← Book details Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 71

Sashe 29

Sanyi Da Zafi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

shigowa yayi yazo har wajen gadon yace Mama can you walk? Ko in dauko kujera ? Dan murmushi tayi tace haba zan iya tafiya Riyad saukowa tayi daga gadon ahankali tafara tafiya yana kaffa kaffa da ita dudda bawai riketa yayi ba Mama ta rame sosai kaman iska zai kadata tafadi sunyi tafiya sun fito cikeda kulawa yace zaki huta Mama? Wlh har cikin zuciyanta tajejin Riyad yanzu, he s caring and just too protective da sauri tace a bangajiba da karfina fa muje kagani murmushi yayi suka fito har wajen mota baya yabude mata dayake jeep ne sai alokacin ya taimaka mata ta shiga ta hanyar dan dukawa ya nuna mata shoulder shi yace dafani ki shiga kallon shaddan jikinshi kalkal Mama tayi saikuma ta kalli hannunta dudda bawai datti bane a hannunta amman saitace kai haba karna bata maka kaya ahankali yakai hannunshi yakama nata yadaura akan shouldershi yana rage tsayi yace Mama kibata duk albarkanki ne ahankali Mama tai murmushi kafin ta dafashi da kyau ta daga kafanta ta taka step din ta shiga motar yana kallonta yace are you comfortable Mama gyadamai kai tayi tace yes Riyad thank you daidai lokacin Rashida na shigowa hospital din tana cikin wani empty keke napep ta hangosu, azuciye ta sauko ta taho wajen daidai yajuyo, chak ya tsaya yayi folding hannunshi a kirji tundaga kan kafafunta yake kallo dake cikin wani bakin flat shoe daya gama mutuwa but dudda haka kafanta ya haska flat shoe din, zuwa skirt dake jikinta na atampa da pink hijabin data saka mai hula ya tasya mata a guiwa, tana zuwa ta tsaya agabanshi cikeda masifa tace bakai zaka kaimu gida ba nariga na kira keke wani banzan kallon raini yamata yace then saikije ki sallameshi yanda yamata maganan kaman ta kurma ihu mutumin nan dan bala in rainin wayo ne sabida yaga yanada kudi da hotel shine zai dinga ma mutane magana yanda yaga dama, wai ina ruwanshi dasu? Cikin fushi tace nace maka kafito mini da Mamana daga motan ka, wayasani ma ko dan yankan kaine kai tunda sai shegemana kake wani kallo yamata sai kawai yawuce yabude mazaunin direba ya shiga ya zauna itakuma ta shiga kiciniyan bude kofan back sit, da hannu Riyad yakira mai keken da sauri ya sauko yazo wajen yace gani yallabai kudi dayawa yazaro daga aljihu ya mikamai yace gashi kaje karba yayi yahau godiya Mama tai murmushi ciki ciki dan duk tana kallon draman tai kaman batasan sunayi ba making sick and tired face, danna glass na window tayi takalli Rashida dake tsaye tana kallon Riyad kaman zata iya fada dashi akace tayi, Mama tace shigo muje kina batama Riyad lokaci zaije aiki fa Rashida kallon Mama tayi har idanunta sunyi ja akufule tace kuje ni bazan shiga motan ba Mama na kallonta tace zan saba miki fa wlh, zoki shiga mota muwuce kallon Mama tayi bataso ta batama Mama rai yasa ta danne zuciyanta da kyar ta zagayo harta bude kofan baya Mama tace tunda ga direba kin samu ko dole ki shigo baya wani sweet smile Riyad yasaki ya gyara fuskanshi da sauri yana kallon waje kaman baisan anayi ba, kaman tayi ihu Rashida ta maida kofan tarufe takoma gaba tabude kofan ahankali tadan kalleshi ganin waje yake kallo abinshi yasa da kyar tashiga ta zauna ta jawo kofan tarufe tana harare harare, murmushi yayi yatada yajuyo yadan kallo Mama da tausassan murya yace Mama are you comfortable? Natada motan wani irin murmushin dadi Mama tasaki tace m comfortable d ana muje wani irin zafi Rashida taji aranta yanda Mama takira Riyad danta kawai saita ciro wayanta ta manna earpiece tasa a kunne, tada motan Riyad yayi suka tafi baya wani gudu sosai, Mama sai hira takemai kaman tasanshi hakan yakara tunzura Rashida dudda batajin mesuke fadi but tana ganin bakin Mama na motsi, har anguwansu hira suke sai kallon motan ake a kofar gidansu yayi parking ya bude kofa ya sauko yabude baya Mama ta sauko ahankali yabude booth ya kwaso bags nasu Mama tace key na bakin jakan takai hannu tasa