Sashe 6
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
tsayar da mota tare da bude murfin na fita, door in da Ilham ke zaune na bude tare da finciko ta a fusace har seda ta tsorata, na bude gaba na sakata bayan na watsa mata wani shegen kallo me cike da gargadi hakan yasa bata yi yunkurin komawa bayan ba har na shiga mazauni na. Kyakkyawan mari me kyau nayi wa bakin ta da ya gama zuba min rashin kunya ta yadda seda ta sa ihu tana rike bakin ga ba halin guduwa na rufe motar, kunnen ta na kama na ri e da kyau ta yadda na san gargadi na ze shige ta na fiddo kyawawan ido na waje na haske ta dasu ina zare su "Duk sanda kika kuma yi min rashin kunya, kallon banza ko harara se na ci uban ki tun da baki da kirki, kina zuwa school kina haduwa da marasa tarbiyyan yara kina koya ko?". Da sauri ta girgiza kai jikin ta na rawa dan yadda na mata ba aramin tsorata tayi ba ga bakin ta dake zafi dan har lips din sun fashe "Ni ba sa'ar ki bace balle ki kawo min iskanci, duk rashin mutuncin da ke kan ki se na sauke miki shi dan duk kika kuma min aya daga abin da na fa a se na kulle ki a daki na zane ki ciki da bai ko kuwa in wullo ki daga sama ki fado ki mutu kowa ya huta, zaki kara?". Yanzu ma da sauri ta girgiza kai na kuwa sake ha e rai tare da zare mata ido "Baki da bakin magana ne kike min knodding?". Yadda nayi maganan a tsawace yasa bakin ta na rawa ta furta "A'a...a'a...ba zan kuma ba...". A firgice, haka na mata warning me kyau kafin na sake ta bayan nasa ta gyara kan ta na tashi mota muka cigaba da tafiya ina bin karatun Alkur'ani da nasa suratul Noor cikin raina kuwa cike fal da tunanin yadda zamu kaya da boss dina wajen aiki saboda nayi makara fiye da ka'ida a tsukin. Har cikin school premises din na kai ta tare da kara mata kudin break ta karba tare da barin wajen da sauri, na bi bayan ta da kallo ina tariyo tsoro na da na hango cikin idan ta sannan na fita, se kuma tunanin yadda zamu kwashe da Salees in ta fa a masa ya fado min, dogon tsaki na ja ina jin na shiryawa duk ma me ze faru, abu aya na sani ba zan dau raini daga uwar ya in Kuma na dau yarinyar ba, yar da da na sami haihuwa da tuni ina da sama da ita sosai, kai baze sabu ba wannan karon nima na shiryawa duk abinda Salees ya taka. Da wannan tunanin na karasa wajen aiki na inda nake aiki da ma'aikatar haraji wato revenue nake kuma da office na bakwai mafi girma a wajen, sai da na kai uzurin rashin lafiya wa me gidana kan na koma office ina Ina istigfar na karyar da Salees yasa nayi. Aikina nayi cikin nutsuwa duk da sa'i da lokaci wasu abubuwan na daga rayuwa ta kan fado min cikin rai sai dai bana bari ya zauna balle ya hana ni aiki na ke ture shi gefe. Waya ta ce ta dauki soft ringtone me da i wanda na sawa duk family na, ina dubawa na ga Ummi na ce, take naji wani sanyi ya shiga sauka cikin raina na dau call din cike da farin cikin jin muryar mahaifiya ta "Ummii naa" "Dijeehh naaah". Itama ta amsa min cike da so da kauna ta wanda suka fallasa kan su sanadin rashin haihuwa da Allah ya jarrabe ni dashi "I miss You Ummi naa, hope kina lafiya ba abinda ke damar min mamana". Sai da tayi yar dariya sannan ta amsa min "Ina lafiya Khadijah, ina fatan kema haka kuma babu wani matsala ko?". "Alhamdulillah, Allah ya kara muku lafiya ke da Abba na, matsala kam babu Ummi sai dai duk da haka muna bukatar addu'ar ku". "Wannan kam a kullum ba'a fashi Khadijah, kullum addu'a ta da fatana shine Allah ya azurta ki da rabo me albarka, Allah ya kare min ku ya tsare ku daga dukkan wani sharri ya albarkace ku ya kuma hada min kan ku". "Amin Ummi na, Allah ya saka da alkhairi ya kara girma tare da nisan kwana me albarka". "Amin, ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da rayuwar ki cike da tawakkali tare da godiya ga Allah, har kullum ina fa a miki be manta dake ba ba kuma baya son ki bane ya jarrabe ki, ki rike addu'a ki tsarkake zuciyar ki ki kuma zauna da abokiyar zaman ki Lafiya, dan Allah Khadijah kar ki bari she an ya zuga ki a kan an ta ko ita, in da kara da mutuntaka ya'yan mijin ki naki ne, ki gyara musu ina suka kuskure amma ban da cutar wa dan Allah". Wani irin rauni ne ya lullu e ni kamar yadda ya kasance yana faruwa duk Ummi take min nasiha "Insha da Ummi na, ina iya kokari na ki cigaba da taya ni da addu'a, ina autan ki ne ban ji shi ba kwana biyu?". "Allah ya shige mana gaba, auta yana can ya fita neman maganar da ya saba, ai ni dai wannan da se Allah ya shirya min amma jin magana kam ba'a cewa komai". Da haka muka bar waccan maganar muka koma hirar mu har lokacin da muka yi sallama na aje wayar ina sauke numfashi.......................! Ouummey Ouummey 03 {4/29/2023 }