Sashe 63
Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
first love. ATM card yaciro ya ijiye kan cinyanta dasauri ta kalleshi tace na menene wannan ? Da sauri ya tashi yawuce dinning adan kunyace, Munir yafara wani makirin murmushi yace Ammi wai matarshi yakeso ahadama akwati, komi da komi yakeso ki hadama Cousin dinmu, batada kaya duk ya kyautar da kayansu agidansu, I know his password Ammi I will tell you kallonshi Ammi tayi saikuma tai murmushi kawai bata sake magana ba cus bayama iya magana sosai. Rashida tadade zaune awajen gashi bataci komiba kuma takasa ci jin ana kiran zuhur yasa ta tashi ta shiga cikin asibitin tai salla tasake fitowa tazauna kasan bishiyan tai shiru titi kawai take kallo chan hawaye ya gangaro mata jin an kira asir yasa tasake tashi ahankali tawuce ciki tayi sallan la asar a jam i bayan an sallame tafito tana tafiya ahankali a gefen hanya harta fito waje takoma kasan bishiyan ta zauna, wani babban mota ne yayi parking gaban titin aka bude baya, Buba ne yafito yana sanye da manyan kaya da charbi a hannunshi ga hula da wandonshi nan daidai idanun sahu ustaz, Rashida na zaune kaman marainiya taji muryan Babba yace Rashidah! Dago kanta tayi ahankali takalli Buba da jajayen rinannun idanunta dasauri yaduka yace me kikeyi anan yanzun nan nafito daga asibiti naga wata kaman ke saikuma nacema me tukani mu biyoki nagadai kene me kikeyi anan ? Sauke kanta kasa Rashida tayi da muryanta da baya fita sosai tace bakomi Shiru Buba yayi Ammi tariga tagayamai komi dake faruwa wlh asibitin ma ita yazo nema sabida yakira Riyad yagayamai lallai nan tazo har office na Dr Bugaje yaje tacemai ta tafi yasake kiran Riyad shima yakira gida akace bata dawoba. Ga mamakin Rashida saitaga Buba yacire takalminshi ya ijiye akasa baidamu da fararen kayane ajikinsa ba yayi zaman sa yana facing nata saikuma yayi murmushi yace yanzu naga dalilin dayasa kika zauna anan gaskiya akwai ni ima ga iska ko? Shiru Rashida tayi batace komiba, murmushi Buba yamata saikuma yakai hannunshi yakama habanta yadago kanta like a little child Buba yace ni ba dan gidan Sarauta bane Rashida ni dan kauye ne, nine mahaifin Ammi, Malami ne ni a kauyenmu inada almajirai da yara dayawa, yanda nake Kaka awajen Riyad haka nake Kaka awajen ki, kin manta banace kome aka miki ki kira ki gayamin ba? Meya faru eh? Tell me, ko bakida kowa kinada ni kinji shiru Rashida tayi tana kallonshi hawaye na cikowa idanunta batasan mesaba but har cikin zuciyanta taji shi batajin haushinshi, ahankali Buba yace kina kewan Mamanki ko? Gyadamai kai tayi ahankali, Buba yace kinaji kaman rayuwanki batada sauran amfani yanda Mama bata raye ko? Sake gyadamai kai Rashida tayi ahankali Buba yace kinaji an cuci Mama dayawa ko ? Sake gyadamai kai tayi Buba yace kinaji kaman kiyita kuka kiyi kuka kiyita kuka da duka muryanki ko ? Gyadamai kai tayi sosai wannan karan ahankali Buba yace yi kuka Rashida yi kuka kaman yabude wani tap fashewa da kuka sosai tayi awajen Buba na kallonta batare daya hanata ba, shima Riyad dake chan dayan bangaren titi tareda Munir a mota suka tsaya suna kallonta dan tunda Buba yakira bata asibiti and bata koma gidaba hankalinshi yayi mugun tashi, dauke kai yayi daga kallonsu dasauri jin idanunshi natara ruwa kanshi na sarawa