← Book details Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 71

Sashe 31

Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jikinshi kaman magic, kafanshi kafanshi sanye da Jordaan leather loafers brown, hannunshi daure da agogon Audemars Piguet, dayan hannunshi rike da waya samsung galaxy fold, ba hula gashin kanshi ya kwanta yana sheki sai kamshi yake zubawa, dauke kai tayi da sauri daga kallonshi dan he s so clean wlh ko datti ko stain ko tabo guda daya babu ajikin kayanshi, haka kayan a goge babu squeezing ko daya, shima tundaga kan kafafunta dake sanye dawani black takalmi flat da duk an dinke ya kalla dudda fararen kafanta are shinning ga long fararen nails na kafanta da babu lalli ko daya akai zuwa ataman dake jikinta da hijabin da ledoji biyun dake hannunta bakake data rike sannan yazubama fuskanta idanu she looks tired, she s even sweating a goshi dan duk gashi ya kwanta a goshin nata, ga lips dinta sun bushe kaman she s a bit sick. Kallon fa ? Tai maganan cikeda rashin kunya dayasa ya daidaita kwayar idanunshi cikin nata dasauri ta janye idanunta hakanan taji takasa kallonshi but tsabagen karfin hali tace kadena zuwa gidanmu banso cikeda isa kaman anyi forcing nashi yayi maganan awulakance yace are you angry ba wajenki nake zuwa ba ? Wani dum! Taji saukan maganan da sauri ta kalleshi tsaf shima yake kallonta mene mutumin nan yace? Mema ya dauketa? Taji haushi dan ba wajenta yake zuwa ba on wat ground? Kokarin hado martanin dazata bashi take dan she was a bit speechless but yarigata wani kallon raini yamata calmly yace bakida matsayin dazan zo nemanki yana maganan yabi ta gefenta yafice wlh takai 1 good minute fassara maganan shi take akanta taji ranta na kumfa dasauri tajuyo tafito kofar gida daidai yaja motanshi tabishi da kallo yana wani saka bakin glass a idanunshi ko inda take bai kallo ba yawuce abinshi kaman zata hadiye zuciya tamutu tace nima ka isa kazo wajena ne aka gayamaka? Sai ji dakai kaman wani dan shugaban kasa sabida yana takama da dan hotel din dayake dashi I will leave your company soon zan nemi wani hotel din wlh kuwa tana maganan tajuya tana saisaita bacin ranta takoma cikin gidan kaya tagani cikin gidansu harda su indomie da kwalin kwai kudan 5 crete gasu manta manyan roban madara Milo oat, wlh shopping data gani zube a compound yakai na 300k ga bandir na kudi kuma ijiye kasa na yan 1k guda biyu dasauri ta shiga ta tsaya gaban kayan ranta abace tace Mama waya kawo mana abubuwan nan Ahankali Mama tace Riyad yakawo kaman zata fashe sabida bacin rai tace Mama shine zaki karba? Kallonta Mama tayi tace babu yanda banyi dashi ba amman yaki yarda wai ni mahaifiyar sa ce kodan darajan azumi na amsa, kinga uban kudin daya ijiye dane naki amsa da kyar na zari yasake daura daya, haka ya ijiye komi anan dan ni naki karba cikeda bakin ciki harda abinda yamata a zaure tace Mama shine baki kira yara kinsa sun maidamai da kayan mota ba ? Kaman wacce aka daka kawai saita fashe da kuka sosai ta ijiye kayan data shigo dasu daga kasuwa nan kasa ta tsallaka tashiga daki kawai tahau kuka idanunta sunyi jajir tashi Mama tayi tabiyota ciki cikeda damuwa tace Rashida mekuma haka da kuka? Duk mai imani yadaga ido yaga rayuwanmu dole yaji tausayinmu, na karba badan komi ba saidai naga yaron kirki ne hakanan zuciyana ya natsu dashi kuma bawai saurayi bane ya gayamin yanada mata so mutum ne mai hankali ba yaro ba, saikuma dalili nabiyu shine karbansu zai saukaka miki kema at least daganan zuwa 2month zamu manta da siyan Kayan abinci albashin dazaki samu saimu hada da wayan nan kudin ki biya kudin school fees ragowan mu rike na asibiti, you think I m happy da rayuwan wahalan dakikeyi? Understand me it s Ramadan kyaututuka haka is normal ko na yan anguwan man sabida baki karba ne da yanzu an kawo mana, it s okay ya isa stop crying Mama tajawota cikeda lallashi rabon datai kuka haka tun ranan da aka kwantar da ita a asibiti cikin kuka tace Mama stop collecting abu daga hannun kowa, I m enough for you, Mama bazan taba bari ki kwana da yunwa ba, I will never hawaye taji yaciko idanunta saikuma tai murmushi ta danne takai hannunta ta share mata fuska tace I know y ata will never allow me to go hungry, natuba to bazan kara karban komi daga hannun kowa ba, Rashida na is enough for me, the best daughter aduk duniyan nan, come here Mama kawai ta rungumeta tana murmushi she s lucky Allah ya azurtata da y a dake sonta haka, sun dade ahaka sannan Mama ta dagota takai hannu ta yaye hijabin jikinta ta tana taba wuyanta tace jikinki da zafi baki da lafiya ne ? Ahankali tace cikina ke ciwo kadan gobe naje asibiti zan karbi magani cikeda so Mama tace sannu kinji, zauna kihuta ni zan miki girki dasauri tace zanyi Mama tashi zatayi Mama takama hannunta bawasa kan fuskanta tace zauna kihuta zama tayi Mama ta tashi atampanta tafara dubawa ta yaba sannan