← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 48

Sashe 35

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wattpad @ouummey Ouummey 12 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Twelve_ Haka ya wanzu dafe da kan sa da ke masa matsanancin ciwo cikin wani hali, kirjin sa wani irin bugu yake masa kamr ze faso waje, irin yadda kan sa ke sarawa ji yake kamr ya cire ya yar. Wuni guda haka ya wuni cikin wannan har zuwa karfe biyar da ya iya tashi yana dafe bango saboda jirin dake dibar sa, yana ji ana kiran sallar Asr amma ya kasa tashi har aka idar duk akan kunnen sa. Anan bedroom din yayi alwala ya gabatar d sallah a zaune saboda jiwar da yake gani, addu'ar da yake so yayi ma kasawa yayi dole ya silale ya kwanta kan praymat din yana runtse ido. Oat din ta damawa Miemie kamar yadda suka fi kiran Meemah saboda sunan Maamahn su da taci sannan ta fita zuwa dining dauke da ita a hannun ta ta zaunar da ita kan seat daya itama ta zauna a daya, Ameerah ta zubawa abinci a plate ta tura mata gaban ta hakan yasa ta kalle ta cikin rashin fahimta dan mostly tare suke ci "Eat your food Ameerah and pls do take care of Miemie bari na gano Dada". Gyada mata kai Meerah tayi iya kuma ta shiga zuba abinci cikin plate daban, faten dankalin turawa me ruwa ruwa ta zuba masa da ya sha kayan lambu da kuma hanta sosai, cikin nutsuwa ta dora kan madaidaicin tray tare da dora goran ruwa me madaidaicin sanyi se kuma lemon kwali ta dauka ta nufi falon sa. Kan Centre table din sa ta aje abin kana ta karasa kofar bedroom din sa ta shiga knocking ganin bata gan shi a falon ba, a hankali take knocking din dan har ta takura masa sanin da tayi baya san hayaniya, jin shiru yasa cike da fargaba ta fara tura kofan a hankali har ya bude sosai kana ta shiga bakin ta dauke da sallama. A gigice ta karasa wajen da yake kwance ta shiga girgiza shi tana kiran sunan sa sedai ya kasa amsa wa, wannan ya kara gigita Haanah ta nemi fita a guje dan neman wanda ze taimaka mata a kai shi asibiti amma dole ta tsaya jin yadda ya riko hannun ta. "Yanzu zan zo, am coming Dada, zan kira maigadi ya taimaka min mu kai ka asibiti ne, sannu Dada yanzu zan zo". Da kyar ya motsa bakin sa yayi magana cikin muryar sa dake fita da kyar "Dauko min drugs dina a drawer Haanah". A rude ta shiga amsa masa tana mikewa "Toh Dada, sannu bari na dauko, sannu Dada". Da tarin magungunan ta dawo gaban sa ta zauna kana ta dauko wanda ze sha kasancewar ta san prescriptions din sa, bottle water din ta bude ta aje kana ta fara kokarin taimaka masa ya tashi zaune, duk da yanayin da yake ciki seda murmushi yayi escaping daga lips din sa, yo Allah ya tuba Haanah ko motsa shi zata iya yine balle ta daga shi. "Sannu Dada, sannu, open your mouth ka karbi maganin kaji". A hankali ya bude bakin ta sa masa kwayoyin kana ta sa masa bakin robar ya shiga shan ruwan, seda ya hadiye maganin gaba daya sannan ya janye bakin sa yana sakin numfashi kasa kasa, komawa yayi ze kwanta tayi sautin rike hannun sa tana girgiza masa kai "A'a Dada, kar ka kwanta maganin ze dame ka, ka dan zauna kadan ya fada maka, lemme bring your food tukuna". Jingina yayi kamar yadda ta bukata ita kuma tayi saurin fita zuwa inda ta aje abincin sa ta dauko masa, cokali tasa ta debo tare da kai masa baki taba fadin "Dada haaaaa". A tausashe, girgiza mata kai yayi alamun a'a se kuwa ta kwabe fuska tana neman yin kuka "Pls Dada ka daure kaci ko ka sami karfi kuma ciwon ya tafi, You know bamu da kowa a duniyan nan da ya kai ka Dada, we loose our Maamah ba zamu so muyi loosing din ka ba, you're all we have, our only strength and source of happiness, pls eat for our sake Dada, for your little ones kaiiii". A sannu ya bude bakin kamar baya so ko da yake ba kama bane baya so din, ze ci ne dan su kamar yadda ta fada dan mafi girman tashin hankalin sa shine ganin damuwa kan fuskokin ya'yan sa, har can go to any limit dan ya sa su farin ciki ko da kuwa shi baya ciki, a hankali a hankali ya dinga karbar abincin har ya koshi, she's glad ganin yaci da yawa dan farin cikin ta sosai ya bayyana kan pretty face din ta taba ta sakin cute smile "Ka gani Dada, dama