← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 48

Sashe 23

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wattpad @ouummey Ouummey 08 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Eight _ A hankali na tura kofar na shiga baki na dauke da sallama, Muryar Ummi da ta amsa min yasa na san tana zaune a falon so ina cire takalmi na na shige gaba daya na cike da dokin ganin ta, aikuwa da gudu na karasa na fada kan ta ina dariya "Kai kai kai, kayar dani kike son yi Khadijah, irin wannan fadowa ai se ki karya ni, wai ke bama ki san kin girma bane?" Ummi ta fada cikin dariya itama tana rike ni a jikin ta, gyarawa nayi na zauna kusa da ita kamar zan koma cikin ta na kwantar da kaina kan kafadar ta ina fadin "Nayi kewar ki ne sosai Ummi na, wata uku fa rabon da nazo naga Ummi na ai nayi kokari". "Ba wani kokari, mu da ada mace se tayi shekara bata je gida ba in ba wani abun ne ya faru ba". Zaro ido nayi, shekara, lallai "Tab wallahi ba zan iya shekara banzo gida ba, waiiii". Hararata Ummi tayi "To in ba'a barki ba ya zaki yi ai dole ki zauna". "Ai ko daga wajen aiki ne se na biyo, yanzu haka fa Salees be san zan zo nan ba, kawai na kasa daurewa ne na biyo". Ban san abinda ya kaini da shegen surutu na na fadi haka gaban Ummi ba bayan na san halin ta, aikuwa ture kai na tayi da sauri daga jikin ta lamarin da yasa gaba na ya fadi ga kuma amon muryar ta cikin ban umarnin in juyo gare ta cikin tune me shaida sam babu wasa a tattare da ita. Matsawa nayi daga kusa da ita da dan sauri kadan dan Ummin mu na da saurin hannu wataran duk da bata fiye yi min ba amma ina shakkar bacin ran ta "Kika ce ba da sanin mijin ki kika zo nan ba?". Yadda nake raba ido a wajen zaka dauka kisan kai nayi dan Ummin mu bata wasa da yaro akan gaskiya, duk shirin da kuke da son da take nuna maka baze hana ta rikide ba a take. "Uhm ko na tambaye shi baze bar ni bane Ummi". "Okay se hakan ya zama excuse din da zakiyi satar fita?, Saboda kina takamar kina aiki ko?, Ita yar uwar ki ba haka take zaune ba, ko kuwa kin fita iya son gida da iyaye ne?". Da sauri na girgiza kai alamun a'a kana murya na rawa na shiga bata hakuri, aikuwa na sha fada kafin ta hakuran sannan ta ora da nasiha kan biyayya da hakuri cikin zamantakewar aure. "Ummi wallahi na gaji da zaman gidan nan, jiya zuwa yau ne fa kawai nayi farin ciki amma kusan kullum cikin damuwa da bacin rai nake". Shiru Ummi tayi bata ce komai ba se tsura min ido da tayi, ban so na fada mata ba dan nasan zata damu amma waye nake dashi bayan ita, uwa tafi kowa fahimta da kuma sauraren ya'yan ta haka kuma cikin hikima da basira zata kwantar musu da hankali, duk da mun yi magana da Abba har naji sauki sedai ba kamar Ummi ba dan Abba da yace ze kira ni da safe be kira ba, nasan kuma ba komai yake gudu ba face ji na cikin tashin hankali, sedai nasan da Ummi ce wallahi se ta kira ni, ba kira ba kiraye kiraye ma dan uwa daban ce, ina son iyaye na duka amma matsalar mace a gidan aure yar uwar ta mace ce kawai zata fahimta. "Akwai abinda ke faruwa wanda ya kamata na sani ne Dijeh?" Seda na sauke ajiyar zuciya kafin na shiga bayyana mata halin da nake ciki, sedai dole na boye wasu abubuwan dan nasan ze sa Ummi taji haushin Salees sosai wanda maybe har mu shirya ita tana kallon shi da abin, ba kuma wai Ummi bace kadai haka duka iyaye suke so pls yan uwa mu dinga sanin iya abinda zamu fada a gidan iyayen mu. "Ki kara hakuri khadeejah, ina da tabbacin Allah baze bar rayuwar ki haka ba insha Allah, ki cigaba da kau da kai akan shi da matar shi da an shi, ban da daukar hudubar banza duk da nasan ba kawaye ke gare ki ba, amma zuciya ma na iya kai mutum ta baro, ki rike addu'a da karatun Kur'ani, komai yayi zafi maganin sa Allah, nima ina ta taya ki kullum, insha Allah Allah zai dube ki da duk ma masu iri matsalar ki". "Ameen Ummi na Nagode sosai". "Se kuma batun gudun mijin ki, kar in kuma jin wannan shashancin a wajen ki, ban sani ba ko sakarcin autanci ke damun ki, wataran in kika yi wani abin kamar in zane ki, nasan kin sani amma