← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 48

Sashe 24

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ki ba, jiki na ne kawai yake fada min nayi laifi, dan Allah ki fada min kuskure na I promise to repent insha Allah". Shiru nayi cikin harhado laifukan Salees gare ni na shiga analysing wanne zan fada wanne zan bari dan wallahi ba zasu fadi duka ba saboda yawan su. Jin yadda yake hura min iska a kunne yasa a hankali na bude baki na "A kullum fatana da buri na be wuce karasa rayuwa ta da kai ba Salees, ban taba hasko rayuwa da wani da namijin ba bayan kai, kai na fara so kuma har yanzu kai nake so sedai abubuwa da yawa na dakatar dani a kan ka. Allah be bani haihuwa ba Salees, da siyar wa ake yi wallahi bana jin da ko shekara zan kai a gidan ka batare da da ba, da kwatowa ake yi shima ko da zan rasa raina zan fita nayi gwagwarmaya na kwato, haka kuma da soyayya ke bada haihuwa nasan da tun farkon auren mu ka bani, sedai Allah ne me badawa ga wanda yaso ya zaba ba kuma dan mu da ya hana baya san mu ba amma mutane basa fahimtar hakan, ba damuwa nayi da wasu se sun fahimta ba in har Kai da nake tare da kai ka fahimta, sedai abin da ke tayar min da hankali kai ma din kallon mara amfani kake min, kai ma din ka gaza fahimtar ba kasawa ta bace, so da yawa se in ga kamar jira na kake abu ya hada mu kayi min gorin rashin haihuwa, wannan shine babbar matsala ta a gidan nan se kuma na matar ka ya biyo baya, amma a kan ta ba zan ce maka komai ba dan duk abinda take yi Allah yana kallon ta kuma i do believe yasan yadda ze yi da ita". Shiru dakin ya dada yi na tsawon lokaci kafin Salees yayi breaking silence din "Am sorry for all my mistakes, am sorry na saki bacin ran da nayi times without number, am sorry for everything khadeejah, dan Allah kiyi hakuri and am ready to change, for good and for you khadeejah, ki fada min me kike so nayi wallahi i promise you zan yi". Abin mamaki kawai yake ban dan rabon da mu sami mutual agreement kamar haka wallahi ba zan ce ga yawan shekarun ba, abin da na rike kawai its too long, an dade sosai. "Ka ringa bincike kafin yanke hukunci, ka dinga sauraren both side kafin zaban me gaskiya, ba abinda nake bukata a wajen ka face adalci, kulawa da kuma tausaya wa, this is all I need from you Salees, dan Allah". Na hade hannaye na alamun roko hawaye na zuba a ido na, da sauri ya dora nasa kan nawa ya jimke kana cikin taushin murya ya amsa min "I promise you love, care and justice daga yanzu har zuwa ranar da numfashi ze bar gangar jiki na, insha Allah ba zan kuma yanke hukunci batare da bincike ba, insha Allah zan zama me adalci gare ku baki daya, ke kuma abu biyu nake so wajen ki dan Allah, uzuri da soyayyar ki, ina barar wannan abubuwna khadeejah". "And i promise you also". Ba muyi bacci ba seda muka cimma matsaya wa rayuwar mu, wannan daren ya shiga cikin tarihin rayuwa ta domin dai tun da muka shiga daki da shi tun dawowa ta karfe hudu da rabi Salees be sake fita ba se washegari dan hatta sallah tare muka dinga gabatarwa a daki. Tun daga wannan lokacin zance alhamdillah domin kuwa Salees ya tabbatar da alkawarin sa ko ince yana kan tabbatar wa dan haka har wata kiba nayi ta kwanciyar hankali da samun nutsuwar zuciya. FALMATA Yau ma zaune take a falon ta, sedai tun da gari ya waye take jin ta ba daidai ba, cikin ta wani irin ciwo yake mata da ya hanata zama guri daya, tun tana daurewa a daki har ta kasa ta janyo wayar ta ta shiga kiran me gidan, wayar na ringing amma ba'a dauka ba, azaba ta sa itama ta kasa daina kiran wanda a kalla ta masa miscall kusan ashirin amma no answer. Azabar ciwo da radadi yasa ta wurgar da wayar ta shiga malelekuwa kan carpet din kasan gadon, gaba daya ta fita hayyacin ta , a haka Allah ya jefo daya daga cikin masu aikin ta, cikin tashin hankali ta fice a guje dan zuwa sanar da mutan gidan halin da uwardakin ta ke ciki, sedai bata sami Alhaji ba dan baya gida, ita kuwa Hauwa da ta fada mata Allah ya sawwaka kawai tace ta dauke kai. Dole harira me aiki ta kuma kwasowa a guje ta dawo, ita ta zauna da ita sedai ta rasa me zata mata, cikin ikon Allah ta hango wayar Hajiya Falmata ta dauka hannun ta na rawa, dake tayi makaranta har zuwa secondary se ta lalubo number Hajiya Farida ta kira, shine fa ta zo, ashe maganin ta ne ya kare ga ba kudi hannun ta, dole Hajiya Farida ta tafi siyowa ita kuma harira ta taimaka wa uwardakin nata zuwa falo kafin Hajiya Faridan ta dawo.......................... Ouummey Ouummey 09 {5/7/2023 }
Chapter 24 · 0% Book details