← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 48

Sashe 39

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ya nufi barin dining din, zuba ido nayi kawai in ga hukuncin da salees ze yi ko da dai ba wani sabon abu bane cewa zeyi yaro ne. To ny utmost surprise se kuwa Salees ya mike a hanzarce har yana neman ture table din ya maza ya riko hannun Sahal dake huci kamar ze daki wani, cikin lallashi da kwantar da murya ya shiga lallaba shi kan yaje yaci abincin "Wallahi ba zan ci ba Daddy, kawai saboda ba'a sona ita Ilham se aka dafa mata abinda take so ni aka ki, shiyasa ma ni na tsane ta dan bata da kirki, mtsww". Ya sake jan tsaki, burin salees dan sa yaci abinci kar ya zauna da yunwa so se duk be yi overlooking wannan rashin kunyar da yayi a gaban sa ba, shi dai damuwar sa yaci abinci, ganin yadda uban ya damu se ita ma Mariya ta shiga maganar playing her own role Wanda ina gani na gane makirci ne "Haba Sahal wannan wane irin wulkanci ne, ka tashi kaci abincin nan ko se ranka ya aci". Kawai se yaro ya fashe da kuka tare da shigewa jikin baban sa yana maganganu "Ka gani ko Daddy, itama Mommy bata sona, i won't eat this food ko zan mutu wallahi, Daddy pls ka maida ni wajen Granny". Aikuwa kamar wanda ake dannawa remote se salees ya ture Sahal daga jikin sa ya shiga zazzaga masifa "Wannan wane irin rashin mutunci ne da wulakanci, akan me zaku samin yaro a gaba da tsangwama har yana gwammace wa rayuwar wani wajen kan gidan uban sa, ba tun yau ba na sh fada muku ban hada son da nake ma ya'ya na da kowa ba dan a kan su wallahi zan saba ma kowaye, har kema ki bar ganin kece kika haife shi dan babu ruwa na ke mahaifiyar sa ce hukunta ki zan yi in kika nemi takura min yaro, gargadi na karshe kowaccen ku ta kiyayi taba min yara, ku kiyayi bata musu dan a maimakon yaro ya bar gida sedai ku kubar shi dan nan ne dolen sa gidan mahaifin sa akasin ku, ke khadeejah tashi ki dafa masa sakwarar". Tun da ya fara magana ban janye daga tagumin da nayi ina bin shi da kallo ba har seda naji last statement din shi "...ke Khadijah tashi ki dafa masa sakwarar"... Na sake maimaita kalaman a walwa ta dan in tabbatar da eh abinda salees ya fada kenan, bayan na tabbatar din se na dago na zuba masa ido wai dan in gane akan fuskar sa wasa yake yi ko da gaske sedai daga look din fuskan shi babu wani alamu dake nuna wasa, he look so serious ma'ana dai sakwarar yake so in yi wa dan gwal din dan sa "Is okay boy, kar in Kuma jin kace zaka je wani gidan, you've no home other than this house which is your father's house, and stop crying, your pounded yam is yet to be ready". Ya fada cikin lallashin dan sa da ya dauka ya dora kan cinya, murmushi sosai Sahal yayi yana kankame baban sa "Thank you Daddy, I love you so much". "Thanks so much boy, daddy loves his little ones so dearly". Se kuma suka saki dariya Salees na mikawa Ilham hannu itama tayi joining din su yamutsa fuskan da Sahal yayi yasa cike da kulawa ya shafa kan sa "Yunwa ne ko, dan yi hakuri yanzu zaka ci abinda kake so". Se kuma ya juyo inda nake "Why are you still seating, pls je ki masa abinda yake so yunwa na damun sa". Yanzu kam na tabbatar da gaske yake abinda ni kuma ba zan dauka ba kenan, haka kawai saboda san ran sa da na dan sa ya hana mu cin abinci cikin kwanciyar hankali dan ko spoon daya ban yi ba yaron nan ya tashi hankalin mu yanzu kuma ana batun in tashi in masa pounded yam "Am sorry bazan iya masa pounded yam ba yanzu its too late, gashi ko abinci ban ci ba and ka san dadewan sakwara in nayi sauri in gama in an hour ga kuma abincin dare na jirana". "So kina nufin ya zauna d yunwa kenan". Se da na nunfasa kana na dubi sashin da Sahal yake tsaye "Ba haka nake nufi ba, yau kam yayi hakuri yaci couscous din gobe se in masa sakwarar ko kuma in yi ta as dinner". Ko kafin salees yayi magana Sahal y riga shi "Allah ba zan ci couscous ba, akuya ne ni da zanci abu me kaman dusa, ni ba zan ci ba". "And I'll cook the pounded yam as dinner, now lemme cook indomie for you da sauri'. "Ni i won't eat sakwara for dinner, ai kin san bana cin abinci me nauyi da dare malamin mu yace mutum yanayin katon ciki". Confusedly na tsaya ina kallon yaron jin kome nace se ya kushe, ko ta ina na fito se yace ba haka ba, gyaran murya yayi yana kallona strictly yace "Kawai kiyi masa tun da ya nace, ina ce muna da pounder". "Ka fa san ya lalace tun kwanaki". Na fada kaman zan fashe da kuka, se shima yayi shiru na dan lokaci kafin pleadingly yace "Pls pound it a turmi tun da bashi da yawa, i can't put an eye yaki cin abinci". "Am sorry Salees, Mariya tayi masa ko kuwa kuje restaurant dan wallahi ba zan iya yin sakwara yanzu ba". And this my reply shine dalilin da yasa Salees ke ta min fuskan shanu yau kwana biyu kenan, dan kamar yadda na fada ba zan yi ba ban yin ba, ban san yaya suka yi ba, Mariyar ce tayi ko kuwa siya suka fita suka yi................... *TWO PAGES TO GO , SAURA PAGES BIYU FREE CHAPTERS SU KARE, KINDLY MAKE YOUR PAYMENT FOR IT'S PAID BOOK* *INTERESTED BUYERS SHOULD CONTACT* *09013101854* Ouummey Ouummey 14 {5/14/2023 }
Chapter 39 · 0% Book details