sabida ciwo yace s go I want to get her few things a super market motan Munir yaja sukabar wajen yace muje hospital kaga Dr ko muje gida yazo yadubaka wlh you re not feeling fine dan yatsine fuska yayi yace s just a slight headache na sami bacci me kyau zai tafi kallonshi Munir yayi saikuma yamaida kanshi hanya bai sake magana ba. Kusan 10minutes tayi tana kukan sannan Buba yace ya isa haka, ya isa ahankali yace tell me mekikeso yanzu? Kallonshi tayi takasa magana cus bataso tayi magana dazaiyi sounding kaman tanaso Buba yamai magana ya janye zancen bashin hawaye ne yasake gangaro mata daga idanu hakan yasa Buba yakai hannunshi yashare mata fuska anatse yace Rashida naga mahaifiyarki nayi magana da ita, iya sanina da ita da iya maganganun damuka yi abu daya na fahimta game da ita shine bata taba fatan wata rana ki tsinci kanki a irin halin nan ba, Rashida mahaifiyarki bazata taba jin dadi taganki zaune anan kaman marainiya ba kaman wacce ba a so ko zataji ? Girgixamai kai Rashida tayi, Buba yace kene farin cikin mahaifiyarki, kene abin kaunarta, kece hasken idaniyanta Rashida Mamanki don t want you to be this weak and like this Buba yanunata yace kinsan meyasa Mahaifiyarki tai rayuwa mai tsowa da lafiya? Girgixamai Kai Rashida tayi Buba yace sabida tasan diyarta is a strong girl! Tabata maganan Rashida yayi sosai Buba yace nasan an cuceku, nasan so many things are not right but Rashida dubi sama kiga Buba yadaga hannu yanuna mata sama hakan yasa yace shi Allah baya bacci kuma baya yafe hakkin wani akan wani, an kashe Mama amman an kwashe mata zunubi muna kyautata zato Mama yar aljanna ce, karshen ta yayi kyau Rashida meyafi haka? Buba yace trust me Allah zai sakama Maman ki, zaki sha kallo nan gaba, Allah zai saka mata wallahi kuwa Buba yayi maganan kafin ahankali yace Rashidah Mahaifiyarki ta rasu da buri aranta akanki na ganin kin zama likita ki ijiye komi a gefe a matsayinki na yar halak kiyi rayuwan cika burin mahaifiyarki become a Doctor, baki samu kin ceci mahaifiyarki ba but you can save other patients like Maman ki right? Gyadamai kai Rashida tayi tanajin wani karfi data dade bataji ba, Buba yace become somebody in life da zaki bawa mahaifiyarki daraja jama a su kalleki ace ohh yanzu yarinyar diyar mai HIV dinnan ce tazama haka Allah kabani y a kamanta nima hawaye ne ya gangaro daga idanunta Buba yadaura hannunshi akan kirjinshi yace Rashida ke jikana ne! Naji labarin abinda Riyad yamiki idan kinaso yanzu zan iya baki kudin ki biyashi ya sauwake mikin, kome kikeso I will support you and fight for you tun ranan namiki alkawarin nan kin tuna? Gyadamai kai Rashida tayi ahankali Buba yace kinason nabaki kudin kibiyashi ya sakeki? Shiru tayi tana tunani, Riyad insult her pride and ego, he used kudi sabida yasan batada su, ita kuma she will prove to him cewa ita Rashida ce diyar Mama, she will work hard for that money and pay him duk randa tagama makaranta, ahankali ta kalli Buba girgixamai kai tayi har kasan ranshi yaji dadi amman azahirance yace mesa? Cikin muryanta da baya fita tace inaso nabiyashi with my hard earned money, zan gama school zan fara aiki zan biyashi Buba basaika tayani biya ba shiru yayi yana kallonta yace naje dake kauyenmu toh? Girgixamai kai tayi ahankali tace gobe zan