← Book details Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 71

Sashe 2

Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da gaban wando yana kokarin kiran waya, yashiga gudu shima yana binshi abaya, sosai yake gudu ganin daya yabiyoshi yanakai hannunshi cikin wando dan ciro wayanshi yakasa kawai yahau staircase yashiga sauka yana kallon baya jin gudun sahu dayawa ana biyoshi dudda baya ganinsu dan basu riga sun hayo benen ba ganin wani kofan restroom na mata dan ansa ladies ajiki yasa kawai yabude kofan yafada jiki wani kalan mugun karo sukaci dan tana shirin fita ne tai tangal tangal zata fadi da bala in sauri ta dafa bango shikuma yajuya ya tura kofan bayin dasauri tareda saka sakata na sama da kasa yana kara murza jam lock sannan yajuyo daidai tana dagowa tana shafa goshinta cikin tsananin fushi dan tadan buge kuma taji zafi zatai magana, cikin a very soft yet anxious voice guy din yace please ki boyeni some guys naso su kasheni ne and call the police dudda taji zafin bigewan datayi amman ware manya manyan dara daran idanunta tayi kaman fitila tana kallon mutumin dayashigo cikin bayin mata da ranan nan Allah yaso ba kowa ciki ma, farin guy ne bawai irin fari sosai dan zata fishi haske but yanada normal fair skin not black skin, dogo wanda akalla zaiyi 34-35 ko 36yrs hakanan, baida kiba at the same time baida rama, yana sanye da riga na latest collection na Dior fari yadaura wani leather brown jacket asaman sa da yabar boturan abude bai rufe ba hakan nasa kana ganin farin rigan ciki, saikuma yasa jean na Rick Owens, sai wani boot dake kafanshi brown na Tomford mai bala in kyau da agogo daure a writs nashi na rolex, yanada very very dark hair dake nan kwance so wavy, dark eyebrows da eyelash nashi yamafi na wasu mata yawa, ga dan gemu dayake dashi da saje acike dudda gemun baida tsayi sosai looks like yana trimming gemun dan hair na wajen gabaki daya na dsame length, lips nashi are full irin asalin masculine lips that are a bit pinkish, idanunshi sunyi jaaa sosai, ganin yanda take kallonshi yasa yace call security hankalinshi atashe yadanna kofan da hannunshi yana kallon kofan jikinshi nadan rawa kana gani kasan da gaske he s in trouble jin gudun mutane dayawa haka ga maganan su yana tashi kasa kasa baku ganshi ba? We have to kill him ance kar mubari yakai gida araye wannan kofan fa kunduba ciki ko ya boye wajen ? Hankalinshi atashe yajuyo yana dan zaro idanu hakan yasa itama gabanta yafadi bayin tashiga kallo kafin idanunta su sauka kan cart din garbage can dake wajen wanda take juye dattin bayi aciki ta gungura tafito dashi takai bola, daga kafanta tayi without making sound taje ta tsaya kusada can din tasa hannunta ahankali tabude marfin sannan tadago kanta daidai sun fara knocking kofan zaro idanu yayi da sauri ta nunamai can din da hannu alamun yazo yashiga nan da sauri yazo ya tsaya kusada ita yakalli bolan cikin can din wani kalan yatsinewa cikinshi yayi yaji kawai amai yatasomai da sauri yadaura hannunshi kan bakinshi jin aman zai fito, tazaro idanu tana kallonshi yau da babuma wani bolan kazanta sosai ma shine zaiyi amai lallaima, daidai an kara knocking dasauri da murya kasa kasa tace kaga idan bazaka shigaba nifa ba ruwana, kafita ni nacigaba da aiki na, I don t have any security number I don t work here yau kawai an kirani nai replacing wata ne just for today juyo da kanshi yayi yakalleta itama kallonshi tayi da manyan idanunta kusan iya kirjinshi tsayinta ya tsaya daidai anyi mugun knocking kaman za a balle kofan baisan lokacin dayay tsalle yafada cikin trash dinba yasa hannunshi yana kama hancinshi lekowa tayi takalli ciki yanda yakeyi yasa tai dariya dayasa fararen hakoranta suka bayyana more of dariyan mugunta tace yi bacci toh kallonta yayi yanda take dariya dimples nata na lotsawa bama ta tsoro yanda kasheshi akeso ayi, bama ta tsoro tana mace itama sujimata ko su illatata, he s just staring at her da suprise, jakanta dake kan slap ta kalla saita wuce da sauri tabude taciro wani black gyalenta na abaya tazo wajen ta warware ahankali ta yafa kanfuskanshi, wani irin lumshe idanu yayi jin kamshi mai sanyi daya sauka kan fuskanshi mai ni ima in this moment na wari dayake ciki sai kuma ya sauke gyalen da sauri ya kalleta yace wat are you doing? Tana kallon kwayan idanunshi itama ba kunya ko shakka tace datti zan watsa akanka yanzu so brace up takai hannun tadauki thrash can dake kasa wanda bata riga tajuye dattinshi ba kawai tajuye asaman kanshi tana murmushi ganin yanda yake kallonta kaman zai rufeta da duka tace I am saving your life here it s your choice wani kalan ijiyan zuciya yake saukewa tsigan jikinshi natashi da kyar yaja gyalenta yarufe fuskanshi dashi yana rufe idanun duka dan yakasa standing dattin datake watsamai akai ta ijiye can din tasa hannunta dake sanye da working glove nata ta kwashi satt n ta rurrufeshi da kyau sannan ta rufe marfin tadan sauke ijiyan