tashiga daura musu abinci itakuma anan bacci yayi awon gaba da ita. Da kyar Mama ta tadata around 4 na asuba sabida suyi sahur, tariga tasan bata azumi wucewa tayi tama Mama abincin sahur sannan tawuce bayi yau da hot water tai wanka dan zazzabi takeji da ciwon mara but she feels she can manage dan is not that serious tana dawowa takaima Mama itama nata ruwan zafin tashigo daki tace muje Mama idanunta Mama ta kalla tace dan Allah kina zuwa clinic kisha magana kar zazzabin nan yarufeki da kyau kinji gyadamata kai tayi Mama tace barshi zan iya zuwa bayin da kaina jeki kimtsa batai musu ba ciki tawuce tashiga kimtsawa tasa black abaya tahada jakanta na baya saikuma ta kara kwanciya yawanci a rashin karfi ne kafi gane Rashida is sick dan baka ganewa a baki da fuska sabida masifa da fada, shigowa Mama tayi ganinta a kwance yasa Mama tace namiki shayi ? Girgizama Mama kai tace idan naje school zanci abinci Mama karki damu da dan damuwa Mama tadauko mai tana shafawa hartai salla tana kwance wajen saima lumshe ido data farayi sai kawai Mama ta barta zuwa 7 ta tabata tace tashi kitafi school tashi tayi ganin Mama tafara damuwa yasa tace laaaa Mama kinga najini garau maybe dama baccin danake ji yakara karamin zazzabi 200k na jiya Mama takawo da 100k nasu tasa asama tabata tace gashi ki biya kudin makaranta kisai yan littafan da baza a rasa ba kallon kudin tayi zatai magana Mama tace ni Maman ki aka bama kudin nan, nikuma nabaki, kaman yanda Hajiyan nan taraba mana 20k a clinic naje na siyamiki crocs consider wannan kudin haka, go and pay school fees naki and buy textbooks dakike bukata ayanda fuskanta kadai yayi kasan bataso ba but ganin yanda Mama tayi yasa tasa hannu ta karba kawai tasa kudin ajaka ta goya, taja black gyale tashiga rolling tai kyau kaman balarabiya dudda bakomi akan fuskanta sannan tace Mama natafi 5k takara cirowa cikin kudinsu dabaifi 50k ba Mama tabata tace dan Allah kihau keke yau, kici abinci mai kyau a school kinji gyadama Mama kai tayi tace natafi Mama thank you adawo lpy Allah bada sa fita tayi tana kaiwa junction ta shiga cafe tai printing ramita, sannan tafito tashiga keke sai bank taje tafara biyan school fees nata sannan tafito tashiga keke again sai asibitin su, sauka tayi wuraren 9:30 taga student nasu Maimoon na hangota ta taho wajenta dagudu tace anyi releasing namu yau, kaman za ayi manyan baki ne dai ance mu student mutafi wlh ahankali tace really, bari na karbi magani to natafi dasauri Maimoon tace meke damunki ? Dan yatsine fuska tayi tana tafiya tace I think I m coming down with Maleria saikuma cramps Maimoon tace oh no sorry office nasu tashiga tabude locker ana ijiye musu magani haka tadauki na Maleria da cramps suka fito yawance Maimoon ke hiran, ahankali tace I want to buy food da water dazansha magani dashi dasauri Maimoon tace muje cafeteria Jellof rice tasaya da beef 800, tasai ruwa daya ganin tana bude jaka yasa Maimoon tace mu zauna anan kici mana girgiza kai tayi tace kema kawai na gayamiki ne only Mama na ke sani idan bana azumi I don t want people knowing kunya yake sani dan murmushi Maimoon tayi tana kallonta yanda take arranging abincin ajaka tana maganan she looks so cute and adorable maida jakan bayanta tayi ta goya tace bari naje to sai gobe Gyadamata Kai Maimoon tayi suka fito tana kaiwa titi tashiga keke, is just around 10 yanzu gwara ta tafi hotel tamusu aiki saita sami free evening har gaban hotel din aka kaita ta sauka tabiya kudi tashiga ciki, direct changing room nasu taje, saida tafara chanza kaya sannan tadan fito ganin kowa na aikinshi yan morning sun riga sunzo tun dazu so kafin wani yadawo dakin nan cikinsu kuma probably sai idan yan afternoon sunzo kuma, hakan yasa tadawo ta maida kofan tarufe batare data saka sakata ba takoma ta zauna taciro rice daga bag da water dakuma maganinta ta ijiye kan long bench dake wajen itama ta sauna ahankali sannan ta dauki abincin tabude tasa spoon tafara ci ahankali bayamata dadi ma abincin sabida zazzabi. Ahankali yake tafiya da shi da Munir dawasu ma aikata guda biyu dake biyedashi abaya, akwai some changes dayakeso ayi abinda ma yakawo shi hotel din kenan this morning, duk ya gama nuna musu saura changing room na ma aikatan shi corridor suka shigo suna biyeda shi yasa hannu yabude kofan yasakai ciki yana magana yace the lockers nakes Shiru yayi ganin yanda Rashida tawani yarda takeaway jellof rice din da ruwan yashiga tittila akasa ta tashi tsaye da sauri daidai su Munir zasu biyoshi su shigo ciki yace wait! Duk kallonshi sukayi suna tsaye bakin kofan batare da sun shigo ba strictly yace kuje lobby yanayinshi kawai yasa Munir yace okay yajuya ma aikatan ma suka bishi yajuyo yazuba mata ido tana kallonshi cikeda fada baki tabude zatai magana dan akwai abinci abakinta sai kawai tai wani wawan kwarewa sai tari, maida kofan
Chapter 31 · 0% Book details