blavk jakan aljihun taciromai tabashi yana sane yasan bata iya bude kofan motanshi ba ya shareta shiga da Mama ciki yayi sai kallon gidansu yake koina a gyare tsaf zaunawa Mama tayi yace bari naje Mama Allah kara sauki Mama tace nagode nagode Allah maka Albarka, wai ina Rashida ne hala ta wuce wani waje baice komiba yawuce Mama tabishi dagodiya dayake motan tinted ne baya iya ganota but yaga yanda motan ke motsin ana bubbugata yayi kaman bai saniba yawuce yabude kofa yashiga ya zauna batare daya kalleta ba yace wat are you still doing in my car ? Akufule tace inba dole ba mema zai kawoni cikin your so called car ? Still yaki kallonta yace get out! Kaman yana magana dawata dabba kirjinta tafarfasa yake tace ka budemin kaga idan nakara wani numfashi a motan naka dan kallonta yayi strictly yace who are you to make Riyad work for you ? Mamaki ne yakashe Rashida irin what exactly guy din nan thinks of himself ne, tadai daure ta danne zuciyanta da kyar tace to ai ban iya bude kofan bane ni dan juyowa yayi yayi facing nata yace then learn to soften muryanki and ask for help politely miss ido cikin ido take kallonshi ya zubamata mayun idanunshi dayasa kawai taji jikinta namata wani iri, duk yanda taso ta daure tacigaba da kallonshi itama saita kasa tadauke idanunta dan kasa jure kwayar idanunshi tayi, ta hadiye wani abu da kyar dataji yaa tsayamata a wuya tadan runtse idanu kai kasan she s about to say komene zatace ne out of compulsion tace kadan budemin kofan motan nafita sosai yake kallonta sabida yanda kawai yaji muryanta pierce his heart, this is the first time tunda ya santa takemai magana softly but da gangan dan ya kureta yakaita bango yace soften your voice more and add please cus no one command Riyad! Da sauri ta kalleshi wani kallo yamata na idan baki fadi ba zanja motata nayi gaba abuna, kaman tayi ihu takeji shine namiji na farko so far so good tunda ta girman nan ya iya tankwarata yakuma juyata haka, batasan mesa ba batakaimai duka ko kokawa ba the normal ita datuni takaimai duka suyi dambe but shi takasa, agogon hannunshi yakala kirar TAG Heuer yace you have 5secs left ko i will go wherever zani u will be here is none of my business yayi maganan yana kunna motan ma abinshi, wani ijiyan zuciya ta sauke ta sauke muryanta kasa kaman ba ita ba sounding like a Baby tace kadan budemin kofan motan dan juyo da kanshi yayi ya kalleta muryanta is the best muryan mace daya tabaji in his entire life, yanda yake mata wani irin kallon yasa ahankali kaman ba itaba lips nata na rawa rawa tace .lease ..please! sannan ta dauke kai da sauri kaman tai abin kunya din nan, sabida son yakaita bango gabaki daya shikuma annoyingly and authoritatively yace good gurl! kaman wata damusa ta kalleshi for the first time Riyad yasakin mata wani kalan murmushi dayasa taji zuciyabta yabuga rasss! Yana beating dum! Dum! Dum!! Da sauri ta dauke kai trying to control yanda zuciyanta ke beating takasa, dan tasowa yayi daga sit din dayake ta gefen ido taga ya nufota da sauri ta juyo da kanta ta kalleshi dan kaman zai hugging nata, hada ido sukayi gashi yaki daina kallonta kaman akwai wani abu dayake son gani game da ita sai kawai lips dinta yahau rawa tawani koma baya da sauri ta manne jikin kujeran kaman zata nitse ciki har hannunta rawa yake barin yanda kamshin turarenshi ke shiga hancinta jinshi dab da ita infact yadin kayan jikinshi ke tabata ta she was scared, lost, shaking, it was just a freaking reaction jikinta keyi dabatasan na me ba, he could feel heartbeat dinta, he could clearly see kwayan idanunta, this whole fadan nata is just an act! A mask! Hannunshi yakai ahankali kaman baiso yabude kofan still looking at her ya bude kofan tareda komawa seat nashi ya zauna bude idanunta tayi da sauri he was expecting tamai rashin kunya but saiyaga duk ta dimauce ta sauka da sauri kawai ta maida kofan tawuce ta shiga gidansu da sauri sai kawai ya girgiza kai yatada motan yawuce yabar anguwan. SANYI DA ZAFI
Chapter 29 · 0% Book details