← Book details Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 71

Sashe 27

Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

mata kyau sosai ta goya jakan school abaya da pink crocs din nan akafanta sai wayanta dake hannunta tana gumi a goshi dan da kafa tazo gashin gaban kanta duk sun kwanta, ko kadan batasan zata ganshi ba ganinshi yasa ta hade rai sai kawai ta shigo ta ijiye jakanta kan kujera tazo ta gefenshi takai hannunta da sauri ta taba goshin Mama tace Mama ya jikin meke miki ciwo yanzu ? Dauke kanshi yayi daga kallonta Mama tace lafiya na kalau da idanu ta nuna mata Riyad hakan yasa ba yabo ba fallasa tace sannu wayanshi yaciro yashiga dannawa Mama tamata dakuwa da hannu hakan yasa ahankali tace ina yini shiru yayi chan yace sai shegen jiji dakai sabida yaga yanada hotel halama na babanshine ba nashi ba tafadi aranta, maida wayan yayi a aljihu yamike tsaye yace Mama bari naje dasauri Mama tace nagode nagode Riyad Allah maka Albarka nagode kaji saika dawo agida Mama zasuji yayi maganan yana juyawa yawuce yafita wucewa wajen wardrobe na dakin Rashida tayi taciro kudin tarike a hannu tace ina zuwa Mama kafin Mama takirata harta bude kofa tafita daga dakin dagudu tabishi abaya ita bama tasan sunanshi ba hakan yasa ta kasa kiranshi gashi wayanshi na kunne har parking space yabude mota ya shiga mota yana kokarin tadawa tai knocking glass din hakan yasa yasauke glass din kasa ya zubamata mayun idanunshi haka nan taji gabanta yafadi kawai saitaji muryanta ya makale, dan gyaran murya tayi kadan duk yana kallonta sannan tadago hannunta dake dauke da kudin ta mikamai yabi kudin da kallo da aka daure da lobari sannan yajaye idanunshi dagakan kudin yazuba mata manyan idanunshi still baice komiba aranta tace amman anyi dan wulakanci anan saikuma ta daure ganin kallon kudin me yake mata tace 150k ne nan, sauran kudin daka kashe I will pay you back small small dauke kanshi yayi daga kallonta ya kunna motan kaman wanda akace dole yayi magana yace keep your money ban bukatanshi jitayi ranta yafara tafarfasa sabida yanda yayi maganan a wulakance ta kalleshi tace nikuma ban bukatar taimakon ka ko angayamaka i need your help to take care of my mother ne ? Da kokarin yin reverse yake but jin maganan ta yasa ya dan dakata yakalleta yace you need all the help Rashidahhh! Faduwa gabanta yayi yanda yakira sunanta saikuma amsan daya maida mata yadawo mata wani irin sparking taji tanayi zatai magana taga yayi reverse abinshi yana kallonta yana saka wani bakin glass a idanu sannan yajuyar da kan motan yafice abinshi kaman ta kurma ihu takeji. SANYI DA ZAFI
Chapter 27 · 0% Book details