Sashe 14
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wattpad @ouummey *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Five_ Har ya gama zuba surutun sa ina zaune kamar yadda nake tun farko sedai tsoron Allah ya dade da cika zuciya ta jin wai yau a kaina ne Salees yake rattabo wadannan Laifuka da matsaloli, lallai rayuwa juyi juyi ce wai kwado ya fada ruwan zafi. "Uhmmm yanzu duk wannan abubuwan ita hamshakiyar ke yi amma ka zauna kana kunsar bakin ciki, lallai sannu khadeejah autar mata". Sake kasa da kai nayi ina jin tune din da Hajiya Iya ke magana dashi kafin ta ja dogon tsaki "Ke dago nan ki kalle ni bana son munafurci, ana magana kina sunkuyar da kai kamar wata mumina bayan kasurgumar muguwa ce ke, dago nace ki kalle ni". A sanyaye na dago na zuba ido na cikin na Hajiya Iya "Yanzu ke dan kin kasance butulu wadda bata san alkhairi ba har ya'yan Salees abin ki ne a wajen ki bayan dimbin halaccin da yayi miki a rayuwa?, Da zaki fidda hannu ki daki yarinya karama irin haka saboda baki san zafi da ciwon haihuwa ba, anyi magana ke ga Sarkin an iya bakin rai kin dauki fushi da su". Se kuma ta juya kan Salees "Ai duk kai ne shashasha shi yasa har mace ta raina ka, ban da raini kana kallon ta tana iskanci ka zuba ido baka yi maganin ta ba, ko da yake ai ta gama da kai yanzu ma da sauki tun da kana iya ganin laifin ta". "Saurare ni nan kiji, in kin gama da Salisu to ni na fi karfin ki, shima kuma gashi nan Allah ya fara karya alkadarin ki ta hanyar matar kwarai da ya samu, na san ba komai ke damun ki ba face bakin ciki da hasssada tare da asararren kishi, ke a rashin tunanin ki se mu bar Salisu ya zauna da ke kadai bayan ba haihuwa kike ba, kullum yayi ta cika miki ciki da abinci kina juye wa a masai babu fus balle as, to ta Allah ba ta ki ba, jinin Salisu ne gasu nan kina gani, karewar bakin ciki ki hadiyi zuciya ki mutu ni da wallahi farin ciki zan yi dan zaman ki gidan dana dan kawai babu yadda zan yi ne amma ba so nake ba. Batun yara kuma daga yau na shata layi tsakanin ku, ko da wasa kika Kuma kai hannun ki kan jikoki na wallahi a bakin auren ki dan se Salisu ya sake ki ko na tsine masa albarka, uwar su kuma in dan kin ga me hakuri ce kike cuta mata to Allah yana kallon ki kuma baze bar ki ba". "Kai kuma in zaka dauki mataki akan juyar matar ka ka dauka in kuma zaka cigaba da zama tana raina ka kai ka sani". Hakuri Salees ya shiga bawa Hajiya Iya ganin har dashi cikin fadan sedai ni tun daga gaishe ta ko tari ban yi ba balle wani ban hakuri, na bata hakuri akan me, me nayi mata, bayan duk cin zarafin da aka min kuma na bada hakuri, tabdi. Aikuwa rashin bada hakuri na ya sake tunzura Hajiya ta cigaba da bala'i da fade faden maganganu na cin mutunci d zarafi a kaina har muka mike zamu tafi "Allah ya bamu alkhairi Hajiya". Na mata sallama batare da na bada hakurin ba, Hannatu tayi tsagal ta zage ni yarinyar da yanzu take shekara sha takwas, fadin shekarun da na bata ma bata baki ne "Juyar banza da wofi mara amfani kawai, ciki ba komai se kashi, mtsww Allah dai ya raba yayan mu da kayan bakin ciki". Na jita sarai kuma zagin ya ci min rai dan na tsani raini a rayuwa ta shiyasa duk runtsi bana yarda na wulakanta ko cin mutuncin na gaba da ni. Ashe shima Salees zagin ya masa zafi dan har na dan yi gaba se ji nayi ya fisgo ni baya kofar dakin hajiyar ya hade rai tamau yana yiwa Hannatu mugun kallo "Dan ubanki matata sa'ar ki ce?". Ya tambaye ta a kausashe lamarin da ya matukar daurewa Hajiya Iya kai dan su a ganin su ai yanzu Salees ya daina so na dama suna cewa soyayyar sihiri ce, to tun d yanzu ya karye ai zasu taka ni yadda suke so "Kar ka kuma zagar min ya in ba haka ba ranka ya aci". "Amma Hajiya kin san dai hakan ba daidai bane, ban da iskanci karamar yarinya kamar Hannatu ta kalli khadeejah ta zage ta, Hannatu da bata fi kanwa ta kusan shida ba wajen khadeejah, to wallahi tun wuri ki shiga hankalin ki in ba haka ba se na kusa karya ki, mahaukaciya mara hankali kawai". Ya fada yana karasa directing maganar kan Hannatu, nidai