← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 48

Sashe 38

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wattpad @ouummey Ouummey 13 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Thirteen _ Yana lura da yarda Haanah ke walwala da farin ciki har zuwa lokacin da suka yi masa sallama suka tafi daki dan yin bacci, da ido ya raka su har suka shige daki yayinda ya sake gyara zaman sa kan cushion din da yake yana kwantar da kan sa kwakwalwar sa na yin nisa cikin tunani. Seda ta tabbatar ta Miemie tayi bacci kafin ta sauko daga gadon ta dauki wayar ta da sauri, curiously ta shiga kiran layin kakar ta without minding dare ya fara nisa dan ita after ten lokacin, seda wayar ya kusa karewa kafin aka daga tare da sallama, a dokan ce Haanah ta amsa wa kakar ta and without sauke numfashi ta ora da dalilin kiran "Albishirin kin Yaaya". Daga can bangaren dattijuwa ce zaune ina gadon ta me kyau kamar na yaran amare yan gata, ba wani shekaru ne da ita da yawa can ba sedai zata kai sittin da wani abu zuwa close to saba'in, cike da son jikar tata ta amsa mata da "Goro fari kakal Rayha". Ta bangaren Rayhanah duk da bata san yadda Yaaya ke bata mata suna amma farin cikin da take ciki yau ya hana ta complaining "Dada ya yarda ze yi aure Yaaya" ta fada excitedly tana washe baki kamar gonar auduga, unbelievably Yaaya ta zaro ido tana sake manne wayar da kunnen ta "Kai haba dai, wa ya fada miki wannan tatsuniya?". Seda ta tura baki gaba jin yadda Yaaya ke neman karyata ta bayan ta san karya bay acikin habits din ta sannan ta bata amsa "To wallahi da gaske nake kuma ba tatsuniya aka bani ba shi da bakin sa muka yi magana dashi kuma ya yarda yace ya amince ze yi aure". Wani irin kwallan farin ciki ne ya taru a idanun Yaaya da yasa muryan ta ya raunana "Allah yayi miki albarka Rayhanatu, Allah ya jikan mahaifiyar ku ya sa ta huta, ke kuma Allah baki miji na gari da yaya masu albarka da zasu ji kan ki kamar yadda kike jin kan mahaifin ki". Da Ameen Ameen Haanah take ta amsa Yaaya har ta gama addu'ar ta ta shiga share hawaye "Dama na fada miki ki daina raina karfin talakar gani, kina ta wani fada min ba zan iya ba b azan iya ba se gashi ba baki mamaki, kuma ina nan ina jiran alkawarin mu dan ban manta ba kince zaki bar min murjanin ki in dai na sa ya yarda, bye dare yayi se anjima". Rayhanah ta karashe tana dariya jin muryar Yaaya itama tana darawa, aje wayar tayi tare da kallon bed din Meerah se ta ga tuni ta yi bacci so se itama kawai ta kashe wuta ta kwanta kan gadon ta wanda kowa da nashi a dakin. Ta can wajen Hajiya Yaaya kuwa tana jin Haanah ta kashe waya itama ta aje taya tare da daga hannu ta shiga godewa Allah idanun ta na zubar da hawayen farin ciki, a cikin kaf rayuwar ta a yanzu dai bata da wani rai da take kauna kamar dan ta mahaifin su Rayhanah, tsananin soyayyar da take masa ne ya jagorance ta wajen aikata son zuciya ko kuskure zata kira abin wanda ya zama Mabudin duk kan wani kunci, damuwa, tashin hankali da rashin walwalar dan nata haka kuma suka zama makullin farin ciki da jin dadin sa, bata fahimci tayi kuskure ba seda lokaci ya riga ya kure ta yadda bata da wani abin yi musamman ma da duk lokacin da ta nemi yin wani hobbasa dan nata ke dakile t ta hanyar nuna mata ai komene tun da ya kasance zabin ta to he can endure it e ven if it'll cost his whole life ne. Bata yi kasa a gwiwa ba t shiga toilet ta dauro alwala tare da tada kabbara dan mika godiya ga Allah tare da fatan ya sallada abin a ran dan nata ba se nan gaba ya tubure yace be san zancen ba wanda a yanzu wannan opportunity din kadai take kallo as hanyar gyara kuskuren ta dan haka zata yi iya kokarin ta wajen ganin ta bawa mafi soyuwar dan ta farin ciki. ________ Rayuwa na ta tafiya abubuwa na faruwa masu dadi da akasin ta, a kalla yanzu kusan wata hudu kenan da muke zaune lafiya a gidan mu se yan abinda ba'a rasa ba, duk da zan iya cewa a kwanakin nan yanayin namu ze fi kyau da a kira shi kadaran kadahan dan kuwa dai ba wai muna cikin farin ciki bane, haka kuma ba wai ana tsananin tashin hankali ko rigima bane. Fushi ne dai yake yi kan