← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 48

Sashe 18

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ganiyar so da kaunar ta?". Wani irin laushi da rauni zuciya ta tayi a lokacin, kai wallahi maza sun iya dadin baki ta yadda zaki yi abu se bayan kin aikata ki dinga tunanin taya ya kika yi, me ya kai ki, wanda ko gobe se kin kuma yi in baki jajirce kin kai zuciyar ki nesa ba. Idanunsa da suka cika da hawaye na dago na kalli Salees, soyayyar sa ta cika min rai, na far kokarin bude baki na dan shaida masa ban dena son sa ba, ban bar kaunar sa ba haka kuma zan cigaba da hakuri dan kawai in yi rayuwa dashi, sedai kamar wadda aka dannawa pause haka na tsaya ina kallon sa na kasa fada, ba komai yasa hakan ba face abubuwan da ya dinga aika ta min a kwanakin baya, irin bakin ciki da bacin ran da ya kun sa min, wai har a gabana yake fadawa kishiya y fara gajiya da hali na, meaning ya fara gajiya dani, wanda a da be san da halin nawa bane ya so ni da a yanzu ze ce wai hali na, kawai nice ya gaji dani yake neman wulkantawa shine kuma yanzu ze dauko wasu shanyayyun kadafun sa ya zo yana karanta min karya. Eh karya mana a yanzu, na san a da Salees ya so ni Kamar yadda ya fada, nima kuma nayi haukan son sa, sedai ko rantsewa nayi ba zan kaffara ba a yanzu baya min ko da rabin rabin son da yayi min a da, akwai dai abinda yake bukata daga gare ni, akwai abinda yake so nayi masa ko yake nema a waje na shine bari ya yaudare ni da kalmar soyayya. Murmushi na saki bayan na gama kallon idon sa, se yanzu na gane me ya kawo shi daki na, se yanzu na fahimci soyayyar d yake fada yana min, ni dama nayi mamakin wai Salees ke fada min kalaman soyayya haka abinda in ban mance ba rabon da in ji irin wannan kalaman a bakin shi tun bayan haihuwar Sahal shekara goma sha biyu kenan yanzu. Be yi tsammani ba be yi tunani be se ji yayi nq ture shi daga gare ni na dauki waya ta nayi waje a hanzarce dan bani da lokacin zama magana dashi, ban shirya hakan ba tukuna dan wallahi alkawari nayi se na rama ko da kashi daya ne cikin kashi darin bacin ran da yasa ni. SALEES Ido ya zuba mata yana sake kankance ido cikin son tabbatar mata eh da gaske yake yanzu ya fara son ta ma, ganin yadda itama take kallon sa yasa zuciyar sa ta shiga tsalle a kirjin sa yana addu'ar Allah yasa ta yadda da abin da ya fada mata dan ya kai makura wajen san kasancewa da ita. Ba karya ya fada ba har yanzu yana son ta yana kaunar ta, sedai wasu halaye da ta ara ta yafa wanda be san ta dasu ba yasa yake yi mata abinda ya ga dama don ba zata bata masa rai a banza ita tayi farin ciki ba, be san wake koya mata bakin hali ba da yasa har take tsanar masa yaya da kuma neman ta ringa tsallake umarnin sa wanda shi kuma baze dauki haka ba. Be aje ya'yan sa a kusa ba a ran sa, sune abu mafi soyuwa gare shi so baze lamunci yaji ko ya ga tana musu wani abu na rashin kyautawa ya kau da kai ba, haka Mariya, tana iya kokarinta wajen ganin sun zauna lafiya amma Khadijah taki bada dama bayan da farko ita ta nuna ba abinda take nema daga Mariyar face zaman lafiya se gashi ta tankwabe rokon ta da kan ta, amma ban da wannan abubuwan yana son matar sa, Khadijah ce macen da ya fara so haka kuma macen da ya fara kasancewa da ya ke kuma samun gamsuwa wajen ta fiye da kowa, ta ya ya baze so ta ba?. Yana cikin tunanin yaji ta ingiza shi gefe tare da ficewa daga dakin da sauri, a rikice ya mike ze bi bayan ta se kuma ya tuna da Mariya da kanwar ta dake zaune a falon, dole ya tsaya ya koma dakin ya shiga kai da kawo ransa yayi mummunan aci da abin da tayi masa...................... Not edited Ouummey Ouummey 07 {5/5/2023 }
Chapter 18 · 0% Book details