Sashe 20
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wattpad @ouummey *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Seven_ Ban tsaya a falo ba na wuce garden din mu dake can bayan gidan, ba wani babban waje bane sedai gwargwado yayi kyau, kan elephant grass din wajen na kwanta abina ina sauri numfashi, kalaman Salees na sake dawo min cikin rai na, lallai Salees ma, yanzu shi after all that happened har yana da karfin halin nufin na da bukatar da, ko da yake ba abin mamaki bane. Amma fa ba karamin juriya da karfin hali nayi ba wajen ture kalaman sa daga raina haka kuma ba karamin kokari nayi ba wajen ganin be yi galaba a kai na ba, dan da gaske zuciya ta ta raunana, so da kaunar sa sun rufe ni. Ko yanzu ma da nake kwance tunanin rayuwar mu ta baya nake yi, haduwar mu, soyayyar da muka zuba zuwa rayuwar auren mu me cike da farin ciki kafin Mariya ta shigo cikin mu kuma komai ya canja. Ajiyar zuciya na sauke jin mutum a jiki na da na tabbatar Salees ne, nima dama ban yi zaton ya bar ni haka da wuri ba dan yana cikin maza masu naci kan abinda yake so, sedai na kudire ko yafi antaru taurin kai da naci wallahi baze sami komai daga gare ni ba. Da sauri na mirgina jin hannun sa ta cikin riga ta, tunkurkur na zauna tare da zuba masa idanu na da mayen son sa suka sa yayi ja lokaci guda ina bata rai matuka, cike da basarwa irin tasa ya nuna kamar be gani ba ya matso tare da son sake shige min sedai tuni nayi baya da sauri Ina turo baki "Bana son irin abinda kake min wallahi, baka na dawo nan bane, ya kamata ka gane hutawa nake son yi". Dan tsai yayi yana duba na da mamaki dan zan iya cewa ban taba yi masa gardama ga bukatar sa ba cikin rayuwar da muka yi ya tsawon shekaru goma sha shida, na san dole abin ya dake shi gashi kuma nayi fuska abina tare da komawa na kwanta na bashi baya. Sosai jikin Salees yayi sanyi sedai he's the type that doesn't give up easily so se ya Kuma matsowa tare da sa hannu ya juyo dani ta karfi, be kuma jira komai ba ya danne ni cikin son se ya hade bakin mu guri daya, aikuwa kamar me haka na shiga fighting din shi na kuma ki bashi duk damar da yake so, ya zata abin wasa ne ya shiga kokarin kashe min jiki sedai ya ga ko kadan ban da niyyar saduda asali ma na kara kai mi ne wajen kokawa dashi dole ya hakura ya daga ni tare da tsura min jajayen idanun sa da ke cike da neman magana ga kuma bacin ran da na tusa masa, yana daga ni na tashi ina gyara riga ta na mike tsaye tare da kakkabe jikina nayi hanyar barin garden din ina karkada masa jiki, ko banza na san shima na bata masa kamar yadda yake bata min. SALEES Duk yadda yake tunanin iskancin khadeejah ya wuce wajen, kalli yanzu abin da tayi masa kamar wani kwarto alhalin yana matsayin mijin ta shugaban ta, a yanzu kam dari bisa dari ya yarda raini ne tsagwaron sa tsakanin sa da Khadijah, ta raina shi ne take masa haka, ai da datake ganin girma da kimar sa musu wannan ze iya kirga so nawa ta masa, lallai se ya dau kwakkwaran mataki kan ta, ba dai jikin ta bane take masa wulakanci dan ya bukata?, To ta rike abin ta ta jika tasha dan alkawari ne baze kuma neman ta ba, in kuwa ta kawo kan ta lokacin zata san ita bata iya wulakanci ba dan se ya nuna mata shima tantiri ne kamar ta, yana ji da fiye da duk abinda take ji. Ya dade zaune a wajen kafin ya iya mikewa ya koma gida, fita ya so yi ko yaji sau in bacin ran sa sedai baze iya ba, a yadda marar sa ke damun sa cikin ma da kyar yake taka kafa. Ganin yadda ya wuce su rai bace fuska hade yasa Mariya tashi ta bi bayan sa da sauri, sedai ko kafin ta kai gare shi tuni ya shige tare da datse kofar, turus ta tsaya tana kallon kofar dan this is unlike him, bugawa ta shiga yi hankali tashe sedai duk iya bugun ta yayi mata banza ko uhm bece ba haka ne bude kofar ba har ta gaji ta juya jiki a mace ta sauka kasa. Shi kam Salees duk bugun da take yi yana ji kuma yana sane yayi mata banza, abinda bata sani ba dan ita ya rufe kofar dan ya san se ta zo takura