wani incident da ya faru shekaran jiya, abin ba wani me zafi bane amma dake a wajen Salees ko me ya shafi ya'yan sa me zafi ne ba ya daukan shi da wasa se kuwa ya daukaka abin har fiye da misali. A shekaran jiyan ni ke da girki, hakan yasa na shiga kitchen kamar kowane lokaci na shirya launch kasancewar Sunday kowa yana gida, before in fara girkin da se da nabi ka'idar da ya tsara na cewa duk wadda ke da girki zata fara tuntubar yaran sa abinda suke so, in bakin su ya zo daya su biyun shikenan se a yi wanda suke so din gaba daya ko kuma ayi musu su biyu sannan me girki ya dafa abinda yayi niyya daga baya, in kuwa bakin su be yi daya ba to kowa a dafa masu wanda yake so individually, tun lokacin da yasa dokar na fada masa hakan wani karin aiki ne na daban gare mu amma se yace shi haka ya tsara dan in yaran sa ba su ji dadi sun yi walwala a gidan su ba a ina zasu yi?, Dole haka na yarda a wancan lokacin dan maganar shekara hudu baya nake yi wannan. Abinda ya faru shekaran jiya kuwa shine na tambayi Sahal abinda yake so kafin na shiga kitchen se yaron yace me zan dafa, take nace masa jallof couscous se watermelon juice, da farin ciki da komai Sahal yace min shi zai ci meaning base na masa different girki ba, ita kuwa Ilham da na tambaye ta se tace rice and stew zata ci, daga haka na shiga kitchen na hau ayyukana, nan da nan na hada abubuwan da zan yi na jera kan dining sannan na wuce daki na yi wanka tare da canja kaya kana na kwanta na huta ina jiran dawowar mijina daga masallaci Karfe biyu ya shigo wanda tun da na hango shi ta window na fito falon yana shigowa na masa sannu da zuwa tare da masa jagoranci zuwa dining din Mariya da yara suka biyo bayan mu, seda kowa ya zauna sannan na shiga serving din su daya bayan daya har n gama kafin na zubawa kaina na zauna dan fara ci sedai abin kamar almara se kuwa Sahal ya ture plate din gaban sa a shagwabe yana tura baki nan da nan kuma idanun sa ya tara hawaye, irin yadda baban ya rude yana tambayar sa lafiya se kawai na zuba masa ido ina jiran jin me ze ce, zuciya ta kuwa har da ayyana min may be shi da mahaifiyar sa ne "Bana son abincin nan Daddy". Da sauri na zaro ido jin abinda yace fuskar sa a kwabe kamar ba shi ne har da tsalle dan nace jallof din couscous din zan yi ba "Why didn't you tell your Aunty da zata yi girki?, She would have cooked your heart desire for you". Salees ya fada trying to rarrashi dan sa yaci abincin "Daddy I've told her ni pounded yam nake so while Ilham tace rice and stew, but see what she serverd me after serving Ilham her favorite". Strictly Salees ya dago yana dubana with plain expression a fuskan sa "Shi meyasa ba'a dafa masa abinda yake so ba after kuma yayi mentioning?". Seda na hadiye wani yawu ganin yadda yake interrogating dina kamar wata yarinya gaban ya'yan sa da matar sa sannan na iya na bada amsa "I've asked him me zeci and shima se ya dawo min da tambayan me zan dafa so i replies with jallof couscous, har da tsallen sa yana cewa yana so kafin na tambayi Ilham ta fadi nata, and here's the same boy narrating different story dan ban San yaushe yace pounded yam yake so ba". Daga yadda yake kallo na na fahimci ba wai zance na ya gamsar dashi bane sedai be yi hukunci directly yadda ya saba ba se ya dubi Ilham "Wane amsa yayan ki ya bawa auntyn ku da tambaye shi kan abinci?". Wlh a lokacin I was speechless, kenan salees na nufin be yarda da abinda na fada ba?, Mu sa ma be yarda ba, mu sa a ransa kawai yana ganin karya nayi, in ma hakan ne kenan baze iya rufa min asiri gaban yara ba se ya zubar min da kima, ko so daya shin Salees be kamata yayi tunanin tarbiyyan ya'yan sa ba, gaba daya se naji komai ya fita a raina, shikan sa Salees din naji ya zube min a ido na "Daddy naji fa sanda yake cewa couscous ze ci fa, Allah be fada mata sakwara yake so ba". Irin yadda Mariya ke bin Ilham da wani mugun kallo ka dauka kisan kai yar nan tayi bayan gaskiya ne kawai ta fada, shi kuwa Sahal yana jin me Ilham ta fada se kuwa ya ture plate din a matukar fusace da har yasa abincin kai ta zube kana ya tashi yana jan tsaki
Chapter 38 · 0% Book details