← Book details Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 71

Sashe 26

Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ijiye ledan dake hannunshi yay na gefen gadon yace ya karfin jiki Mama ina kwana murmushi Mama tayi tace jiki Alhamdulillah naji sauki, nagode da kulawa ka kawoni asibiti banda bakin maka godiya Allah maka Albarka takalli Rashida dake tsaye wajen kofan tai folding hannu tace baki iya gaisuwa bane ko akwai abu abakinki ne dan juyawa tayi da kyar tace ina kwana baki Mama tasaki tana kallonta ganin baka yasa da kyar tace mungode dasauri Mama takalleshi tace Ya sunanka ne? Ahankali yace Riyad sunana daidai lokacin akai knocking tareda shigowa dakin wata ce tana sanye da uniform na ma aikata tace good morning Ma dazu nazo nakawo muku breakfast naga kuna bacci natafi dashi dan karyayi sanyi yanzu zanje nakawo muku tawuce tafita daga wajen kofan akunbure Rashida tace Mama kicemai yasa a sallamemu mutafi asibitin mu dan juyowa yayi daga inda Yake yazuba mata ido dauke kai tayi strictly yace Dr yace 3days Mama zatayi anan and hakan ne zai faru dasauri Mama tace Riyad kaga ai dawainiyan zaiyi yawa ta ina zamu sami kudin biyanka? Dan Allah kasa asallamemu naje general dana saba zuwa kaji, Allah yamaka Albarka Allah yakara daukaka daidai lokacin aka kawo abincin breakfast ne omlete da bread toast sausage tea dakuma bowl na fruits yarinyar ta saukar dama da Mama wajen ijiye abinci kan gado sannan takai dayan abincin kan table sannan takalli Riyad tace Sir do you need anything No thanks yafadi atakaice, Mama ta kalli Rashida dake tsaye kikam har lokacin awajen kaman mai gadi tace zokiyi kari kitafi school don t even tell me bazaki ba kaman zatai kuka tace Mama ni banso naje wazai zauna dake natafi I will be here with Mama a Mama har Rashida dukansu kallon Riyad sukayi, hakanan Mama kawai taji tanason natsuwan yaron, abin yana mata ma kaman tasanshi batason tai rubbing in his face hakan yasa tai murmushi tace to kinji Riyad zai zauna yatayani hira zoki ci abinci kitafi school kinyi katti already banson kina fashi a school kije gida ki shirya kitafi bataso taje school ba but abinda yafima damunta is wannan mutumin dayakeyi kaman irin ya sansu din nan ko su yan uwa ne saiwani shishigi yaje musu mutumin da shekaran jiya ta sanshi, batason tai gardama sabida Mama batada lafiya hakan yasa ta taho wajen gadon gefen Riyad ta ballama jakan abubuwan dayakawo harara karaf akan idanunshi sannan tadauki jakanta dake wajen ta taso tajuyo hada ido sukayi tadauke kanta tajuya Mama tace abincin fa akufule tace ni bazan ci ba tawuce wajen wardrobe na dakin taciro kayan jakan an Mama daya kawo ta maidasu ciki kudin taboye karkashin kayan sannan tawuce tai hanyar kofa tace natafi tabude kofan tafice ijiyan zuciya Mama tasauke tasa cokali ta a abinci tace I have a very stubborn yarinya Riyad dan murmushi kadan Riyad yayi baice komiba, Mama tai shiru kaman mai tunani tace s all abinda na mallaka aduniyan nan saita dauki fruits takai bakinta tafara taunawa sai kawai tafashe da kuka as if she s holding on to something ahankali Riyad yace Mama stop crying she will stop being stubborn soon duk yarinta ne, zata dena nan gaba, stop crying kinji Mama is not good for you zai hanaki warkewa ijiye spoon din tayi takai bakin hijabinta ta goge fuskanta tace ciwo na bana warkewa bane, HIV gareni Riyad tadanyi murmushi tace I don t even know why nake fadamaka nasan kariga kasani Rashida tacemin agabanku abokiyar aikinta tace inada shi tai shiru sai kuma ta zufar da iska da a bakinta tace ve caused Rashida pain tun tana ciki na, yarinyar nan tayi girma cikin bullying din society yar fasika yar mazinaciya yar me HIV so sometimes I don t even blame masifa da fadan da stubbornness nata society shaped her to be that way dole tai finding means na yanda zatai surviving. Mama takara shiru saikuma tasa hannu tadauki bowl din fruit din tarike tadauki spoon tadau lemu zatakai baki is as if akwai so many things acikin zuciyanta dake damunta tace wlh, wlh tunda nake arayuwana bantaba fasikanci ba, inada cikin 6months ina laulayi sosai aka kaini hospital akamin gwaje gwaje the next thing inada HIV, aka gwada Mijina baida shi, kishiyata ma baidashi babu wanda ya yarda da magana ta, Mijina ya koreni, yamin koran kare, nakoma garinmu dayake dagani sai yayana iyayenmu suka haifa shima ya koreni wai bazan jamai abun kunya ba yana babban mutun a kauye karnazo naraba ma kauyensu kanjamau, haka nai garari aduniya da ciki ajikina Tasakeyin shiruuu tana kallon bowl na fruits din tace har yau har yau bansan tayaya nakamu da HIV ba Riyad, haryau bansani ba saikawai tafashe da kuka dayasa idanun Riyad sukai ja yasauke kanshi kasa Mama tabashi tausayi and wlh he believed her cus you can see honestly a maganan ta, her body language, maida bowl din tayi ta ijiye tace cikin garari na haifi Rashida, komi nawa saida na saida