← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 48

Sashe 42

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kofar tare da murza key din da ya sawa kofar na fita, Rukayya, Sadiya da Hannatu duk na tsaye bakin kofar, ashe suke bugu tare da kiran sunan sa suna fada masa Hajiya Iya tace ya fito daga daki na kafin ran shi ya baci. "Rukayya Sadiya ai kun san ni kun san ni ba mayya bace ko, kema Hannatu kin sani ko?". Wani matsiyacin tsaki Sadiya taja tare da juyawa ta nufi falon ragowar suka rufa mata baya suma bayan sun yi nasu tsakin Hannatu na kunkuni kasa kasa, a haukace na rufa musu baya ina kuma yi musu magana, ni dai buri na kawai su yarda ni ba mayya bace. Fisgo ni Salees yayi jikin sa ya rungume, duk yadda nake ture shi ya sake ni ya kiya har seda ba hakura na lafe jikin sa na shiga maida numfashi da karfi da karfi kafin kuma wani maraitaccen kuka yi kwace min, kuka nake yi me suna kuka wanda tun d nake shiga tension a gidan Salees ba na tunanin na taba makamancin sa, Muryar Hajiya Iya ce ta sa Salees janye wa da sauri yana sosa kai "Sake ta sallamamme, sake ta nace karamin mara mutunci, mara zuciya kawai, kai in da kasan kan ka har ka kuma kallon wannan abar bayan abinda tayi, wuce muje, kema munafuka muje dan yau ko mutuwa zaki yi karewar mutuwa se an yi maganar nan yau". Hak ta tasa mu gaba har ciki falon, na sake neman waje na zauna haka ma Salees itama ta koma wajen ta ta zauna "Abinda y faru jiya d dare zuwa yau ya zama na farko na karshe, wallahi tallahi rantsuwar dan musulmi kika Kuma taba min suruka ko jikoki se ran ki ya baci, in zaki yi maitar ki kiyi ta can a waje amma ban da nan dan b zaki ci riba ba". Seda na saki sheshshekar da ta taso tun daga kasan zuciya ta sannan na dago "Na rantse da girman ubangijin da ya halicci sammai da kassai Ni ba mayya bace Hajiya, a cikin trend din dangin mu wallahi babu maye balle in gada". "Yo Allah na tuba maitar da ake siyarwa yanzu kamar alawa a kasuwa, ai ba abin mamaki bane dan babu a dangin ki kuma an same ki da ita, ni dai na fada miki wallahi ba zan lamunta ba dan gwara ki cinye kan ki da ki taba min zuri'a". "Me nayi muku da zafi hak da zaku jefeni da kalmar maita, me na tare muku da zaku min wannan accusation din, auren Salees gare ni ne laifin da har yaja min wannan zargin ko kuwa tsabar tsana ce?". Na tambaya hawaye na kafewa a fuska ta yayinda ya koma zuba ta cikin zuciya ta "Yi man shiru munafuka mara tsoron Allah, wa zaki yaudara da kalaman ki ko da wani fuskar tausayi bayan ke baki tausaya wa kan ki ba, daga yin mafarkin ki kin biyo ta a guje kin daki cikin ta yarinya ta tashi da ciwon ciki da zubar jini, hankali be kwanta ba har seda cikin jikin ta ya zube, cikin yan uku annamimiya kin yi mana asarar rai har uku, wallahi Allah ya isa tsakanin mu dake dan ba zamu taba yafewa ba". Hajiya Ramatu mahaifiyar Mariya ta fada tana fashewa da kuka yayinda Hajiya Iya ta shiga sharar ido itama su kuma ya'yan su suka rufe su suna basu hakuri da fadin Allah ze saka musu, ni dai tun jin wai Mariya tayi mafarki na se na juya gare ta na zuba mata jajayen ido na ina kallo na tsayin lokaci kafin cikin wata irin murya na tambaye ta "Na zubar Miki da ciki ta hanyar maita ko Mariya?, Kin yi mafarki na na daki cikin ki gashi kuma ya zube ko?". Kallo na Mariya take yi kawai bata ce komai ba hakan ya sa na saki wani busasshen murmushi mara kyau balle fasali haka mara ma'ana "In har na zubar Miki da ciki, in har na taba yin wani abu dan cutar da ke ko ya'yan ki Allah ya saka Miki da gaggawa Mariya". Na fada da karfi ta yadda kowa ze jini kana na maida duba na kan Hajiya Iya da Hajiya Ramatu "Kuyi hakuri Hajiya, kuyi hakurin cinye muku cikin Mariya da nayi kuma ku kwantar d hankalin ku domin ba zan kuma saukar da kwadayi na kan ya'yan ku ba". "Kuma kuyi hakuri". Na fada directing to su Safara'u da ragowar matan da kuma su Rukayya kana kuma na tashi da sauri nayi daki na tare da kullewa da key, irin ciwon da zuciya ta ke yi a lokacin ba me sauki bane, hawaye ya kafe a idanu na, walwa ta ta tushe na rasa tunanin da zan yi, daga karshe se na samu kaina da nufar toilet na dauro alwalar da ban san daidai nayi ta ba ko akasin haka, Kur'ani na dauka na shiga karatu a zuci kafin a hankali murya ta ta fara fitowa kadan kadan har ta fito sosai kana kukan ya biyo baya. Ina jin bugun