Sashe 5
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wattpad @ouummey *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter two_ Haka na kwana cike da kunci da acin rai, kwata kwata dama ban sa ran Salees ya biyo ni wani rarrashi ba dan nasan ba yi zeyi ba, so da yawa na kan yi mamaki yadda tashi aya rayuwar aure na ta juye daga happy married life cike da so da kauna zuwa wani yanayi da ba zan iya fa a ba. Sai dai ba abin mamaki bane in akayi duba da irin nakasun da mutane ke gani tattare da ni, ba wai tawayar halitta ba, bana hali ba face na wani arziki da Allah ke bawa bayin sa da yaso ba dan kuma dan ya tsane mu mu da be bawa ba, a'a sai dai dan ya jarraba karfin imanin mu, wanda in ba ya shiga cikin lamarin ire ire na ba cin wannan jarrabawar tana yin wuya domin abun ba sauki, lamarin babu dadi sam haka yanayin me matukar ta a zuciya ne. Da safe ko da na tashi ban fasa yin abin kari ba sanin nike da girki, sharp sharp na hada breakfast tare da zubewa kan table kana na ora na Ilham da zata tafi dashi school sannan na koma aki dan shirya wa zuwa wajen aiki, a hanzarce nake komai dan na makara saboda rashin samun bacci da wuri sanadin acin ran Salees da mariya. Sai da na tabbatar da zaman gyalen jiki na sannan na fesa turare kasa asa wanda ba'a jin amshin sa se an matse min waje sosai sannan na fito, kan table na tadda su zaune cikin farin ciki suna hira abin su, da ka gan su kaga wasu ma'aurata da rayuwa kewa dadi sabanin ni da rayuwar aure na ke cike da bakin ciki, acin rai tare da takaicin da namiji iri iri. Kau da damuwa ta nayi na shanye ta cikin ciki na na karasa tare da jan kujera na zauna "Good morning zuma na, fatan ka tashi cikin koshin lafiya". Na fa a ina kissing lips din sa kana goshin sa sannan na juya ga mariya "Barka da safiya maman Ilham, fatan kun tashi lafiya". Duk da naga sanda yanayin ta ya canja lokacin da na sumbaci Salees amma tuni ta ture tare da maye gurbin matsewar fuskar ta da wadataccen murmushi tana amsa min har da yar dariyar ta "Lafiya lau Auntyn yara, fatan kema haka". "Alhamdulillah kam". "Ehm nace dan Allah kiyi ha uri da abinda ya faru jiya, sha'ani na yara ne me sa mutum ya rude amma ba da wata manufa nake kawo Amir ba, kin san al'amarin raino in ba wanda ya ta a yi ko yake cikin yi wani abin ba yarda zaka yi in an fada ba, ni kaina da Umma ke fa a min akwai yara masu kukan dare ban yarda ba seda na haihu, amma karki damu kema soon zaki fahimta in Kika haifa". Duk wannan surutun da take yi ni tuni nayi nisa da zuba abincin da zan karya dan Ina zama na zubawa Salees, ban ago ba duk da naji me tace ban kuma yi mamakin maganar da ta fa min a wayance ba dan indai ita ce nasan zata yi fiye da haka dan tuni na dade da gane da kuma fahimtar inda ta dosa. Wahalallen murmushi na kakaro na orawa fuska ta na ago ina duban ta "Haba ai ba wani abu bane maman Ilham karki damu". Haka muka fara cin abinci tana ta zungurin Salees da hirar Amir da ta Ilham shi kuma ya biye mata dan a bayyane yake yana mugun son an sa tare da kulawa da duk abinda ya shafe su, gane hakan ne kuma yasa mariya ta samu damar kuntata min kamar yadda ta dauri niyyar yi tun haihuwar Ilham zuwa yanzu kan Amir. Tissue nasa na goge baki na ina mi ewa daidai fitowar Ilham daga dakin mamanta goye da skul bag in ta na tafiya makaranta, tun da yarinyar ta fito na kalle ta na kau da kai batare da na sake duban ta ba duk kuwa da yadda nake son yin hakan. Allah ya sani ina matu ar kaunar Ilham saboda yadda ta dauko kamaninn Salees kamar yayi kaki, yanayin ta na surutu da sakewa yasa take da farin jinin jama'a ciki kuwa har da ni sedai dole nake koyar dannewa tun wani incident da ya ta a faruwa. "Good morning Daddy, good morning Mommy". Ilham ta gaida iyayen ta batare da ni ta kalle ni ba, ban damu da hakan ba na sake daidaita zaman mayafi na tare da aukan handbag dina na kalli Salees "Ni na tafi se na dawo". "No ki tsaya ki sauke baby a school yau ba zan fita da wuri ba". Ya katse ni da sauri