Sashe 9
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ba, haka kuma in Kika fasa fadawa Salees ba ki haifu ba, maza fa a masa yazo yayi wa khadeeja tuf ta mutu kin ji, shashasha mara tunani, a fa a miki yarki tayi wannan rashin mutuncin amma ki goyi bayan ta saboda rashin sanin ciwon kai, to ai karki fasa, dan yau dai ba ayi masa haka in zaki gyara ki gyara". "Naki na gyara, nace naki na gyara in, yar ki ko yawa, aikin banza da zaki zo kina wani kinibibi ai se ki bari se kin haifa se karki goyi bayan naki, ko da yake macen da ta shekara sha shida da aure bata ta a ko bari ba ta ina zata haihu, wai wanda be san ciwon da bane zece ga yadda za'a masa tarbiyya, mtsww juya kawai mara amfani". Wannan kalma ta juya itace kalma mafi ciwo a duk cikin kalaman Mariya, sanin babban weakness dina gorin rashin haihuwa ne yasa Mariya daura damarar cewa se ta ga karshe na, gashi ni kuma bana iya daurewa wannan gorin, ko nayi kokarin haka se fuska ta ta bayyana halin da nake ciki, idanuna da suka yi jajir na kalli mariya dasu se kuma na juya na shige aki da sauri ita kuma ta raka bayan da harara. Cikin son karfafawa kaina gwiwa na dinga tausar kai na dan na gaji da kukan da nake yiwa mariya, na gaji da bata hawayena kan ta, na gaji da komai ma na ta. Haka na wuni a daki saboda bana san fita balle shaidan ya raya min wani abu na biye mata balle kuma azo ace laifi na ne kamar yadda ake ora alhakin komai dake faruwa a kaina, saboda ita in kirsasshiyar mace ce da gane halinta na gaskiya se wanda Allah ya ciyar kamar dai iri na da zama ya ha a ni kishi da ita na zama victim. Washegari ban taya jiran wata Ilham ba na tafiya ta aiki, ko da na gama na dawo a nan na tadda me gidan ya dawo dan ina shiga falon idanun mu suka sar e cikin na juna, wani kallo me zafi na watsa masa cike da jin haushin sa, tun da mutumin nan ya tafi be kira ni ba balle text, ni nakira shi ya turo min kalmar "busy", daga ita kuma be kuma cewa komai ba haka kuma be neme ni ba, wanda in rayuwa da adalci kamata yayi ko da ace busy din ne in yayi free ya Kira ni yaji ya nake, ya bani ha urin tafiya batare da ya sanar dani ba tun da ina da hakki amma duk be yi haka ba se dawo wa nayi na tadda shi a dararraje cikin iyalin sa suna hira cikin farin ciki da alamar rayuwa ta gama yi musu da Ko da nayi sallama ban lura da sun amsa ko ba su amsa ba nasa kai ciki, kamar in wuce batare da na kula shi ba se kuma zuciya ta tuna min da zaman kishiya a tsakanin mu wato Mariya, haka na daure cikin son nuna babu wata matsala tsakanin mu na tafi gare shi da niyyar yi masa side hug amma se ya goce yana watsa min zazzafar harara lamarin da yasa na an yi turus cike da kunyar yarfa nin da yayi a gaban kishiya "Daga ina kike?". "Wajen aiki". Na bashi amsa a sanyaye idanuna na cika da hawaye "Me ya hana ki kai baby school?". an jim nayi kafin na bu e baki "Bata shirya ba ni kuma zan makara". "A'a Khadijah kiji tsoron Allah gwara ki fa a masa gaskiya kawai, wallahi dear tun seven na safe baby take a shirye, dalilin ta na kin kai baby kawai dan tayi abu ba daidai ba na yi magana ne. Wai baby ce tayi mata rashin kunya shine ta mari bakin ta da kuncin ta tare da murde mata kunne, to ganin yadda ta dawo da zazza i a jikin ta fuska a kumbure yasa na yi mata magana, daga cewa ta dinga sassauta hukunci shikenan take fushi da mu a gidan nan, ko magana bata kuma yi min ba tun jiya har yau da ta fita shine kuma dalilin barin Ilham, dan Allah ka bata hakuri, Khadijah kiyi ha uri ni ba da wani abu na fa a ba". Irin yadda take tsara labarin abin da be faru ba tare da cakudawa da burbushin gaskiya yasa kawai na zuba mata ido na ma kasa magana, shi kuwa Salees batare da binciken gaskiya ne ko karya bane ya hau kai ya zauna ya dinga surfan bala'i, yi yake kamar bazai daina ba, nikam da na gaji kawai na wuce su na shige aki na kama kuka dan na kasa daurewa. Wai ashe laifi nayi da na tafi na bar shi a wajen, bawan Allahn nan be yi duba ga halin da nake ciki ba, be min adalcin jin ta baki na ba, be tausaya wa addara ta ba ya kira Hajiya Iya ya shiga fa a mata karya da gaskiya. Kiran wayar Hajiya Iyan ne ya katse min kuka na inda tace tana jira na gobe a gida, da toh kawai na amsa na kashe wayar raina a bace, zuciya ta cike da kunci dan nasan a can in ma ba za'a saurare ni ba, ba za'a bani dama ba, za'a yanke min hukuncin da aka so ne kawai bisa doron son zuciya, nikam ina ganin addarar rayuwa.............!. Ouummey Ouummey 04 {4/30/2023 }