Sashe 18
Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
dot tagama da hospital wanda a outpatient department group nasu yake tareda wani consultant na pediatrics, she s happy sosai yanda itada Bilal da crew dinsa na yanmata basa group daya, salla tawuce tafarayi a masallaci sannan ta linke lab coat nata tasa a bagpack tawuce tafito daga mosque din tagoya jakan abaya tasa takalmi tafito Keke napep ta tare zuwa hotel, sauka tayi tabiyashi ta shiga ciki ko kallon receptionist wajen batayiba as usual changing room tawuce tashiga cire kayan jikinta tayi ta saka dark blue dogon wandon da light blue shirt mai botur tundaga kasan rigan har sama wajajen wuya, farin fatan jikinta ya haska kayan sosai kaman dan ita akai uniform din, clean baby hijab nata far ta dauka ta saka wanda yarufe mata kirji sannan tasa takalminta, fitowa tayi zuwa office din Madam tai knocking akace mata ta shigo, shiga tayi tace good afternoon Afternoon Rashida oya ga card din jeki goge office din maza maza, ki dauko kayan gyaran office din a store karban katin tayi tace okay fitowa tayi tawuce store tahada duka abubuwan dazatai amfani dashi sannan tawuce elevator zuwa 5th floor tayi corridor office din, manna katin tayi kofan yayi kara sannan ta tura kofan ahankali hakanan kawai taji gabanta yafadi ga office din yayi mahaukacin sanyi kaman kankara AC a kunne, ahankali ta shiga tareda maida kofan tarufe cikin yar muryanta tace wayyoo sanyi dasauri tawuce wajen kashe AC ta kashe tanabin office din da kallo alamun an shigo dama jiya ance Oga yazo lokacin da zata tafi saisa ya shigo office dinshi kenan, a aljihunta tasa hannu ta zaro yar wayanta ta makala earpiece din a kunnenta ta danna wakan Araina Grande mai suna Into You, sannan takoma wajen kofa tadauko kayan ayyukanta tawuce bayi ta tara ruwa tafara bin wakan tafito tadauki handglove black na aiki tazura a hannu tadauki brush din share kura tafara aikinta tana waka Ko manager shi batasan yana nan ba babu wanda yasani sabida yanda yazo da jallabiya he looks like normal guest yawuce direct elevator, tunda yazo yake kwance dazun nan ne ma ya iya tashi yayi zuhur yakoma ya kwanta though ba bacci yakeba but ya lumshe idanu kawai having moment of peace, tunda aka bude kofan office din aka shigo yaji, sai chan kuma yaji murya mai bala in zaki tace wayyoo sanyi, saikuma ga same muryan tafara waka tana aikace aikace dake making sound, shi kadai yace is she some sort of DJ ko wata Artist? Cus muryanta dadi bata missing ko harafi daya, kaman tana performing a stage, chan kuma kawai saiya tashi zaune sabida ta kunna vacuum cleaner bayajin muryan nata da kyau kaman da, karan vacuum cleaner yafi muryanta kara, ahankali yataso yataka zuwa wajen kofan hannunshi yakai ahankali zai kama handle na kofan yabude kofan sai kawai yaji yafasa cus baimason aganshi amman kuma saiya tsaya chak awajen yanajin the way she s singing din cus takashe machine din yanzu tana bin wakan Into your arms na Witty Lowry, God! Her voice is captivating kawai yaji yakasa matsawa. Daukan bucket na mop din tayi a hannu tarike vacuum cleaner shima a dayan hannun ta tako zuwa gaban dakin sabida tagama da office sai uwardakan before wanke bayuka, juyar da fusknata tayi tana ijiye vacuum cleaner akasa still holding on to the bucket na mop takai free hand din tabude kofan ahankali fuskanta na kallon side din tana rera waka tadawo da hannun tana kokarin daukan vacuum cleaner back danta shigo tunda tabude kofan Tunda tabude kofan yayi setting eyes nashi chak akanta yana kallonta tundaga kan pink crocs din dake kafanta dayay finding nasu so funny, dogon dark blue wandonta dabai kamata ba at all kusan ma yaso yamata yawa ya kalla, zuwa navy blue rigan dashi ma bai kamata ba zuwa farin hijab din jikinta that looks extremely neat da side na face nata da he could see sajenta da dan gashinta baki sidik daya leko, daidai tadaga vacuum cleaner ta juyo da kanta kawai taga dogon farin mutum da farin jallabiya ajikinshi ya tsaya chak kaman gunki yazuba hannu a aljihun jallabiyan yana kallonta batada tsoro but saida ta tsorata tayi baya da sauri ganin namiji hakan yasa cord (wayan) vacuum cleaner ya kwasheta jikake timmm tafadi akasa ruwa mopping din hannunta ya kware mata daga ciki zuwa wando, zaro ido tayi atsorace tace wayyoo Allah na tai maza maza ta tashi tama rasa mezatayi arude tace I am sorry ganin kaman ba ghost bane maybe shine me hotel din takai hannu tana kakkabe jikinta da cinyanta da sauri chan ta lura da aljihuta ajike dasauri tace Innalillahi wayana hannu tasa a aljihun taciro wayanta ta cisge earpiece din tashiga tattaba wayan baya haske tace innalillahi Innalillahi bude wayan tayi da sauri taciro battery ta huhure wayan sannan tawuce table dagudu ta ijiye wayan awajen danya bushe sannan tajuyo tama kasa kallonshi taduka tana daukan mop tace sorry i will clean everything yanzu chak yake kallonta dan yana ganin full fuskanta ya ganeta the girl from the airport! The feisty gurl! Yarinyar daya dade yana nema to reward her for saving his life GOGAN NAMU BATA GANESHI BA? KODAI IDONANE SANYI DA ZAFI