← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 48

Sashe 32

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Eleven_ "Kaje Dada zan kula da ita, insha Allah ba zata yi rigima ba". Gyada mata kai yayi tare da pecking goshin ta ya juya ze cigaba da tafiya "Dada". Ta tsaida shi, da sauri ta karasa gare shi tare da shan gaban sa ta shiga bin shi da kallo "Baka yi bacci ba jiya ko?". Kau da kan sa yayi daga kan ta yana hadiye wani daci a ran sa jin yadda tayi magana da wani sassanyan sauti me cike da tausayawa "Dan Allah kar ka fita Dada, kaje ka sami bacci, i promise to look after Meerah and Meemah". Wani murmushin ya sake yi mata kana ya riko hannayen ta yana mata magana a hankali ransa cike da so da kaunar wannan yarinyar tasa me matukar nutsuwa, wayo, hankali da kuma fahimta "Bana tare da bacci Haanah, idanu na ne na tashi suna ciwo, take a look here". Ya fada yana zira hannu cikin aljihu ya fiddo da maganin ciwon ido, a hankali ta sauke ajiyar zuciya kana ta sake masa kyakkyawan murmushin da ya haska matashiyar fuskar ta me cike da kuruciya "Oh Dada, har hankali na ya tashi fa na zata bacci ne baka samu ba, shikenan a dawo lafiya Dada na". "Allah yasa Haanahn Dada, pls do take care of your little ones, I won't take long insha Allah ". Gyada masa kai tayi har lokacin murmushin ta na nan, da sauri yayi gaba jin wayar sa na daukan ringing, da kallo ta bi bayan baban nata me cike da tsananin tausayi hadi da kauna me yawa kafin ta juya zuwa cikin falo ta same hanyar da suka fito. A falo ta tadda Meemah da Meerah both decently dressed cikin islamiyya uniform din su, dage musu gira tayi while tana sake musu tattausan murmushi kana ta bude hannayen ta, da gudu suka karaso suka bata a huge sisterly hug ta sa hannu ta sake kai su jikin ta sosai, kusan minti biyu kafin ta sake su tana bin su da kallo inda tayi branching kan fuskar Meemah dake yatsuna fuska tana wani tura baki. Tun kafin ta kai ga tambayar ta meye Meemah ta fara magana cikin zazzakar muryar ta me cike da tsiwa "Kai gaskiya kadai ya Meerah baki iya hug ba, jibi yanda kika matse ni kamar zaki da kayan ciki na su fito ta baki na, da kyar fa nake numfashi, tabdi". Meerah da abinda Meemah ta fada ya kular tayi kan ta zata kai mata duka hakan yasa Haanah yin intervening da sauri "Me ye haka kuke yi?". "Jibi yadda take min rashin kunya Adda bayan ke da Dada kun hana ta". Wani kallo Haanah tayi wa Meemah da yasa ba shiri ta kalli Meerah "Koyi hakuri Adda Meerah ba zan sake ba amma kema ki daina matse ni gaskiya". Meerah zata sake magana Haanah ta daga mata hannu kana ta tashi tana pointing musu hanya "Oya let's have our breakfast, we're almost late". Ba musu suka yi gaba ta bi bayan su har kan dining din su dake sha e da kayan kari wanda a kalla mutum goma zasu ci a wadace, babban plate Haanah ta dauka ta zuba musu gaba daya chips din wajen ta aje musu gaban su ita da Meerah sannan ta ha awa kowa tea a cup, ita kuwa Meemah farfesun hanta ta sa mata a karamin bowl ta bata bread da Egg. A nutse suka karya cikin nutsuwa babu me yin magana har suka gama kowa ya zari tissue ya goge bakin sa da hannu kana suka wanke a wash hand basin dake dining area din. "Ku dauko jakan ku muje na san Lawan na can na jira". Da toh suka amsa mata suka yi yadda tace, a tare suka fita daga falon tayi locking din sa suka wuce parking space inda suka tadda Lawan na jiran su kamar yadda tayi zato, Meerah da Haanah suka shiga baya Meerah kuma gaba, har ya tada motar zasu fita ta wani zaro ido tana fadin "Lalalala, tabdi malam Lawan tsaya tsaya". Tsayar da motar yayi yana kallon ta haka ma su Adda Haanah jira suke suji tace tayi mantuwa se suka ji tana fadi "Ban yi wa Dada sallama ba Adda, bari in maza in je". Da sauri Haanah ta dakatar da ita da fadin "Ba kya ganin mun yi late ne, ki bari mu dawo dan Dadan ma baya nan, Malam Lawan muje ko". Turo baki tayi gaba ta gyara zaman ta dan dole dan yadda taga Addan ta hade rai ta san ba ta isa ta kawo wargi ba. Har bakin kofar class ya kai su Meemah da Meerah inda Haanah ta sauka a ajin su Meemah kasancewar ta malamar su shi kuma ya juya ya