← Book details Sartse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 32

Sashe 16

Sartse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya sake faWa yana fita, ina tsaye na kasa gaba na kasa baya ya gama shiga da jakun kunan kayan nawa, sai da ya gama ya ce.

Ki shigo mana.

Habiby ina maka magana ka yi min banza.

Da yaushe? Me kika ce? Kuma anan zaki min maganar?

Hanyar part Win na ™arasa na fara ™o™arin buWewa.

Habibty mene haka kike yi ne wai? Ki nutsu mana.

Banza na yi da shi na fara murmurWa ™ofar, ina fatan Allah Yasa ba abinds sheWan ke ™o™arin raya min ba.

Wai me kike nema anan?

Hasken mene a wajen?

Hasken wuta mana, ko baki gani ba?

Nagani, shi ya sa nake tambayarka me ya sa aka kunna haske a wajen.

Shine na ce ki je na yi miki bayani.

Cika ™ofar na yi na nufi part Wina, ina shiga na zauna akan kujera na haWe rai ina jiran shi, yana shigowa ya zauna a kujerar da nake kai ya ce.

Habibty wai mene haka duk kika Waga hankalinki? Kinje kina ta buga can?

Habiby waye acan Win, ni jikina ya bani mutum ne a wajen.

Eyh Habibty mutum ce a wajen.

Na mi™e tsaye a tsorace.

Mutum? Wace?

Habibty dan Allah ki fahimce ni.

Wace kalal fahimta, wace irin fahimta kake so na yi maka?

Kina ji, wallahil azim na rasa ta yanda zan faWa miki tun kina nan, Habibty tun muna wancan gidan namu, Big Daddy ya Waura min aure.

Ji maganar na yi kamar an buga min guduma a akaina, wai an Waura masa aure, shine dalilin da yasa ya kaini aikin Hajji kenan, ni da mahaifiyata da ya yana? Ya kaini aikin hajji sabida na basu dama su ci amarci shi da matarsa? Shine zai siya ni da daWin baki, me ya sa duk maza suke haka ne? Wai ni Nana yaushe zan ji daWin rayuwa? Yaushe wahala zata yanke mini ne? Wan irin abu ne wanna Turaki ya yi min, ace ya tura ni aikin Hajji kawai ina dawo na tarar da shi da wata matar, to tukwicin aikin Hajji ne ™arin auren? Ko kuma tukwicin ™arin auren ne aikin Hajjin, ni bangane ba.

Habibty! Habibty!

Na ji muryarshi tana shiga kunnuwa na, sama sama.

Habibty dan Allah ki sauareni, ki ji me zance miki mana.

Na fara zubar da hawaye, ina jin wani Waci a raina, nama kasa magana sabida wani irin bugu da naji zuciyata na yi da wani irin ™arfi, wanda zai iya cutar da lafiyata, da sauri na sami waje na zauna, na haWa kai da gwiwa na fara janyo kuka, amma ina ya gagara zuwa, sai wani yaji yaji da nake a cikin idona, wani raWaWi da zafi, ga zazzafan bugu da zuciyata take yi.

Hannuna ya fara shafawa yana faWin.

Habibty, Nana, kina jina.

Kamar wacca aka tsikara na mi™e tsaye na ™wace hannuna, sai da na kalli Turaki na kusa mintuna goma, kawai na juya na kalli ™ofar fita, na yi waje a guje, ba shiri ya biyo ni yana faWin.

Habiby ki tsaya dan Allah, Habibty ina zaki?

Waje na nufa na fara ™o™arin buWe ™ofa zan fita, Turaki ya yi saurin kama hannuna.

Habibty ina zaki a daren nan?

Ka cika ni, ko ina nema wallahi gwanda naje, amma Turaki ba zan zauna a gidanka ba, bazan sake zama da kai ba, sabida kai macucine, kai mugu ne, ka zalunce ni, wallahi ban yafe maka ba.

Hasbunallahu wani imal wakil, Nana dan Allah ki fahimce ni, ki ji me zance miki dan girman Allah.

Me zaka ce? Raina min hankalin zaka ci gaba da yi? Ka ce min Big Daddy ne ya yi maka aure, ko me? Ka yaudareni ka yi min ™arya, a ko dayaushe ina tambayarka, amma sai ka ce zaka iya zama da a haka, ashe duk ™arya ce, duk yaudara ce? Tun farko kasan bana haihuwa amma kazo ka yi min daWin bakin cewa ka rayu da ni a haka, zaka aure ni a haka, amma kaje ka yi aure da wacca kake so, wacca kake tunanin zata haihu ta tara ma zuri a, to ni zan tafi zan ha™ura da rayuwa da kai, zan je na yi wata sabuwar rayuwa, ko da babu farin ciki a ciki.

Nana dan girman Allah ki yi min kyakyawar fahimta, ™arin aurena ba shi da nasaba ko wata ala™a da rashin haihuwrki wallahi, ga yarinyar nan ki shiga ki ganta, ta faWa miki gaskiyya.

Har abada bana fatan Allah Ya haWa idona da na ta, kai kanka Turaki wallahi bana son nasake ganim fuskarka, idan kana da ha™™i akaina Allah Ya saka maka, idan ni nake da shi akanka na yafe maka, amma ka rabu dani, ka rabu da rayuwata, aure idan katashi ka auri goma su haifa ma ya ya dubu.

Na faWa ina buWe ™ofar, ya yi sauri ya ri™e ni ya yi baya da ni, yasa key ya kulle ™ofar.

Nana ba kya ganin dare ne?

Ko menene tafiyata yafi min.

Dan Allah ki yi ha™uri, ki bani dama na yi miki bayani.

Bana son bayaninka, ka ri™e bazai amfane ni ba, ka rabu da ni dan Allah.

