuba, wani irin abu me zugi na fara ji a cikin ™irjina, mai matu™ar zafi da raWaWi wanda yafi wanda na ji ranar da Turaki ya ™ara aure, ina kuka ina haWa masa ruwan wankan, sai da na wanke fuskata sannan na fito.

Ka shiga.

Habibty jira ni dan Allah.

Tom.

Na faWa, shi kuma ya shiga cikin banWakin, ya yi wankan shi ya fito ina nan zuane, sai da ya gama shiryawa sannan ya ce.

Habibyu, nasan kinsan samu da rashi duk na Allah ne, haka kuma Allah maji ro™o ne, nasan yanda kika dage akan addu a, nima kuma na dage Habibty, duk wasu yan uwa da abokan arzi™i suka dage, Habibty Allah yana ji yana gani kuma zai amsa, sanar dake cikin Laila bawai nuna miki farin ciki na bane, ko son Sata miki rai. Na faWa miki ne Habibty sabida yana da kyau na sanar dake tun da wuri kafin ki gani da idonki, dan Allah ki yi ha™uri ki kuma ci gaba da kai kukan ki ga ubangiji dan Allah, wallahi wannan cikin na Laila ba zai canja mata wani matsayi ba ko ya taSa naki, Habibty wallahi har yau har gobe Laila tana cin albarkacin ki ne, tana zamane sabida kina zaune, a yau kikace ta tafi wallahi cikin dake jikinta bazai ruWe ni ba, dan Allah karki sanya wannan damuwar a ranki kinji, bana so wani abu yazo ya dameki.

Haba Habiby, idan banyi farin ciki da samun cikin nan ba me zanyi? Abinda kake so ne fa, kuma kake yi min kara a kai, ni dai dan Allah dan Annabi kar samuwar wannan cikin yasa ka sauya min dan Allah, zuciyata tana sonka tana kuma ™aunarka, dan Allah karka guje ni ko juya min baya.

In sha Allah Habibty.

Ya faWa tare da tashi, ya ri™e hannuna muka fito tare, su Ra is suna zaune a falo muka wuce su, sai da na raka shi har ya shiga mota, ya daWe yana faWamin kalamai masu sanyaya zuciya a cikin motar, sai da ya ga nagamsu sannan ya tada motarshi ya fita, ni kuma na juyo na yi cikin gida. Ina bakin ™ofar shiga part Win na ji an ri™o min bayan rigata, na tsaya ba tare da na waigo ba na fara ™o™arin ™wace rigata.

Juya ce fa.

Na ji an faWa, na yi murmushi ba tare da na jiyo ba.

Laila karki kuskura ki ce zaki ta da hankalinki, dan kinga mijinki yana rawar ™afa akanta, kinsan dai juya ce ba haihuwa zata yi ba, ke kuwa da zarar Allah ya sauki wannan cikin naki lafiya to da kanta, zata bar gidan.

Malama cika ni.

Na faWa tare da waigowa, sai a lokacin ma naga ashe wasu yan mata ne guda uku, sai kuma ita Lailan.

An™i a cika Win.

Cika ni na ce.

Ba za a cika ba fa.

Na yi murmushi na kalli Laila na ce.

Idan ba ta cika ba ke ta jawo wa, wannan cikin da kika gani bai isa ya canja ni daga matsayin da nake ba, kinsan da cewa zamana kike a gidan nan, a yau na ce sai kin bar gidan nan sai kin barshi.

˜arya kike juya, kalle ni da kyau, ciki ne a jikina, haihuwa zanyi, bawai zama nake na ci na kasayar ba, dan haka Turaki sai ya zama nawa.
Chapter 25 · 0% Book details