Sashe 15
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ba?". Da sauri Farida ta shiga girgiza kai, "Ba zaki lalata kiyamar ki ba, ramuwar gayya zaki yi wadda tafi gayya zafi, daga lokacin da kika rama zaki ji sanyi a ranki daga nan kuma se mu tuba, amma ai kafin nan itama taji ko da rabin yadda kika ji ne". "Bazan iya ba Farida, ba zan iya lalata dan kowa ba, ba zan iya sanya mahaifiya kuka ba, ba zan iya fuskantar Ubangiji da laifin shirka ba, na hakura Farida, na barwa Allah shine ze min sakayya kan Alh da Hauwa amma ba zan iya kauce hanya saboda ita ba". "Banza tursasaki ba Falmata, ban kawo wannan shawarar dan batar dake ba sai dan sama miki salama amma tun da baki yarda ba ba za'a yi komai ba, sai dai kiyi hakuri domin zan janye jiki daga gidan ki dan ba zan iya zuwa ina ganin ki kullum kina ramewa da karewa a tsaye saboda bakin cikin wasu ba bayan kina da yadda zakiyi, zuciya ta ba zata iya hakurin ganin ki cikin matsala ba alhalin kece yar uwa mafi kusanci da ni, kiyi hakuri ba wai na janye gaba daya bane sai dai yawan zuwa zan rage, sai an jima zan kira ki in na koma gida". Da haka Hajiya Farida ta dauki jakar ta bayan ta yafa gyalen ta ta fara daga falon, babban compound ne da ya lashe motoci kusan sha biyar wanda daga nan zaka san gidan ba karamin girma gare shi ba, gate ta nufa tana tafe kama zatai bindiga saboda haushi da takaicin yar uwar ta, sanyin ta yayi wa, zuciyar ta ta fiye kyau da yawa haka hakurin ta ya wuce ka'ida. Ta dade da sanin da ita ke rayuwa a gidan matsayin kishiyar Hauwa to wallahi da tuni labari ya dade da suyawa dan ba zata dauki ko rabin rabin abinda yar uwar ta ta dauka ba, da ita ce da tuni ta takawa Hauwa birki dan ai rashin Haihuwa ai ba hauka bane da zata dinga wani iskanci, kai da ita ce da ta nunawa Hauwa itama Shegiya ce dan wallahi yadda take mata iskanci kan haihuwa ita kuma se ta lalata rayuwar yaran ta ga karshen tutiya da tinkaho, abinda take so Falmata ta goya mata baya suyi kenan amma tsarkin zuciyar ta ya hana ta hango me ita take ganowa. Tana zuwa gidan ta tayi parking tare da shiga falon ta me bala'in kyau, abu na farko da ta fara yi bayan zama shine kiran Falmata taji yaya take, Allah shaida ne tana matukar san Falmata, ta dauke ta yar uwar da suka fito kamar ciki daya ne shiyasa duk abinda ke faruwa a rayuwar falmatan yake matukar damun ta. Hankalin ta be kwanta ba se da taji lafiyar ta kalau kafin tayi shiru cikin zurfin tunani se kuma ta gyada kai cikin yarda da shawarar da ta yanke. Tana nan zaune yan matan yaranta biyu suka shigo daga islamiyya, hassana d hussaina. Har kasa suka gaishe ta tare da mata sannu da zuwa ta amsa kana suka wuce dakin su suka canjo kaya "Yaya jikin momyn?" Hassana ta tanbaya a kagauce, sanin yadda hassana ke bala'in son Falmata yasa Farida boye mata halin da take ciki "Ta sami sauki sai dai zamuje India a sake duba ta, yanzu dai kuje ku dora girki sannan ki kira yayanku kice ina neman sa". "Da toh". Husaina ta amsa kana suka shiga kitchen yin girki. D daddare kuwa se ga dan ta Safwan kamar yazo kamar yadda Hussaina ta fada masa tana kiran sa, bayan sun gama gaisawa d a tambayar yaran sa da matar sa ta kawo masa batun da yasa ta kira shi. Albarka tayi ta sa masa bayan ya amsa wa kudirin ta kana ta sallame shi ya tafi bayan ta bashi tsarabar yaran tace ya kai musu.............. Ouummey Ouummey 06 {5/3/2023 }