← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 32

Sashe 17

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waye ya shigo? Waye.

Amma ta ji shiru, muryar Maman Amir na ji tana cewa.

Anya kuwa Hajiya wani ya shigo, da an shigo ai nan za ayu.

Hajiya ta ce.

Wallahi kamar sautin tafiya na ji.

Gaskiyya ba kowa, amma bari a duba.

Ina jinta ta gama le™e le™en ta tsakar gida, taje ta tura ™ofar waje ta dawo, ni kam kuka na ke yi ™asa ™asa, idona yanayin min zafi ma rashin bacci ga kuma uwar gajiya, ga gajiyar zama a jirgi, ga rabin kwana a tsaye, ga kuma uwar tafiya da na yi a ™asa. Ba jimawa wani wahalallen bacci marar daWi ya Waukeni, wanda banyi shi cikin daWin rai ba, ina cikin baccin na ji ana cewa.

Maamah! Maamah.

Na buWe idona naga twins ne, na maka musu uwar harara na ce.

Ku fita ku tafi wajen Hajiya.

Ba musu suka sauka suka yi wajen Hajiya suna kuka, a loakacin na ji muryar Yaya Rumaisa tana cewa.

Daman suna nan?

Eyh nan muka yo da su, jarabar uwarsu wazai iya.

Aifa ana can ana tashin hankali, ni na rasa me ya sa Turaki yake tsoron Nana wallahi, idan suka jera sai ki gansu kamar ya da uba, amma idan kika ga yanda yake rawar jiki idan ta yi masa magana sai ya baki takaici.

Hajiya ta ce.

Aini bana ma iya kallon shiriritarsu, yanzu dai suna can suna fama, tun muna can yarinyar nan ta fuskanci wani abu ya faru, ta bi ta Waga hankalinta, kai kishi masifa ne.

Babba ba ™arama ba Hajiya, amma ita nata da iskanci.

Wani abu na ji ya tokaremin ma™oshi, wato duk sun san da zancen auren na shi, shine ko a jikinsu lallai mutanen nan, to wallahi dani suke zancen Turaki ne ko shine autan maza na ha™ura da shi, aure kam na yi abinda zan iya Allah Ya bada lada, amma tabbas na gama, na zauna na yi rayuwata na kula da tarbiyar twins, na sama musu farin ciki, shine kawai.

Ji na yi jikina yanayi min wani irin tsami, ba shiri na tashi ma fito zan shiga kicin na Waura ruwa, na ji salatin Hajiya, sai da ta gama rangaWa salati sannan ta ce.

Ke yaushe kika shigo gidan nan?

Na yi mata wani kallo, na ce.

Tun safe.

Me kike yi to anan? Ina gidan naki?

Ya sake ni.

Na faWa ima fara juyewa ruwan zafin da nasamu akam tukunya, cikin bawon wanka.

Innullahi wa inna illahir raji un, Rumaisa fito kiji wani mugun zanci.

Šaukan ruwa na yi, na nufi bakin famfon na kuna masa ruwa sanyi ya fara zuba, Yaya Rumaisa ta ce.

Nana kin cuci kanki, akam kishin banza kin rasa mijinki, miji mai sonki, nagartacce.

Na rasa Win, ke kije ki aure shi.

Na faWa ina ™o™arim shiga toilet.

Sai kinci gidanku, kuma ki yi duk abinda kika ga dama, in Allah Ya yarda bazan sake sa baki a lamarinki ba.

Kar ki sa Win.

Na faWa tare da shigewa ban Waki, a yanda nake jin zuciyata cikkn gidanmu Hajiya kawai banza iya tsyaawa mu yi musayar yawo ba, amma duk kansu a wuya nake da su, wai sun san Turaki zai yi aure, amma ko a jikinsu suna jin daWi anyi min kishiya, rashim haihuwata duk bai dame su ba. Haka na yi wa kaina ruwan zafi sosai, sannan na watsa ma fito, cikin jakar kayan Hajiya na duba doguwar riga na Wauka na sanya, na dawo na zauna, dole naje gidan Turaki na Wauko kayana, da waya ta da duk wani abu nawa, kuma babu wani a gidan nan da zan sanya dan duk basu da gaskiyya, ina cikin Wakin na ji zuwan Yaya Radiya, tana zama Hajiya ta ce da ita.

Kinji yarinyr nan ta kashe auren, wai ya sake ta.

Kai innullahi, yanzu tana ina?

Tana ciki, amma karki fara zuwa wajenta, yanzu zata zage ki kamar yanda ta yi min.

Yaya Rumaisa ta faWa, Yaya Radiya ta ce.

Zagi kuma?

Ga Hajiya nan ki tambayeta, har da ce min naje na auri Turakin, tsabar ta raina ni.

Lallai Nana, to ta ci kanta ita ta sani, babu wanda zai mata magana, ita ta yi asarar miji ba wani ba, har ta manta wahalal da tasha wajen Sardauna, tazo nan ta sami gata amma ina, shine akan ya ™ara aure take wannan abun.

Ni haushin Yaya Radiya ma nasake ji da ta gama wannan maganar, na mi™e tsaye na ce.

Ni Nana na gama shan wahala a rayuwa, zan tsaya na yi rayuwa cikin farin ciki ko da kuwa babu taimakon kowa a ciki.

Ina faWin haka na fito daga Wakin, na shiga Wakin da suke ciki, Yaya Radiya ta ce.

Sannunki Nana, kin kyauta kin kashe aurenki.