masa shi kuma baya bukatar takurar ta dan ba abinda zata iya yi masa, khadeejah ce kawai maganin sa ita kuma ya fahimci hayaki kan ta keyi amma yayi al awarin sauke mata duk ma uban dake kan. Haka ya cigaba da juyi dafe da marar sa se uban gumi yake ha awa kafin wani wahalallen bacci yayi gaba dashi me cike da mafarkin Khadijah kala kala. Be tashi ba se after Six, a gurguje yayi wanka ya fita Masallaci jikin sa duk ba kwari, sallar ma ranar cikin wasi wasi yayi ta dan gaba daya hankalin sa na kan Khadijah, tunane tunane kawai yake yi a kan ya, wata zuciyar na fada masa ya sake gwada ta ko zai dace wata kuwa na bashi shawarar fita harkar ta har ta gane kuren ta, be bar masallacin ba se da yayi isha kana ya nufo gidan cike da karbar shawarar zuciyar shi ta sake bata dama. Fadawa nayi kan bed fuska ta cike da murmushi me fadi wanda na manta rabo na da irin shi, wato yau da naga Salees cikin irin yanayin da na kan shiga a dalilin da se naji raina yayi sanyi, sanyi fa sosai dan ba karya naji dadi wallahi. Juyi nayi tayi ni kadai ina sake shirya yadda zan cigaba da zama da kowa na gidan da halin sa, na daina daukar cin kashin kowa tun da ina hakuri amma ba'a san ina yi ba, da ace duk abinda ke faruwa Salees na bin bayana in Ina da gaskiya da maybe ban sare ba haka, amma babu ruwan sa dani, babu ruwan sa da zan damu ko zuba cutu, shi dai duk abinda aka tsara masa shi yake hawa, duk abinda aka fada masa a kaina se ya yadda, nayi ban yi ba duk ba ze bin cika ba, kamar ba shine a baya yake fada min ba wanda ya kai shi sani na ba, ba wanda ya kai shi sanin hali na, ba wanda ya kai shi sanin abin da zan aikata ko ba zan aikata ba, duk ya manta wannan, duk ya zubar da komai ya watsar da komai, baya kallo na a komai face Khadijah, matar da yake aure wadda bata haihu ba, ba'a ma maganar soyayya, dan yanzu ina tantama in akwai so na a ran sa, dan abinda yake min masoyin gaskiya baze yi shi ba. Kiran sallah ya sa na mike tare da shiga toilet na dauro alwala na tada sallah, ina idar wa na yi azkhars dina kana na cire hijab din na fita zuwa kitchen dan yunwa nake ji, noodles na dafa na zauna na ci acan kana na wanke plate din na aje na koma daki, system na jawo na shiga aiki na dan yanzu na sake maida hankali dan bana san abin d zesa suna na ya fita daga cikin masu samun promotion din nan, na saka rai sosai ina kuma fatan Allah ya sa na dace. Karfe tara na tattara komai na aje na shiga wanka, sleeping dress na saka kana na feshe jiki na da turarukana masu sanyin dadi wanda ko ba zan je dakin Salees ba bana fashin sa su, se da nayi addu'a sannan na kwanta bayan na kulle kofa ta. Har bacci ya fara dauka ta na ji kamar an bude dakin an shigo, a tsorace na mika hannu na kunna wuta dan switch din na daga saman kai na ne, a boye na sauke ajiyar zuciya ganin Salees sedai a fili se na bata fuska in bin shi da kallon mamaki da kuma gajiya da ganin sa, maida kofan yayi ya rufe tare da takowa ya zauna bakin gado yana kallo na nikuwa na kau da kai gefe ina bata rai. "Tashi zaune muyi magana". Kamar ba zan tashi ba se kuma na fara tashin a hankali kamar me ciwon laka wanda ina sane nayi dan na bata masa dan tuni na dade da sanin baya san jira a rayuwar sa, kusan minti biyu kafin na zauna sosai sannan na kai kai gefe. "Bana san tashin hankali Khadijah, ki fuskance ni mu sami fahimtar juna". Juyo da kaina nayi na zuba masa ido kamar yadda ya bukata, seda ya dan yi shiru alamun yana tunanin ta ina ze fara kafin ya riko hannaye na, na kalli hannun sannan na maida duba na kan sa "Bana san irin wannan zaman da muke yi Khadijah, ban taba tsara hakan tsakani na dake ba, in laifi nayi miki ki fada min na baki hakuri a wuce wajen amma bana san gaba da fushi". Shiru nayi kawai, lallai namiji bai da kunya, wai ni Salees ke tambaya in laifi yayi min saboda yanzu tashi ta kawo shi, duk abinda ke faruwa be ga ni ba, duk abinda yake min ba laifi bane, aikuwa ze ga rainin hankali in dai nice dan nq shirya masa