resuming zan dinga latti na bika cikeda damuwa Buba yace to me kikeso namiki tell me komenene zan miki, me kukeso ? Shiru tayi sai chan tace yunwa nakeji Buba EPISODE Wani iri Buba yaji yanaji data gayamai yunwa takeji da sauri yatashi yace bari inada abinci yawuce yana dan dingishi danya tsufa tabishi da kallo wlh tana sonshi sosai, mota yaje yadauko wani kula da ruwa da spoon bai damu da yanda ake kallonsu ba yadawo yamaida takalminsa ya zauna yashiga budewa yace dambu kishiyarki ta dafamin yau nace mata ni wajen amaryana Rashida zani kallonshi kawai take yanda yakeyi da sauri da sauri saiya debo Dambu a spoon yakai bakinta tsayawa tayi takalleshi ta kalli hannunshi da abinci da yanda yake kallonta sai taji zuciyanta ya tsinke ahankali tace Buba kai kadai nakeda shi yanzu tunda Mama ta mutu ta banni Jaaaa idanun Buba sukayi da sauri cikin dauriya yace imaza ci kisami karfi bance ki sakemin kuka ba kinaji gyadamai kai tayi tabude baki hawaye na gangarowa ta karba taci haka yadinga bata abincin taci kusan rabin flask din yabata ruwa tasha tsaf Buba yace tashi to muje na ijiyeki agidanki sai nawuce kauye biyar tayi batai musu ba ta mike tsaye suka wuce mota ta shiga baya ya shigo shima sannan driver shi yaja motan har GRA Buba yakaita akofar gidan sukai parking, wata kaka yadauka yaciro yan 500 bandir daya yakama hannunta yasa aciki yace ki rike kudin nan ki boye kinji, kome kike bukata ki saya dasu ina wayanki ? Ahankali tabashi wayan number shi yasa mata yace kome kikeso ki kirani kinji, kimin flashing yanzu nayi saving number ki, idan kunyi hutu a school kinaso kizo kauyenmu hutu ki gayamin zansa a kawoki okay? Gyadamai kai tayi Buba yace promise me bazaki kara kuka ba sabida hankalina ya kwanta kinga na tsufa dai ahankali tace I promise murmushi yamata yace sauka kitafi to Allah miki Albarka ahankali tace Ameen Buba nagode sauka tayi Buba yasauke glass yana lekata yace saida safe gyadamai kai tayi tana taba gate din aka bude mata security cikeda girmamawa yace welcome Ma gyadamai kai tayi adan kunyace ya matsa mata ta shige tana kallon gidan daya hadu ta hango uban cefene Security yace Ma Oga ya aiko da kayan abinci gasuchan idan kin shiga saimu shigar miki dashi Ma gyadamai kai kawai tayi awkwardly tawuce wajen kofan to ita ai bamata dauki key ba kayan abincin take kallo buhun sinkafa, semo, Irish, eggs, drinks, spices, yam, potatoes, beans, fruits da buhu na nama dana kaji dasuka fara tsiyaya sabida ba a saka a fridge ba batanan, key tagani jikin kofan ya makala mata hakan yasa tadauka ahankali tabude kofan kawai gabanta na fadi ta shiga cikin hadadden falon securities din sukace zamu shigo ma tsayawa kawai tayi cikin falon suka shigo sun daddauki abubuwa suka tsaya cikeda girmamawa sukace ina zamukai ma ? Rasa abinda zatace tayi ganin duk kallonta suke yasa tace kitchen wucewa kitchen sukayi suka shiga store suka ijiye, suka dauko naman suka jejjerea komi tsaf a freezer suka shigar da drinks sannan suka fito har lokacin tana tsaye a wajen sukace mun gama Ma, good night gyadamusu kai tayi suka fita saida taga sun rufe kofan sannan ta sauke ijiyan zuciya ta kalli katon falon bata taba ganin gida mai kyau in her life like this ba, yanzu agidan nan zata zauna harsai ta biyashi? Tadade tsaye awajen