Hhhhmmm, yanzu ku abinda kuka yi kyautawa ne? Akan bana haihuwa shine kuka bada gudummawar ayi min kishiya? Bance baya ™o™arin zama dani ba, amma a zaman ba dole sa ya ji bazai iya ba sai ya sake ni, yafi min sau™i akan yaje ya yi min kishiya, rashin haihuwa ai na Allah ne, wallahi kun ban mamaki kuma kun ban kunya, ina matsayin ™anwarku jini Waya, amma akan abin duniya koka goyi bayan ayi min kishiya.

Ke Nana kama bakinki? Kina tunanin akwai wani abun duniya da zai sa yan uwanki su cutar da ke?

To Hajiya mene? Duk sun sa za ayi min kishiya sabida bana haihuwa, amma babu wanda ya sanar dani.

Wai waye ya ce miki akan rashin haihuwa aka yi miki kishiya? Da alama baki samu zama da mijinki ba, kawai kina ganin mace a gidan kika takura ya sake ki kenan?

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(16).

Nifa Hajiya ban ta kura shi ba, kawai mafita ta na duba, duk kun haWe min kai akan abun duniya, babu wacca zata fahimci halin da nake ciki a cikin ku? Da ace ina haihuwa dan Turaki ya ™ara aure babu abinda zai sanya ni na bar gidansa, amma babu haihuwa duk soyayyar da yake min wacce ya aura tana fara haihuwa shikenan, namiji ne fa.

Yaya Ridwan ne ya shigo gidan shi da matarsa, bayan mun gaisa ya ce.

Nana yana ganki.

Na yi shiru ban ce komai ba, Hajiya ta ce.

Ta ha™ura da auren.

Ya ce.

Kina ganin haka zai fi?

Na gyaWa kai alamar. Eyh. Ya ce.

Daman tun a farko na faWawa Hajiya cewar idan har kika ce bazaki zauna ba, to babu wanda zai takura miki, domin rayuwarki ce kuma yancin ki ne, amma kafin ki yanke kowanne hukunci ya kamata ki zauna ki yi tunani, wallahi muma bamu san da ™arin auren ba sai gab da tafiyarku, Hajiya mai sai a filin jirgi na sanar da ita, daga ni har Ra is bamu goyi bayan ki ci gaba da zama da Turaki ba idan ba kya so, duk abinda wani zai faWa miki ki tsaya akan abinda zuciyarki ta yarda dashi, wanda kinsan bai saSawa addini ba, Nana ana yin kishiya, ana zama da kishiya, amma ke taki tazo a wani irin yanayi na daban, duk da ba cewa aka yi bazaki taSa haihuwa ba, amma haihuwar ki ta yi jinkiri, kuma babu lallai babu dole a lamarin ubangiji, amma ki tuna da bambamci dake tsakanin aurenki na farko da na biyu, ki ha™a ki yi wa kanki al™alancin da kike ganin zai fi.

Ni dai Yaya na ha™ura da auren Turaki kawai, bazan iya jure ganin shi da wata matar ba, har ta haifa masa yara ni ina zaune, wallahi duk soyayyar da ta yan uwansa da nake gani yanzu duk sai ta bar kaina, shi kuma Big Daddy Allah Ya saka min, wallahi bazan yafe masa ba, tun farko ba sona yake ba, gwanda na ha™ura na bar musu familinus tun da daman ba can aka haife ni ba.

Na faWa ina goge ™wallar da ta taru a idona, Yaya Rumaisa ta ce.

Nana kina ganin haka zaifi?

Eyh Yaya zaifi, ni abun duniyar Turaki baya gabana, a yanzu ina da yanci ina da damar da zauna na ri™e kaina, na ri™e ya yana, bama iya Turaki tabbas aure na ha™ura da shi har abada, wanda na yi Allah Ya bada lada.

Amma me ya sa?

Yaya Rumaisa ta sake tambayata.

Akwai mutanen da kwata kwata basu da dace a soyayya, wasu a aure, wasu a rayuwa ma baki Waya, aurena na farko na ya kasance auren da na sha wahala mafi yawa a rayuwata, na biyu na sami farin ciki amma matsalal haihuwa ta™i barina na zauna, idan na sake wani a gaba ma matsalal rashin haihuwar ba bari na za ta yi ba, bazan sake yarda da wani daWin bakin namiji ba, har sai dai idan wanda ba ya haihuwa shima na samu, amma muddin namiji yana haihuwa babu abinda zai sanya ya zauna da macen da ba ta haihuwa, da me zanji? Ciwo da raWaWin rashin haihuwa? Ko kuma da zama da kishiya? Na ha™ura wallahi.

Na faWa ina kuka, tare da tashi na koma cikin Waki. Tun jiya sai yanzu na sami damar yin kuka, ai kuwa na saki baki na dinga yin shi da ™arfi har cikin zuciyata, sai da na yi ishashe sannan na samu bacci ya Wauke ni, wanda ban farka ba sai wajen ™arfe biyu. Ina tashi na sake Waura alwala na yi sallah na dawo Waki na sake kwanciya, su twins suna gefe suna wasa ni kuma ina kallonsu, wani irin so da ™aunar su yana taSa min zuciya, a raina na ce. Ko da babu aure akaina babu me raba ni da ya yana, zan baku kulawa, soyayya da gata. A daidai lokacin na ji sallamar Yaya Radiya, hannunta ri™e da plate Win abinci, na kauda kaina gefe ina jin Sacin rai, duk da Yaya Ridwan ya yi min bayanin komai amma kawai na ji haushinsu, sun nuna son abun duniya.

Nana.

Ta kira sunana, na waigo na kalle ta ban tanka mata ba, ta zuane gefen gadon tana kallona.

Ki tashi kici abincin?

Na ™oshi.

Bangane kin ™oshi ba, me kika ci?

Ina ruwanku idan ma naci wani abun? Ina ba kun zaSi dukiyar Turaki ba to mene a ciki?
Chapter 17 · 0% Book details