ina samu na zame hannu na daga cikin nasa se kawai na yi gaba abina na fice dan wallahi ko kadan shigan min da yayi be burge ni ba. Na riga su isa gida dan haka na shige daki na kulle tare da yin lamo kan gado na, in ka ganni zaka yi zaton wata marainiya ce d babu uwa kuma babu uba haka babu sauran gata, kulle ido na nayi ina sauke numfashi ina fadawa kai na rayuwa ce haka kuma Allah yaso gani na, jarrabawa tace da ban isa na tsallake ba har na samu na ji sanyi a raina kafin na shiga toilet dan yin wanka. "Yanzu haka zaki zauna kullum kina kuka akan matsala daya, na baki shawara tuntun tuni Falmata amma kin share, kin gwammace ki yi ta asarar hawayen ki a banza ko, to ai shikenan". Babbar mace da a kalla zata kai shekaru hamsin da biyu zuwa da biyar ta fada tana kallon kawar ta dake zaune ta zuba tagumi hawaye na bin fuskar ta kamar an bude famfo. Ganin bata ce komai ba yasa matar jan tsaki tana duban Falmata "Bata akan ki kadai abin ya tsaya ba, yanzu haka ina fada miki da zan shigo na hadu da wancan fitsararren dan Adam, wallahi yaron nan akan ido na yayi min tsaki har da tsartar da yau sannan ya shige bangaren su, shin haka zaki zauna ke a raine wanda ya alakantu dake ma ana masa kallon banza shara wofi mara amfani Falmata, shin ba zaki yi komai domin kwato abin da ya kasance naki ba tun farko? Ko kuwa zuba ido zakiyi har se rayuwa a gidan nan ta gagare ki, ki dubi karamin yaro Haisam irin motar da yake hawa ki kuma dubi taki wadda kike jin jiki da ita tuntuni, ya kamata ki farka daga barci da kike yi ki amso what is rightly yours, Ina baki shawara ne matsayin yar uwa aminiya wadda bata san ganin ki cikin komai face farin ciki". "Ban damu da nawa ze kashewa yayansa ba Farida, ban kuma damu da kyautatawar sa gare su ba, damuwa ta yadda kome na bukaci Alh yayi min se ya kawo uzuri, ba kuma ze yi abin nan ba ko da zuwa da shekaru nawa ne, a cewar sa kullum nauyi kara karuwa yake a kan sa saidai yana mantawa cikin nauyin nasa akwai ni, ina da hakki a kan sa wanda a yanzu ya sauke wa kan sa, da ni da babu duk daya ne a wajen sa, se ya shigo ya ishe ni da dadin baki, kin san matsalar da nake fama dashi na ciwon ciki, naje naga likita akan shi sedai ya bukaci naje babban asibiti, to ko da naje sun ce se an min aiki, yanzu halin da ake na fadawa Alh dan ya shirya min tafiya zuwa India ayi min aikin a can amma yace be da kudi se gashi dazun nan a gabana yayi wa yar lelen sa alkawarin sabuwar mota zuwa gobe, ban face ya bini ba, ban kuma ce ya biya min tare da wani da zai kula da ni ba, iya ni kadai nace amma yace babu se gashi be rasa na canja wa yar sa motar hawa ba, innalillahi wa inna ilaihi rajiun". Hajiya Falmata ta fada tana sake rushewa da kuka, hatta da Hajiya Farida hawaye take yi na tausayin kawar ta, aminiyar ta kuma yar uwar ta "Mata sune matsalar mata yan uwan su Falmata, na rantse miki da girman Allah duk abinda Alh yake miki da sanin Hauwa kuma tsarin ta ne, tun asali matar nan bata son ki kin sani ta ya zata so miki kwanciyar hankali, kai hasbunallahu wa niimal wakeel". "Farida ina ganin zan hakura da auren Alh kawai dan be da wani amfani a waje na, gara kawai in san single nake da ciwon zuciyar da Alh ke kokarin ganin ya kakaba min karfi da yaji". "Ba zaki bar mata gidan ki ba, ba zaki bar mata mijin ki ba, wallahi ba zaki je ko ina ba, kenan ma kin yi biyu babu, baki ga tsuntsu baki ga tarko inaaa, sam wallahi". "Gwara in tafi da in zauna Ina kun sar bakin ciki". "Kece kin cika sanyin rai, tuntuni na kawo miki shawarar yadda zamu yi maganin ta amma kin xayan wasu tunane tunane, ke yar uwa ta ce kuma kawata, wallahi ba zan taba yin abinda zan cutar dake d sani na ba, ki bani dama mu nuna wa Hauwa ita karamar kwaruwa ce, ita yanzu ta soma bariki lokacin da mu kuma muka riga muka maida ita gida". Shiru Falmata tayi kafin ta saki ajiyar zuciya a hankali "Ba tsoron Hauwa nake ba Farida, saidai ina tsoron Ubangiji na, ban haifa ba, ban ji dadi ba a gidan aure na sannan kuma na lalata kiyama ta Falmata?, Anya in nayi hakan ban cuci kaina