tafi. Karfe biyu suka tashi daga makarantar, Meerah tazo ajin su Meemah dan a nan suke haduwa su tafi bakin makarantar inda Lawan ke tsayawa, sedai ga mamakin su yau Lawan yayi late xan kuwa be zo daukan su ba. Zama suka yi suna yan hirar su tare da kallon yaran dake fitowa daga makarantar har suka ji horn din motar da yasa su juya wa dukan su a tare dan ko a mafar ki suna iya banbance sound din wannan horn din daga na kowace mota. "Wallahi Dada ne, Dada na ne yeeeeehhh". Meemah ta fada tana kokarin rugawa da gudu zuwa wajen motar dake parke gaban su kadan "Kar ki fara yi mana gudu a nan, ki jira muje tare me rawar kan kawai". Meerah ta fada tana hararar ta, tsayawar ta yi bisa dole sedai bakin nan a tale kamar wadda zata yaga shi, jira take kawai su shiga mota ta ha a Adda Meerah d Dada dan ta gaji da yadda take mata fada da abubuwa. Seat din gaba Haanah ta budewa Meerah ita kuma da Meemah suka shiga baya "How's the school babies". "Alhamdillah Dada". Suka fada a tare har Haanah da ta fara girma dan in a gaban Dadan ta ne jin ta take yi kamar wata yar baby. "Yauwa Dada, malamin mu yau ya fada mana ba kyau karya shiyasa zan fada maka abinda Adda Meerah tayi dazu". Da sauri Meerah ta zaro ido jin iya shegen da Meemah zata mata dan kawai ta hana ta gudu, "Kai Meemah kiji tsoron Allah ni kuwa me nayi da zaki fada in ba kalin sharri ba". Dariya Meemah tayi ganin yadda Addan tata ta firgita "Ki bari kawai na fadawa Dada da Adda Haanah kin sha ruwan sanyi immediately after you wake up". Rau rau da ido Meerah tayi tana kallon Haanah wadda itama ke kallon ta jin abinda tayi bayan likita ya hana ta kuma ta sani "Why, meyasa kike yin haka Ameerah?". Sharrr hawaye suka zubo mata dan suna bala'in tsoron baban su dan duk yadda yake wasa dasu yake son su baya hana ya hukunta mutum in yayi ba daidai ba "Am sorry Dada Allah ba zan kuma ba". Shiru yayi mata hakan yasa ta kara volume din kukan ta tana bashi hakuri "Will you pls keep shut, ko baki ga tuki yake ba?". Kamar an yi ruwa an dauke haka ta hadiye kukan ta bayan Haanah ta mata magana, ba wanda ya kuma magana se Meemah dake wasan ta ita kadai har suka kai gida, kowa ya dauki bag din sa suka yi falo. A tsakiyar falon ya tsaya ya zuba wa Meerah ido cikin hukuntata dasu wanda duk yayi musu irin haka suke gwammace wa yayi fada ko ma duka akan wannan silent punishment din. "Ciki na ne naji yana zafi Dada shine nasha amma ba zan kuma ba, am so sorry pls Dada". Kallon Haanah yayi se ta langwabar masa da kai alamun itama tana bashi hakuri, dauke kai yayi ya kalli me kawo gulmar Hajiya Meemah, wai dan gulma itama yarinyar nan se ta karyar da kai gefe wai itama hakurin take bashi, wannan dabi'a tasu na matukar burge shi tare da faranta masa rai. Gashi dai basu yi laifi ba Ameerah ce kadai tayi, amma yanzu da zai nemi hukuntata se duk hankalin su ya tashi ba kuma zasu koma daidai ba har se ya hakura kamar dai yanzu. Girgiza kai kawai yayi ya wuce bedroom din sa leaving them behind Wanda Haanah ta fahimci ya hakura ne dan haka ta ce "Se ki tashi ai babar marasa jin magana,ban da wulakanci so nawa kike so in nanata miki ki daina shan ruwan sanyi da safe after kin fi kowa samun you're not fine Amma shine bakya ji, to go ahead and kill yourself se mu zauna mu uku, kinga se mu dinga lissafin ke da Maamah bakwa tare da mu". Yadda muryar ta ta shiga rawa bayan ta kai karshen zancen ze tabbatar maka tana cike da kewa da alhinin wadda ta kira ga Maamah a ran ta, fashewa da kuka Meemah tayi tana kiran Maamah, ita wallahi Maamahn ta yasa hankalin su tashi. Shaf Haanah ta manta da cewa tan wajen ya sa ta ambaci sunan Maamahn ashe rabon ta jawo musu jidali ne . Fitowar Dada da sauri daga dakin yazo ya dauki Meemah tare da orawa a kafada ya shiga aikin lallashin ta, wannan yanayin ya karyawa Haanah zuciya ta shiga hawaye da shessheka abinda yasa itama Meerah fashewa da kuka. Gaba daya se ya rude ya rasa ya ze yi, waye ze lallasa ma ya rasa se kawai ya juya ya zuba musu idanun sa da suka kada sukai jajir, hada idon da suka yi da Haanah da yadda taga jan da idon sa yayi yasa ta san
Chapter 32 · 0% Book details