kofa tare da muryar Salees amma ban ji a raina zan bude kofar ba, ina kuka haka ina karatu ban fasa ba har se da naji mafi girman kason nauyin zuciya ta ya ragu, wani irin bacci ya dinga sanda ta sannan na aje Kur'ani na bingire a wajen. Ban farka ba se bayan magrib, a lokacin kam alhamdillah bana jin wani bacin rai me girma sedai kalmar maita ta samu wajen zama na musamman a walwa ta, seda nayi wanka na canja kaya na ci snacks dina sannan na bude kofar na fito, babu kowa a falon haka kuma gidan yayi shiru alamun duk sun tafi, fridge na bude na dau ruwan da ya fito dani sannan na nufi komawa daki se Salees da ban lura dashi zaune kan kujera ba ya dakatar dani "Khadeejah". Juyowa nayi na kalle shi tare da sake masa murmushi ganin yadda duk yayi wani iri, tasowa yayi gare ni tare da riko hannaye na "Are You fine, ba abinda ke damun ki, ba inda ke Miki ciwo?". Wani murmushin na sauke jin tambayoyin da yake min wanda shima ya san in nace bana jin kome ya fada karya ne sedai dan na kwantar masa da hankali se na amsa masa "Ka kwantar da hankalin ka, am perfectly fine and okay". "Abinda hajiya iya su.....". Rufe masa baki nayi da hannu na har lokacin murmushi na be bace ba "Hajiya Iya kamar Ummi na ce, so karka damu da abinda ya faru". Daga haka nayi gaba leaving him speechless. Kwanciya nayi kan bed tare da janyo waya ta, ina bukatar shawara a wannan lokacin dan ina jin bazan bar wannan maganar ta tafi haka ba, dole zan dau matakin wannan bata sunan da ake kokarin yi min, kotu zan kai kara, shigar da kara zan yi abin min hakki na, amma kafin nan ina bukatar tattaunawa da wani, ina bukatar wani da ze yi supporting dina ya fada min Yes kin yi daidai Khadijah sedai waye wannan?. Ba ze yiwu in fadawa Ummi ba balle har hankalin ta ya tashi, yaya Salima kuwa na san in na fada mata kamar na fadawa Ummi ne dan se ta sanar da ita, Abba kuma is not a solution dan hanani ze yi yace in yi hakuri, yayyu na kuwa ba ma zan iya maganar dasu ba dan suma maza ne ba fahimta zasu yi ba. Na dade rike da waya a hannu kafin na shiga facebook, group din mu na NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS na shiga nayi posting anonymous message, in brief na fadi matsala na tare da neman shawara bayan na canja abubuwa da yawa daga abinda ya faru dan gudun halin mutane na daukan matsalan mutum suyi ta yadawa. Kafin kace me members suka shiga reacting tare da comments, ban duba ba seda na tara da dan yawa sannan na shiga bi one after the other, sannu a hankali nake karantawa ina analysing bangaren shawarar da tafi yawa, in yi ko kar inyi da dalilin haka, sedai mostly duk suna cewa kar in Kai karar ne saboda ba kowa yayi accusing din ba face uwar miji na, duk kuma so d kaunar da mijina ke min base goyi bayan kai mahaifiyar sa kotu ba hakan kuma ze iya kawo karshen aure na, in bar su da Allah kawai in cigaba da fada masa ze min sakayya da gaggawa. Wannan itace shawarar da na dauka, se da na gamsu da ita sannan na kashe datan na koma na kwanta ina cigaba da tunani. Washegari haka na shirya na taci aiki na sedai kukan da nayi juya yasa fuskana duk ya tasa duk da kuwa na dan shafa powder da kohl dan ya boye yanayi na, karfe goma na safe muka shiga meeting din da anan ne za'a fadi list din sunan mutanen da suka yi dace da samun promotion da kuma gurin da aka canja musu na aiki in an canja din. Suna na ne na biyar a list din, wani irin sassanyan farin ciki da ya sauka a raina a lokacin ba zan iya fada ba sedai be yi nisa ba ya gushe jin an canja min garin aiki an maida ni garin Bakwarni maimakon garin Darma da nake, sanyi jiki na yayi dan a bayyane yake dole haka zan hakura da promotion din in cigaba da zama a nan dan baze yiwu in tafi wani garin aiki ba bayan aure na da mijina na garin Darma ne. Sunan Salees shine na goma sha biyu dan daga kasa aka fara zuwa sama, shima ya samu promotion me girma haka kuma shima an canja masa gari zuwa Bakwarni lamarin da ya faranta min fiye fa komai dan bana tantama yanzu kam zan je tun da shima dole ya koma can. Da wannan farin cikin na dawo gida ina tsara yadda zan je in yi wa family na sallama dan sati kadai aka bamu muyi reporting sabon wajen aikin mu, ranar kam a gidan Ummi na na wuni dan saboda guilty din abinda su Hajiya Iya suka yi min Salees ya bar ni na wuni can. Shawarwari masu yawa Ummi
Chapter 42 · 0% Book details