bari na tuna miki duk randa kika bijirewa bukatar mijin ki zaki kwana ne Mala'iku na tsine miki in har baki roki gafarar sa ba, dan haka umarni ne na baki in kin koma kije ki bashi hakuri kuma ban yarda ki bar shi ba har se kin tabbatar ya hakura, ban da wautar ki khadeejah ai ita mace zata iya kwatowa kan ta daraja cikin ruwan sanyi batare da tashin hankali ta hanyar irin haukan da kika yi ba, ga kuma kishiya a kusa dake da take jiran kowace dama dan sake karbe miki miji amma baki lura ba". Haka Ummi tayi ta min nasiha tare da karin tips din kula da miji iri iri, kar kuyi mamaki dan dama ni bani da kawaye, Ummi ce kawata ita da salima haka kuma itace uwata, wajen shawara ta bani wajen gyara tayi min wajen fada ma duka haka. Kayan gyara masu kyau da inganci ta hado min na karba cike da godiya dan Ummi tsohuwar likita ce, komai zata yi tana yin wanda tasan baze zama illa ga lafiya ba, shiyasa tun muna gida ta ora mu kan akidar fruit dan tace babu abinda ya kai shi amfani jikin ya mace shiyasa har yanzu ya bi jikina kullum se na sha shi kafin na kwanta. A sanyaye na ke tuki dan fa Ummi bata bar ni na wani zauna ba, kwata kwata ko minti talatin ban rufa ba ta kore ni da tsattsauran gargadi, kalaman ta nake tariyowa lokacin da ta rako ni compound "Ita mace nasarar rayuwar ta shine gidan miji Khadijah, nasan bakya jin dadin zaman sedai hakuri zaki yi dan bake kadai ke irin wannan situation din ba, bar ganin taki Kaddarar wallahi da za kiji ta wata se kin ji taki shafar mai ne, se kin ji ke taki ba komai bane compared to ta wata, so ki godewa Allah da niimar da yayi miki ki rike ta hannu bibbiyu ki cigaba da hakuri, masu irin Kaddarar ki da yawan su wasu na gidan iyayen su, ba dan komai ba se dan sun kasa hakuri, ko kuwa an kasa hakuri dasu, ke kuwa kin yi hakuri wanda shine ya zaunar dake har yanzu, haka shima Salees ya yi hakurin da ba kowane namiji ze iya ba saboda abin yayi masa yawa, ga iyayen sa da yan uwan sa basa son ki, ga Kaddarar ki sannan kuma kema se ki basu gudunmawa wajen kai shi bango har se an zo an yi batacciya Khadijah?, Ko kuwa kin daina san Salisun kin ne?". Nayi dariya tuno yadda ta karasa cikin zolaya, na sauke numfashi ina yin alkawarin cigaba da hakuri da kau da kai insha Allah ko dan Ummi na, na lura bata san duk abinda ze raba ni da aurena, a ganin ta maybe ba wanda ze yarda ya aure ni bayan yasan bana haihuwa shiyasa take ta kara min kwarin gwiwa da tausa ta dan na rayu gidan Salees. Da wannan tunanin na karasa gida na kashe motar tare da fita zuwa gida, a falo na same su gaba daya Salees har ya dawo, cikin murmushi na masa barka da gida na wuce ban kalli Mariya ba. Ina shiga shima ya shiga dakin, ban kalle shi ba na shiga cire kayan jiki na har na gama na daura towel, ta bayan sa na zagaya na rufe kofar da ya bar mana a bu e sannan na karasa gaban sa na zuba masa narkakkun idona wanda na shanye shi ina langwabar da kai gefe, lamarin da yasa Salees kasa cewa komai ya shiga kallo na kawai "Wanka zumaaa naaaa". Na fada a narke cikin wani salon murya, ban yi wata wata ba na ja hannun sa zuwa bathroom dina, tare mukai wankan ina bada hakuri a aikace, ko da muka fito tuni na ruda Salees ta yarda ya kasa jurewa bare daure alkawarin sa ya shiga min wani salo ne rikita walwa nima kuma ban yi kasa a gwiwa ba na taya shi yadda yake so har ma fiye, bayan mun sake wanka kan gado na fada dan na gaji matuka gaya, shima bed din ya biyo ni tare da daga ni gaba daya ya dora kan chest din shi ya na shafa gashi na dana busar, duk shiru muka yi se sautin bugun zuciyar juna da muke ji kafin a hankali na ji muryar Salees di na "Nagode sosai khadeejah, Nagode matata, Allah yayi miki albarka". Murya ta na rawa na amsa da Ameen dan ba abinda ya fado min rai se shekarun baya da muka wanzar da tsantsan so da kauna a zaman mu, haka Salees ke min wannan godiyar duk lokacin da ya samu nutsuwa dani. "Na san ni me laifi ne, na san ina bata miki sedai wallahi kin ji na rantse khadeejah ban san me nake yi da yake bata ran
Chapter 23 · 0% Book details