daga nufar falo da nayi, dole na ja na tsaya cike da damuwa dan na makara na kuma san se na kara wata a kan wadda nayi saboda sanin halin Ilham wanda uwar ta ta gama poisoning mind din ta a Kai na "Yi sauri kiyi breakfast ku tafi baby, yau Aunty ce zata kaiki". "To Daddy". Tace tare da zama ta shiga tsakuran abincin gaban ta kamar ba zata ci ba, ni kam daga tsayen da nake mamakin Salees ne ya cika min rai ganin yadda be damu da rashin gaishe ni da Ilham tayi ba, na jijjiga kai kawai tare da kallon wristwatch dina me tsada dake daure kan tsintsiyar hannu na kana na maida kan Ilham da se lokacin take yin spoon na uku a abincin. "Eat fast pls Baby, am already late". Ba wanda ya tanka min cikin su ukun haka kuma ba ta fasa cin abincin yadda ta ga dama ba, nikam tuni raina ya aci dan nasan da hujja take yi dan ta bata min lokaci saboda i overheard them once tana fada wa uwar bata san tafiya dani saboda ni nake kai ta wataran kamar dai irin yau in baze fita da wuri ba, budar bakin uwar ta bata shawarar dinga bata lokaci in tare zamu tafi, a cewar ta har na gaji na tafiya ta kafin ta gama shininnikin ta. "Ina ganin zan wuce fa Abban Ilham dan na makara tuni gashi kuma naga ita bata gama ba". Ban jira amincewar sa ba bare umarnin tafiya na shiga takawa zuwa waje dan da kyar ma na lallashi kaina na yi maganar dan kar yaga laifi na sedai ashe ban tsira ba "Wai meke damun ki ne a kwanakin nan Khadijah, ina fa lure dake duk sanda nace ki sauke baby a school se kin kawo uzuri, makara, ba zaki fita da wuri ba and many more, me kike nufi ne?". Seda na lumshe ido jin wata sabuwar fitinar kuma da sanyin safiya kafin silently na juyo Ina tausar Kai na "Babu abinda nake nufi fa Abban Amir, kalli agogo it's already past eight kasan Kuma ka'idan aikina thirty minutes past seven ne na makara". "Ba matsala, zaki iya tafiya zan kai ta da kaina Allah yasa uban ta na da motar". an jim nayi kamar na tafi sai dai zuciyar neman zaman lafiya ta rinjayi me tunzura ni se kawai na koma cikin falon na zauna tare da rufe ido, daga haka nake jiyo maganar Mariya murya kwance cike da tsantsar kissa da yaudara "Haba baban yara, me ye na fusata haka, ai kaga tana da uzuri me arfi, ko rannan ma ta tafi ta bar baby ne saboda tana da meeting, se kana mata hakuri fa, kasan bata saba da hidimar yara ba". Abin dariya wai Salees se ya dubi mariya "Abin da Khadijah ke min a gidan nan ya fara isa ta, amma ba komai ta cigaba". Se kawai fuuu yayi sama, "Dan Allah Auntyn yara ki dinga kiyaye abinda ze sa Abban Amir ya dinga miki fa a haka, wallahi bana jin dadi". Ban iya cewa komai ba saboda kullutun da ya tare min makogaro, da na bu e baki nasan ba me da i zan fadawa Mariya ba wanda da nayi hakan nasan wani tashin hankalin ze Kuma zama so se kawai na zabi yin shiru, ina jin ta tashi ta bi mijin ta sama ta bar ni nan zaune na kasa motsi cike da acin ran da ta jagoranci zama silar sa, seda siririyar muryar Ilham yet cike da rashin kunya ta ratsa kunne na "Ni kin ga Malama in baki shirya tafiya ba ki bari in fa awa uba na ya kai ni, atoh tun da ina da iyayen da suka haife ni su ba juya bane". Wal haka na ware idanuna na sauke kan fuskar yarinyar me cike da kuruciya hadi da yarin ta da a lokacin take shekara na sha uku, fuskar nan irin ta mahaifin ta a yamutse ta turo baki gaba cike da tsiwa yayinda madaidaitan idanun ta ke wulkitawa da hararar da take min. Cike da wani kudiri a raina na mike tare da fita daga falon ina dan karkada mukullin mota na har na karasa tare da budewa, farar mota ce me kyau tasha wanki tana ta yalli, da addu'a na bude mazauni na na shiga tare da rufewa kana nayi unlocking sabida ta shiga dan ina hango ta biye da bayana, murmushi nayi jin shigar ta bayan motar wato ta mai da ni driver Kamar yadda ta saba in tafiya ta ha a mu tun da ta fara wayo. Sai da muka hau titi sosai bayan na bawa me gadi ihsanin da na saba na cigaba da tuki na cike da nutsuwa, ba wata tafiye me nisa muka yi ba dan bamu gama fita daga unguwar ba na