← Book details Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 71

Sashe 64

Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafin ahankali tawuce sama tana tafiya kafan kadan gaban dakinta na jiya ta tsaya tadade tsaye ahaka sannan tasa hannu tabude kofan, ahankali ta shiga, manya manyan jakunkuna tagani na shopping manya manyan ciki kayane ta hango ciki saikuma daya na su cream da kayan shafa daya kuma taga su chocholate da snacks daban daban. Irinsu biscuits, Pringles da komi, shiru tayi saikuma ta zauna kasa tareda ijiye jakanta tai shiru tana kallon komi kuka takeso tayi but ta hana kanta, magrib dataji ana kira yasa ta tashi tawuce bayi kayan jikinta tacire sun gaji sunyi datti sai kallon washing machine dake bayin tayi kafin kawai ta matsa ta ijiye kayan cikin lundry basket tadaura towel tafito ganin babu sabulu abayin tafito tana kallon jakan data hango sabulai tai shiru tana tunani idan yace suma saita biya fa, saikuma ta tuna yace zai sauke hakkinshi na mijinta kudin daya kashe kafin auren ta dana Mama kawai yakeso, dudda haka takara shiru kafin ta daure kawai tasa hannu tashiga ciro abinda ke ciki taga akwai body wash face wash dakuma set na su shampoo da conditioner da cowash da body scrub tawuce bayi. She wants to go back school gobe hakan yasa ta wanke kanta da shampoo da conditioner ta sannan tai wanka da ruwan zafi sosai bakaramin dadi taji ba tai brush sannan tai alwala tafito tasake dawowa ta tsaya tana kallon kayan wani farin rigan bacci data hango saman wani jaka tadauka takala spaghetti hand gareshi daurewa tayi tasaka tasa hijabi tai salla jin jikinta na mata kayau kayau yasa tasake dawowa wani cream ta shafa ta feffesa turare tacire na towel kanta ta maida bayi sabida gashinta yabushe tadawo jakan again dan duba ko akwai comb ganin babu yasa ta zauna saikuma ta kalli black bag nata da sauri tawuce tadauka tabude 200k na sadakinta tafara kwasa taja drawer gefen bed nata tasaka su ciki da 50k Buba sannan taciro lab coat dinta dataga duk yayi squeezing ga datti ta tafi bayi bataga omoba kawai ta kwara bath wash nata ta wanke dashi saikuma tafito tana tunanin yanda zata shanya kayan. Akwatin dazu da safe tabude taciro wani pink hijab tasaka sannan tasauka kasa rikeda lab coat din nata adan karamin bowl tabude kofa tafito ta tsaya gaban flat nata tana kallon yanda har an wanke wajen jinin naman, securities din na chan dakinsu dake wajen gate tana jiyo muryansu suna hira abinsu bataga wajen shanya ba daidai lokacin taga sun fito suna kokarin bude gate ana sako kan motan ciki ta ijiye bowl din ta takoma ciki da sauri tawuce sama ta maida kofanta tarufe tasaka key. Parking yayi dayake da kanshi yayi driving yakalli gaban dakin tareda yin murmushi intentionally yasa akabar kayan awajen cus yanaso tai engaging da activities na gidan ta tadan sake ta warware, yakalli bowl din lab coat din kafin ahankali yadauka ya zaga backyard da kanshi ya shanya mata yanaji yanda kayan ke kamshin shower bath that means bataga omo ba, dawowa yayi yabude falon ya shige ya maida kofan yayi locking yawuce kitchen, detergent ya dauka yasa a bowl din yahayo sama har gaban dakinta ya tsaya sannan yaduka ya ijiye bowl da omo yawuce ya kunna tv nan falon sama kafin yabude dakinshi ya shige. Salla tayi na isha i tanajin karan tv matsar da komi tayi tafito da komi na jakanta tayi babu some books nata Allah sa bai saida gidansu da yan littafan ta da credentials nata suke cikiba, shiru tayi saikuma ta jingina kanta gaban gado tai shiru tana tunani daban daban hawaye ne ya gangaro mata a idanu kafin bacci yayi nasaran kwashata awahale ahaka tana zaune daga ita sai yar rigan iya cinyanta ga gashinta a sauke. Mugun sanyin AC yasa tafara rawan sanyi ta tashi tahau gado dasauri taja bargo ta dukunkune wuraren 6 tabude idanunta da kyar ganin gari ya waye yasa ta tashi zaune da sauri tasauka daga gadon tafada bayi tayi brush da alwala tafito tasaka hijab tai salla tai karatun Al ani tunawa da laboact nata yasa ta mike tsaye da pink hijabin ta bude kofan tafito tanadan lekawa ganin bakowa yasa tai staircase tashiga sauka kasa hartai wajen kofa tana kokarin budewa kaman ance ta kallo wajen saitaga labcoat nata akan kujera an goge, dan jim tayi tana kallon lab coat din kafin tawuce tasa hannu tadauka tawuce takoma sama ta maida kofanta tarufe ta ijiye kan gado kawai saita shiga kaye kayan abubuwan cus tasaba aiki dasafe gashi akwai time before 9 duka kayan ta cicciro ta jera a wardrobe sannan tadauki wani atampa mai red embellish lace yayi kyau tasaka, dinkin riga da skirt, tadauki red veil ta ijiye sannan tafada wanka tayi wankan tafito ta shirya tasaka kayan dasuka mata mugun kyau babu comb hakan yasa tai parking gashinta like that kuma yayi kyau saita sake zama tadauki waya taga yanzu ma 7:30 na safe yayi. Tashi tayi ta tsaya ta kalli kanta a madubi har yanzu idanunta a kumbure but sun soma washewa and fuskanta