zuciya cike da karfin hali tawuce tai wajen kofan tabude cikeda masifa tace wai waye ke knocking haka ina aiki ? Ganin maza kusan biyar yasa tadan koma baya kadan ta tsaya chak tana kallonsu dudda gabanta na faduwa bata nunaba dukansu kallonta suke ganin wata yarinya da akalla zatai 22yrs haka tana sanye da cleaners uniform riga da wando ash color tasa wani karamin farin hijabi daya tsayamata iya kirji hannunta sanye da glove kafafunta sanye da rain boot, cikin rashin tsoro tace baku iya karatu bane duk girmanku ku gane ladies restroom ne nan ? Dukansu kallonta suke ganin yanda take musu magana gata wata kalan kyalkyawan yarinya fara sol saidai akwai uban baki ga rashin kunya ga muryanta shegen zaki kaman zai fasa dodon kunne, babban ne yahade rai yace ke wani bai shigo nan ba ? Wani kalan matsiyacin kallo tamai tace kai nan wajen yamaka kama da inda wani zai shigo ? Dukansu baki suka sake suna kallonta daya daga cikinsu yace ke kinsan waye mu kike mai rashin kunya ? Tana kallonshi tace kai kasan wayeni zakuzo ina tsakiyan aiki na bayan nayi stating agaban kofa working no entry kunzo kuna bubbugamin kofa kuna maza toh ubanme kukazoyi nan kuje men restroom mana, I will call security wlh kallonta Oga yayi this loud girl can ruin work nasu ta tara musu jama a yanda take this vocal ma killing her will never be easy still saita tara jama a, they don t want scene hakan yasa yace please let her be she s crazy, I don t want problem, ku rarrabu kuje mu nemoshi ni nasan yana floor din nan tsaki tayi tace mahaukata kawai dukansu su shiddan juyowa sukayi suka kalleta wlh ko dar batajiba tasa hannu ta maida kofan ta buga tarufe tadauki wayanta ta danna waka tamaida earpiece tacigaba da mopping kasan wajen wanda shiya rage mata dama tariga tagama wanke cikin bayukan yanda takebin wakan tana aikinta bata missing any verse wlh zaka dauka mawakiya ce kuma da karfi take wakan abinta.. Dudda yanajin warin bolan dayake ciki kaman zai kasheshi ga tsoron dayakeji but hakanan muryanta da yanda take wakan hold on na calming nashi down sosai, muryanta yamafi na asalin wanda yayi wakan dadi, what a voice! Tass tagama aikinta ta jingine komi inda zata jingine sannan tadauki jakanta tarufe tagoya abaya tasa hannu tabude kofan bayin hada ido tayi da maza biyu daketa sintiri awajen ta ballamusu harara tacire board na close dake gaban kofan bayin takoma ciki ta ijiye sannan ta gunguro garbage can din da kyar sabida nauyi amman ta daure tafita tafito dashi ko kallonsu batayiba saima wakanta data cigaba dayi abinta tawuce tasauka har kasa tazaga baya inda suke ijiye dattin saida ta jujjuya ganin babu kowa yasa tabude marfin bolan batare data kalli cikiba tace you are safe yanzu you can come out kafinma ya yunkuro tajuya abinta tahau tafiya dan sauri take is already 3:30 by 4 zata shagon abinci gashi this whole drama yabata mata lokaci, da kyar ya iya ya lallaba yafito daga bolan sai amai duk wani abu dayaci saida ya amayar dashi sai kakkabe jikinshi yake yadago zai mika mata gyalenta daidai tanashan kwana harta tafi, he wanted to say thank u dudda she s a crazy wicked girl tana zubamai dirt tana murmushi but she helped him, hannunshi yakai aljihunshi yataba but baiji wayanshi ba kuma baisan a ina ta fadi ba wlh kuma shi bazai duba bolan nan ba, daidai wani cleaner na gunguro nashi bolan dasauri yace please bani aron wayanka nakira binshi yayi da kallo ganin kaman ba lafiya yasa yabashi wayanshi Munir yakira kafin yayi magana yace Munir kazo ka daukeni a airport pls karka fadama kowa kana zuwa katambayi wajen zuba bola ina wajen kafin yayi magana ya katse wayan yabama yaron yazauna awajen kawai feeling terribly sick kusan 1hr yana wajen jikinshi yadau mugun zafi ga tsigan jikinshi na tashi kaman zai mutu yana zaune ahaka yaji ance. Riyad dasauri yadago kanshi da gudu gudu sauri sauri Munir yataho wajen yace what happened to you like this? Wat are you doing here? Why are you so dirty ? Tashi yayi yana kokarin yima Riyad magana yace someone tried to kill m kawai ya sume da kyar Munir yasamu wani cleaner yazo kawo datti shima aka tayashi daukanshi suka tafi mota aka sashi sai gida bayan yakira Mom akira Dr. Tawani special secret gate Munir yabiyo aka budemai already ga mutane tsaitsaye Gwaggo (Mai Babban daki) gawata black beauty mata dake sanye da hijab mai dan kiba (Mom), Wambai, Waziri, Kabeer da su Halilu, Ibrahim da Shuaibu, Baffa Mujitapa dukansu suna wajen da family Dr nasu, yayi parking agurguje Munir duk sukai wajen fashewa da kuka Mom tayi tace what happen to yarona Munir? Wakeson kashemin shi daga shigowanshi garin nan? How did they even know ya shigo? Gwaggo jini a hannunshi look, Doctor do something Mom tai maganan tana kama hannunshi ashe wukan ta yankeshi dazu, atare dukansu mazan suka ciccibeshi zuwa wani dabkareren flat na Mom Gwaggo tace meya sameshi haka Munir? Jibi jikinshi? Meya faru Munir ?
Chapter 2 · 0% Book details