kana jin yunwa, kalli fa ka kusan cinye wa na ji dadi, yanzu zuwa anjima zaka iya kwanciya amma da zaka hakura har kayi isha tun da kaji ana sallan magrib yanzu". "Allah yayi Miki albarka Rayhanah, Allah ya hada kan ku da yan uwan ki ya albarkace ku da mazaje nagari". "Ameen Dada, Ameen, in kama ka kaje kayi alwalan?". Dariyar sa me kyau yayi "Haba dai, Dadan ki is not as weak as you're thinking, zan je da kaina, kema je ki kuyi sallah da yan uwan ki and stay with them nima yanzu zan fito". Pecking goshin sa tayi tana wide smile "Okay Father, a fito lafiya". Ta fice rike da tray din kayan abincin sa, a falo ta tadda su Miemie da Ameerah zaune suna kallon cartoon, kallon ta Meerah tayi tare da daga mata gira alaman yaya yake and she answered cikin yi mata alama da hannu alamun he's fine. Duk suna yin body language ne saboda Miemie dan tana jin ance Dada sun san zata addabe shi ne ta hana shi sukuni da kiran Maamah da a rana se ta kira yafi cikin calbi. Rayhanah bata mamakin hakan dan a bayyane yake Miemie Maamah's girl ce akasin su da suke Dada's babies, a rayuwan su basu taba sanin wani abu wai shi kulawar uwa ba hakan yasa tsakanin su da ita kallo ne da gaisuwa, daga nan kuma se su takure waje daya, walwalar su kuwa har se idan Dada na gida. Zama tayi kan dining ta dan ci abinci a gurguje kana ta tashi zuwa bedroom tana musu magana "Oya girls, time for magrib prayer". Tashi duk suka yi zuwa dakin inda one after the other suka yi alwala Ameerah tayi wa Miemie sannan suka saka hijabs din su da Rayhanah ta dauko musu kana suka jeru kan praymat daidai lokacin da Dadan ya leko, ganin su a haka ya juya ya fita zuwa Masallaci suma suka tada nasu sallan. Suna idarwa suka yi azkhars din su again Rayhanah ta tashi ta dauko musu kur'anan su dake bedside drawer ita da Meerah suka fara karatu inda Meerahn ke biya mata karin da aka yi musu juya zuwa na yau, seda suka gama sannan ta kara mata verses biyar inda ita kuma ta cigaba da maimaita wa Haanah kuma ta koma ga Miemie. Cikin wayo da dabarar da Allah ya mata ta yi sa Haanah ta biya mata aya dayan da ta kara musu yau a school, tar yarinyar ta kawo karatun ba ko tuntube hakan yasa ta kara mata aya biyu marasa tsayi, shima se da ta ga ta iya sannan ta bar ta. Hijab ta cire ta karbi nasu ma da suka cire ta ninke tare da maidawa cikin wardrobe kana ta juyo se kuwa idanun ta suka fada cikin na Dadan ta da ke tsaye yana bin ta da kallo cike da soyayya da kauna me tsanani, a ko da yaushe ya kai kan sa kasa da sunan sujjada baya dagowa face yayi godiya ga Allah da ya albarkace shi da samun ya daya tamkar da dubu, yar dake matukar so da kaunar sa hadi da tsananin tausayin sa, yar da ba dan ita ba be san yaya rayuwa zata kasance masa da yaran sa ba alhalin yanzu da ba mahaifiyar su ta gushe. Rayhanah yarinya daya ce amma a wajen sa tafi yaya dari domin kuwa ta share masa hawaye tun kan ta san kan ta, tun tana karama take da basira da wayo hadi da nutsuwat fahimtar abubuwan da suka girmi hankalin ta, a maimakon abin ya dame ta yasa ta cikin wani hali se ya koya mata tausayin mahaifin ta da halin da yake ciki, wanda ta taso ta girma dashi ya ke kuma karuwa a kowace kwana da wuni, kaunar ta gare shi bata buya a ko ina a kuma ko wane irin yanayi, ita ce rai daya dake gane kowane irin hali yake ciki tun kafin bakin sa ya furta, ta san shi ciki da waje sedai kawai yayi mata ta babba da yaro ya layance mata wasu abubuwan amma ba wai dan bata fahimta ko gane ba. Tana fifita cin sa kan nata, walwalarsa kan nata, farin cikin sa kan nata haka kuma tana damuwa da damuwar sa tayi dariya da dariyar sa, shiyasa ita din daban ce cikin yaya ukun da Allah ya azurta shi dasu, ita ce kuma *RIBAR AUREN* Maryam da kullum ya kalla baya dana sani balle nadama yake kuma alfahari da kasancewar ta ikon sa mallakin sa. "Barka da dare Dada na". "Barka kadai yaran Dada, hope you all fine?". "Yes Dada". Suka amsa masa gaba daya ban da Haanah dake ta murmushi tana kallon su, seda ya gama gaisawa da su gaba daya sannan ta durkusa har kasa ta gaida shi, be amsa mata ba seda ya shiga har dakin yasa hannu ya dafa kan
Chapter 35 · 0% Book details