← Book details Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 71

Sashe 3

Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Dasauri Munir yace Gwaggo nima bansani ba but kaman he was attacked ne, yana kokarin fadamin wai ana kokarin kasheshi ya sume ba wayanshi taredashi, shi babu akwati, akusa dashi, awajen bola naganshi da bag pack yana mota dawani dan kwali black, kafin yafadamin komi kuma yasuma gam Mom tarike hannunshi har daki kan wani taskeken gado aka kwantar dashi Dr yashiga dubashi yanda skin nashi da fatanshi keyin wani bororo dahar wani motsi suke yasa yace a chanzamai kayan jikin nan nashi maza, ku goggogemai jiki with clean towel, allergy ke damunshi, he s allergic to dirt da kazanta right from small, kuyi sauri pls fita kowa yayi daga dakin akabar Munir da Mom, Waziri da sauran duk suka zauna a falo yace wazai attacking yaro daga durowan shi kasan nan? Anatse Wambai yace call the police I think sai anbincika airport din maybe ta CCTV za a gani faduwa gaban Kabeer yayi amman yadaure yaranshi always do a clean job he hope bazasu kwofasashi ba, fitowa Munir yayi yace Dr an gama dukansu komawa ciki sukayi Kabeer sai tsaki yake aranshi shida yakeso kowa yaji haushinshi amman jibi yanda kowa ke nan nan dashi, attention yakoma kanshi ma infact, skin nashi gabaki daya yakoma so red, drip akamai fixing da allurai ciki Dr yakalli Mom datafi kowa damuwa adakin yace anjima kadan zai farfado don t worry dan murmushi tayi tareda gyadamai kai Waziri yace ki zauna dashi Gwaggo tace nima ina nan kome za a kawomai kowa zaizo yadubashi saina ganshi inga uban waye keso ya cutar mini da jika, bangama kukan mutuwan d ana ba yanzu halakamin jika za ayi wlh jinina yasha karfin kowa kallon Munir Mom tayi ahankali tace thank you Munir gyadamata kai yayi yawuce yafita daga dakin hakan yarage daga Gwaggo sai ita, dafata Gwaggo tayi tace ki tsare yaron nan ki dage da addu a akanshi, tun ranan da aka haifi Riyad akace yanada taurari masu kyau kuma babban mutum ne shi, kiduba kigani yaran marigayi maza shidda amman shi kadai akeso ahalaka tun yanzu kenan bama asan waye zai gaji kujeran sarautan ba kenan amman so ake akasheshi balle kuma ace shine zai gaji sarautan ki tashi tsaye Maryama, saikin tashi tsaye, kinyi zaman gidan nan basai na fadamiki hadarorin dake cikinsa ba, inde kalubale ne yanzu Riyad yafara gani, idan kuma yazama Sarki yadinga ganin kalubale iri iri kenan har abada, ki tsare yaron nan, kizama idanunshi kunnuwanshi uwa uba kizama inuwarsa dakuma lullubinsa gyadama Gwaggo kai Mom tayi takama hannun Riyad tarike gam tana kallonshi tace Gwaggo meya musu Riyad dako zaman gidan nan baiso, na tabbata baimason ya gaji kujeran nan, dan bata gabanshi Gwaggo tace kwarai Mom tace shi kadai Allah yabani, shi kadai gareni, Riyad kadai Allah yabani yau ana kokarin rabani dashi kankame hannunshi tayi tace Gwaggo zan iya zuwa bangon duniya sabida Riyad! Kuma nayi alkawari duk Wanda yace zai cutar da yarona saidai yafara dani dan daga yanzu zan zama shamaki tsakanin Riyad da komi na duniyan nan, zan zama inuwa hazo zan lullubeshi nakuma kareshi daga duk wata hari sosai Gwaggo take kallonsu sai kawai tai murmushi tadauki charbi ta tacigaba da ja itama bini bini tana tofama yaron addu a aka. JOIN GROUP DANAKE POSTING NOVEL DIN NAN https://chat.whatsapp.com/CrKHphXCxK09RvYbrO1cCU SANYI DA ZAFI EPISODE 3
Chapter 3 · 0% Book details