Na faWa ina jingina da jikin gate Win, ba yanda Turaki bai yi ba na shiga ciki amma na™i, na ce wallahi anan zan kwana asuba na yi na tafi gidanmu, sabida wani irin zafi da nake ji a cikin zuciyata, ko ganin Turaki bana son yi kwata kwata, babu abinda yake yawo a zuciyata sai zallan rashin mutunci da Turaki ya yi min, wai ya tura ni aikim Hajji sabida ya ci amarci, duk akan bana haihuwa, Allah Sarki ni, Allah ya kawo min mafita, amma tabbas nasha wahalal rayuwa, baya ga abubuwan da na fuskanta a rayuwata da Sardauna, yanzu ina fatan nasamu nustuwa da farin ciki, ina ganin kamar rayuwar wahala ta zata ™are, kamar labarin zai shuWe ashe yanzu ya fara, shikenan wahala da wahala ni Nana, cikin murya kuka na ce.

Allah na tuba Ya Allah, Allah karka maimaita min wahalal rayuwa da na shiga abaya Ya Allah, Allah na tuba Ya Ubangiji, Allah ka bani ™arfin da zan fuskanci wannan rayuwar.

Haka na yi ta faman kuka, babu yanda Turaki bai yi ba, amma na yi banza dashi ko waigowa ma banyi ba, kawai so nake garin Allah Ya waye na tafi gidanmu, na je na yi kuka na gode Allah, Burina kawai Turaki ya sake ni, na yi iddah nagama na shiga wata rayuwar, amma tabbas har abada har gaba da abada ma babu ni babu wani auren.

Legendspen

08129553971

SARTSE BOOK 3

Sayyid.

(15).

Da me zanji, Sardauna ya cuceni, wannan rashim haihuwar bazai barni na zauna a ko ina ba, daman ya faWa ya ce bazai taSa barina na aure wani ba, ga kalamansa sai tabbata suke, duk da yana halin jinya, amma Sardauna ya shuka mumunnan irin mai zafi a rayuwata, ya yi min SARTSE mai raWaWi cikin rayuwata, ya gana min azaba, ya cutar da ni, ina tsaye anan dare ya yi nisa, yanda nake tsaye haka Turaki yake tsaye yana kallona, ni kam nama juya masa baya, bayan wasu awowi ya matsu ya ce da ni.

Habibty dan Allah ki shiga ciki mu yi magana, ki tuna kin fa ce zaki yi min uziri akan komai, kar ki manta da kanki kika shaida irin son da nake miki, da kanki kika ce zaki rayu da ni duk tsanani da wuya, kin ce bazaki taSa barina ba, sabida kin tabbatar da irin ™aunar da nake miki, dan Allah ki sau™a™a zuciyarki, ku sanyaya ta karki yi min SARTSE a zuciyata. Habibty rashinki zazzafan SARTSE ne ga rayuwata dan Allah dan Annabi Habibty.

Maimakon sanyi, sai na ji wani zafi a maganganunsa, na maka masa wata uwar harara na juya baya, na sake rusa wani ihun ina faWin.

Wallahi Turaki ka rabu da ni, ka ™yaleni duk wasu maganganunka yaudara ne a ciki, ka ™yale ni dan Allah.

Babu ™arya, babu yaudara, babu algus a dukkan maganata Nana, wallahi sonki nake kinsani, kim yarda, dan Allah ki bani dama na faWa miki gaskiyya, na yi miki bayanin komai.

Mitchewwww.

Na ja wani dogon tsaki, a raina na ce. Dan ya mayar da ni sabuwar shashsha shine zai ce wai ya yi min bayani, da ya samu ya yi min kalamai shikenan zanji sanyi, su maza da sunga mace na son su shikenan sai su yi duk abinda suke so, sun san suna zuwa su yi mata daWin baki shikenan, da raunin mu suke amafani wajen zaluntrarmu.

Abu kamar wasa har aka fars kiraye kirayen sallah asuba, sai dai a yanzu na tsgunna daga jikin gate din, shima Turaki ya zauna daga gefe, har aka yi sallah muna nan, gari yanayin haske na fara bubbuga gate Win, Turaki ya fito bayan ya shiga yin sallah ya ce.

Habibty ki tsaya na sauke ki a da kain.

Turaki wallahi ba zan shiga motar ka ba, ka rabh da ni dan Allah, ka buWe min na tafi ko na haura ta sama wallahi.

To ka taki motar nan dan Allah ki hau.

Na bar maka kayarka, ai daman da kuWinka ka siya, to bana so.

Na faWa ina ™o™arin fara Wane gate Win na haura, ganin ina ™o™arin hawa gate Win ya sa Turaki ya ce.

Bari na buWe miki, amma dan Allah ki karSi wannan ki yi na mota.

Mitchewwww.

Na sake jan wani tsaki, sannan na matsa gefe ya buWe, yana buWewa na fita na fara tafiya, tin kafin naje bakin titi ma fara gajiya amma haka na daure na ci gaba da tafiya, ni da na fito kafin bakwai amma har tara ban ™arasa gida ba, duk na gaji na fita hayyacina, fuskata ta yi ja tana fitar da wani gumin wahala, ina tafe ina hutawa, har na ™araso cikin unguwarmu, nasa mayafina na rufe fuska ta yanda babu wanda zai ganni ya gane ni, a haka har na shiga gidanmu, wanda yake cike da mutane masu shigawar Hajiya, kasamcewar jiya saukar dare ce, ina shiga ko sallama banyi ba na faWa Wakim gadom Hajiya, inda naga twins a kwance suna bacci, faWawa na yi kan gadon daga gefe na fara kuka, ina jin Hajiya tana cewa.
Chapter 16 · 0% Book details