ma jan dayayi yasoma washewa tayi wani irin shegen kyau, jikin aljihun lab coat nata ta kalla da aka rubuta Dr Rash tasake kallon madubi ahankali tace Mama I will not give up on your dream kinji Mama, zan zama abinda kikeso na zama, zanyi karatu zan dage zan zama wani abu Mama in sha Allah hawaye ne suka ciko idanunta danne kukan tayi muryanta na dan rawa tace Mama ina kewanki sosai but I promise I will be strong bazan kara bari makiyanmu suga kukana ba Mama Allah zai sakamana da ni da ke natafi school tasake goge idanunta tass ta gyara rolling datayi she looks so pretty Ya Allah, crocs din tasaka daidai kafanta kuma yamata kyau ta tsaya tana kallo mutuwan Mama yasa batamasan inda ta zubar da crocs din da Mama ta siya mata ba, goya jakan tayi tabude kofan dakinta tafito tafara tafiya daidai tahau kan staircase taji an bude kofa da sauri tashiga sauka daga stairs din dan bamataso ta ganshi wlh daidai tana zuwa wajen kofan falon tashiga bude kofan but a kulle ga duk kamshin sa yacika falon, jin takun tafiyanshi daidai yasa da sauri ta matsa gefen kofan tawani juyamai baya, binta da kallo yayi kafin yasa hannu ahankali yabude kofan yafice saida taji yafice sannan tajuyo ganin bashi awajen yasa itama tabude kofan ahankali tsaye taganshi jikin wani arniyan black bulletproof jeep yana sanye da babban kaya yadaura wani alkyabba dake walkiya yana haske yasaka hula akanshi but bai daura rawani ba tukunna, hada ido sukayi da mugun sauri tadauke kanta babu alamun any jokes a fuskanshi yabude mata bayan motan yace gobe driver ki zai fara aiki zoki shiga i will drop you off haderai Rashida tayi batare data kalleshi ba tace I can go da kaina babu abinda zanyi da motarka tai maganan tana saukowa daga matattakalan tazo zata wuce karaf Riyad yarike hannunta a zuciye tadago kanta ta kalleshi tace t to hakanan jitayi maganan ya makale a wuyanta sabida yanda yamata wani shegen kyau da kwarjini kayan sarakunan dake jikinshi yasa yawani cika mata idanu dasauri ta dauke kanta daga kallonshi tashiga kokarin kwace hannunta amman ko gezau babu wasa kan muryanshi yace matan Riyad can never enter public abin hawa take note! EPISODE Dasauri Rashida takalleshi jin abinda yafadi saikuma ta dauke kai takasa magana, cikin dan kakkausan murya yace nima bawai inayi bane cus i want to do nope, as long as igiyoyin auren mu are intact you re my responsibility and dole na cika hakkokina dake kanki you are too small kisa Allah yakamani dasauri tadago kanta ta kalleshi wani shu umin kallo ya zuba mata yace get in cus I don t want to ever force you kiyi wani abu, this is hakki akaina! Abu tahadiye awuya kaman ta shakeshi ta fizge hannunta da karfi tanaji kaman ta kurma ihu cikeda taurinkai tashiga bayan motan ta zauna kaman bataso ta shiga, driver dake wajen gate yataso dasauri ganin ta shiga ga mamakinta gani tayi yashigo bayan shima dasauri ta kalleshi danta dauka agaba zai zauna, gyara zama yayi sai kamshi mai bala in dadi yake, matsawa tayi chan karshe da sauri driver na zuwa ya duka yace Barka da fitowa Ranka shi dade, Allah ya taimakeka, Allah ya karamaka daraja! Gyadamai kai Riyad yayi ahankali, driver yasake dukawa yace barka da fitowa ranki shi dade uwar dakina juyo da kanta Rashida tayi haushin Riyad yasa tawani ballamai harara, da hannu Riyad yamai alamu ya rufo musu kofan, rufowa yayi yakoma ya shiga gaba yatada motan sukabar gidan sundan shiga hanya chan Riyad yace what time zaku gama? Kaman bada ita yake magana ba tai banza dashi, anatse yace ban baki izinin hawa any form na abin hawaba, I asked you wat time zaki gama? Yayi maganan yana zubamata idanu kaman bazatai magana ba chan tace nima bansani ba authoritatively yace mukaje zaki shiga ciki ki duba roaster and call me ki sanar dani, i will send my driver ya dauko ki cikin fushi tace ko an tashi inada wajen zuwa? Ahankali yace where? Shiru tayi tai banza dashi unexpectedly kawai taji ya fizgota ta taho jikinshi lokaci daya hannunshi yasa kan waist nata yarike gam, arude ta kalleshi jin yanda yakama mata kwankwaso hada idanu sukayi kawai taji gabanta na mugun faduwa sabida yanda yake mata wani shu umin kallo takasa magana sai kokarin kwace kanta datakeyi takasa tana numfashi da sauri da sauri, hannunshi akan waist nata kaman shock, strictly yace next time idan namiki magana open mouth ki bani amsa yadanyi shiru kadan yana kallon fuskanta kaman yau yafara ganinta kafin yakara pressing waist nata dayaga tawani zabura yace ina zakije after school ? Wlh she s breathing way to fast sabida yanda take kan jikinshi ga wani irin abu da hannunshi kema waist nata, ga driver na tukasu kuma babba ne driver ba yaro ba, kunya ma taji tanaji kaman ta shige kasa batasan sanda tace saloon zani nai kitso 4 zamu gama yana kallonta yace bazaki je ba! Da sauri ta kalleshi dudda gabanta na faduwa saida ta turomai baki cikeda stubbornness, lips dinta yabida mayen kallo
Chapter 64 · 0% Book details