Sashe 36
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ta sannan ya amsa cike da walwala "Jikin naka yayi sauki ko Dada?". "Eh babyn Dada, Father baze mutu ya bar babies din sa ba har se ya aurar dasu gaba ki daya insha Allah". Dariya suka yi su duka ita da Ameerah suna rufe ido at the same time wai kunya, shima dariyan yayi kana ya dauki Miemie a jikin sa ya fita falo suma suka biyo bayan sa, a kan three sitter ya zauna tare da zaunar da Miemie kan laps din sa su kuma suka zauna each by his side. Cartoon me kau and educational ya kunna musu suka shiga kalla Ameerah da Miemie se hira suke akai, ganin hankalin su ya dauku yasa Rayhanah juyawa a hankali ta fuskanci Dada "Dadaaaaah". Ta kira shi cikin low tone dan kar tayi calling attention din su Meerah, ganin yadda ya zuba mata ido yana bata full attention din sa yasa ta karyar da kai gaban ta ba faduwa haka tana ta addu'a a ranta kan Allah yasa ya yarda da abinda zata fada "Pls Dada kayi aure". Ta fada tana sunkuyar da kai haka tan jin effect din piercing eyes din sa akan ta, kirjin ta na duka jin yayi shiru ta cigaba da magana da rawar murya "You're suffering Dada, kullum baka samun bacci, You're always having sleepless nights saboda mu, abubuwan sun maka yawa Dada, kai din namiji ne, ga matsalan office, ga na jama'a ga na namu ga kuma nasu Yaaya, Dada na damu da yawa, tun tasowa na nake ganin ka cikin kunci da damuwa, i want you to live a happy life Dada, fatana da buri na be wuce in dinga hango kwanciyar hankali, jin dadi da farin ciki a idanu da fuskan ka ba, pls dan Allah do me a favor in ga Dada na cikin yanayin da nake fata kafin Allah ya dauki raina kaji Dada". Tun da ta fara magana babu kalmar da ta doki ran sa kamar irin kafin Allah ya dauki ran ta, abu na zuciya kawai se ya dinga hango har gashi ance ta mutu, ga ta ance itama ta tafi kamar Maryam, se kawai ya shiga girgiza kai yayinda zuciyar sa ta dinga ayyana masa ze iya rasa yar sa mafi soyuwa a ran sa, ze birne rai mafi damuwa dashi "A'a, a'a, no Haanah, ba inda zaki je, a'a ba zaki mutu ba". Ganin yadda Dadan ya rikice yasa ta riko hannun sa tare da matsewa cikin nasa "Calm down Dada, nima ba zan so in mutu in barka ba, I'll not leave you Dada, not now not after, ka kwantar da hankalin ka kaji". Ajiyar zuciya ya sauke tare da rufe ido ya kwantar da kai kan makarin kujera se kuma ya bude ya zuba kan fuskar Haanah da ta cigaba da magana "Zaka yi aure Dada?, Zaka cika min buri na?". Da sauri ya hade rai "Kar na kuma jin maganar nan a bakin ki Rayhanah, ko ba yanzu ba, okay?". A sanyaye idanu cike da kwalla ta gyada masa kai zuciyar ta na karyewa dan ta san ba dan kowa Dadan yaki aure ba se dan su, yana tsoron ya auri wadda zata gallaza musu ko ta nemi raba shi da su "Insha Allah ba zan Kuma magana ba Dada, a koyaushe ni me bin umarnin ka ne, komai zan yi kai nake fara tunani kuma wannan ne dalilin da yasa na kawo batun aure dan nasan insha Allah in kayi dace da mace nagari zaka yi farin ciki a rayuwa, zaka sami nutsuwar da ka rasa tun zamanin kuruciya hak kuma zaka sami kwanciyar hankalin da baka taba tunani ba. Na sani saboda mune kake dodging maganar aure Dada saboda kana tunanin makomar mu in ba'a yi dace da tagari ba, sedai ya kamata akan komai mu zama positive, what if muka yi dace da tagari, kai ma da muma duk zamu sami jin dadi da walwala, and above all hankalin Yaaya ze kwanta, kayi tunani akan Yaaya, itama mahaifiya ce kamar yadda kake mahaifi, yadda kake kaunar mu haka Yaaya ke kaunan ka, yadda kake son ganin mu cikin farin ciki da walwala haka itama Yaaya ke son ganin ka, na sani ka san yanayin da take ji tun da kaima kana jin makamancin sa, shiyasa na kawo maganar da na san zata faranta maka da ita amma ba zan kuma ba insha Allah tun d baka so, am sorry for upsetting you Dada, am sorry pls forgive me". Gaba daya se yaji Haanah ta daure shi da jijiyoyin jikin sa, se yake ji kamar ta sa wata igiya me karfi ta zazzarge shi dasu, kawo batun Yaaya ya sanyaya gabban jikin sa gaba daya, eh ba karya tayi ba domin duk wanda ya kwana ya tashi a gaban Yaaya yasan babu abinda take fata da burin gani irin yayi aure a yanzu, ta sha zaunar dashi tayi masa nasiha, ko kuma tayi ta bashi labari mai cike da hannun ka mai sanda amma duk se ya nuna baigane ba, yanzu kuwa da ta alakanta abinda mahaifiyar sa take ji da wanda yake ji se ya gane radadin me girma ne, haka kuma akwai ciwo a zuciyar mahaifiyar sa dangane dashi "Na amince Haanah, amma not now, ban kuma ce a zaba min ba, a bar ni har zuwa lokacin da zan ga wadda ta kwanta min da kaina". A zabure ta ke kallon Dadan nata ido waje, "Da gaske Dada?, Da gaske ka yarda zaka yi aure?". Gyada mata kai tayi babu digon fara'a a fuskar sa, sedai ga mamakin sa hakan be sanyaya jikin Haanah ba balle har ya hana ta fara'a se ma wani karsashi da ya ga ta samu lokaci daya, karo na farko kenan da Rayhanah tayi farin ciki lokacin da shi yake cikin damuwa................ _*3 PAGES TO GO, FREE CHAPTERS A YET TO END*_. _*KAR KU MANTA LITTAFIN NAN NA KUDI NE KAMAR YADDA TUN FARKO NA FADA HAKA KUMA NAKE ADDING PREFIX DIN _FREE_ A HEADINGS DIN KOWANE PAGE, SO GA MASU BU ATA SHOULD HURRY UP AND START MAKING THEIR PAYMENTS DAN 15 PAGES NE FREE*_. ME BUKATA ZE IYA DM TA WNN NUMBER *09013101854* Ouummey Ouummey 13 {5/13/2023 }