just to sustained bata madara dan ban bata nono ba haka likitoci suka gayamin, ina zuwa clinic lokacin da karfina nafara aikace aikace ina goyata ahaka nasata school ta taso tanada ilimi har yar baiwa ake kiranta lokacin, cikin wahala sosai Rashida ta tashi, ba gatan uba ba gatan yan uwa, just ni kadai takedashi, tun batasan menene HIV be sabida yanda jama an unguwa ke constantly singing dinshi akanta tazo tasan menene shi, tana wajajen JSS1 karfina yasoma gasawa as small as that girl sai ita tasoma zuwa gidajen danake aikatau tanayi amadadina nina zauna agida sabida rashin lafiya tundaga lokacin kawowa yau Rashida dakake gani itace ci na, sha na, suturata, wajen zamana, magunguna na, kudin makarantan ta da komi, anywhere da zata samu aiki tayi she wants to go sabida batason taje taroki kowa yamana abu, ko an kawo mana taimako bata amsa, she s 23 but she works like a 45yrs old man Mama tai shiru tasa hannu ta share fuskanta chan tace Riyad I ve become a burden arayuwan y ata, I ve become a curse in her life, I believe idan na mutu she will enjoy life better Mama! Riyad yakirata da sauri, fashewa dawani irin kuka Mama tayi takalli Riyad tana bubbuga zuciyanta ta saman riga tace I am hurt sabida I have the best daughter a duniya dabana iyama komi kawai nasata a wahala ne, I am selfish Riyad dan dana haifeta dazan iya kaita gidan marayu amman nace nizan raineta ta taso suffering, yara yammata irin ta suna gidan iyayensu akillace nawa na garari aduniya from morning to night bata airport, bata shagon abinci, bata hotel tana shara da wanke wanke da wanke bayi just to make ends meet, so I am selfish Riyad Mama tafara sheshekan kuka da kawai kasan matan nan ta tara abu dayawa azuciyanta ne tace na zaman ma Rashida alakakai arayuwa, na zaman mata annoba, sabida ni kullum aiki take, kowace yar budurwa na gidan iyayenta na jin dadi iya yen na nemo abinci su bata taci ni tawa ke gararin duniya ta nemo tabani naci, I ve burden my poor daughter, I don t deserve to be her Mother wlh I do not!! Tashi Riyad yayi ahankali yazauna bakin gadon dan kukan da Mama take is getting too much, calmly yace Mama don t say that, you are wrong Mama! Ahankali yace kinsan yanda yarki ke sonki kuwa? Saikuma yasa hannu a aljihunshi ya ciro handky yamika mata yace goge fuskanki Mama nabaki labari da kyar Mama tasa hannu ta karba ta share fuskanta tass takalli Riyad da jajayen idanunta, dan murmushi yayi just to calm her down but jiyake kaman yamata kuka shima yace Mama all abubuwan dakike tunani akan yarki is totally wrong cus I see complete opposite of abinda kika fada dan shiru yayi kaman mai tunani chan yace all I see a idanun yarki is you are her motivation, her inspiration, her strength, her confident, Mama kece dalilin dayasa yarka is strong! Fearless and resilient, bold, I witness how she fought with her soul sabida ke Mama! Dan murmushi Mama tayi ganin haka yasa Riyad yace Mama ke kinga yanda tayi ne ai harni namiji saida na tsorata kartazo ta hada dani daidai lokacin Mama ta kwashe da dariya yanda yayi maganan was sooo funny, ganin tai dariya yasa cikedason kwantar mata da hankali yace Mama karki taba tunanin ke burden ce arayuwan ta ko curse all I see is kece the whole entire reason na existence nata, Mama yarki na sonki fiyeda tunaninki and duk yaran dake son iyayenshi bata taba daukansu koya kallesu a matsayin wahala kowani abu trust me Mama murmushi Mama tayi tana kallonshi har cikin ranta taji sanyi da maganganunshi yace idan you want her to keep being her ki warke kiji sauki sabida hankalinta ya kwanta Mama inba hakaba rashin lafiyanki will shatter her tiny little heart I m sure ko ina take yanzu hankalinta rabi da kwata na kanki she might not concentrate ko a school right ? Gyadamai kai Mama tayi ahankali saikuma chan tace nagode Riyad, you made me feel good murmushi yamata yace kici abincin ko zakisha yoghurt ? Gyadamai kai Mama tayi freely kaman ta sanshi da dadewa kawai saiya sauka daga gadon yabude ledan daya kawo yaciro komi yakawo ajuwa dates, ruwan Zamzam babban gora dakuma yoghurt, cup ya dauka na tea da aka kawoma Mama yaje ya zubar Mama sai binshi da kallo take ta natsu da yaron kaman tasanshi da chan, yataho da cup din ya tsiyaya mata yoghurt din aciki yabata karba tayi ahankali tace bani dabinon dasauri yabude daya yabata ta karba yadawo ya zauna tashiga sha tanacin dabinon wlh haka ya zauna da ita sai hira suke kaman sun san juna har Dr yashigo yadubata yadan shiga hiran shima na 5min kafin yawuce yatafi wajajen zuhur yafito yatafi masallaci ana idarwa yadawo yazauna Mama tace bakaci komi ba cikinshi yataba yace kuma yunwa nakeji sosai Mama tea kawai nasha dazan fito dasauri Mama tace tashi kaje gida kaci abinci dan Allah zaiyi magana aka bude kofan dakin da sallama Rashida ce tana sanye dawani material ja dogon riga ne har kasa ta yafa gyale baki kayan sun
Chapter 26 · 0% Book details