Sashe 46
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
doguwar fuskar sa, a gaggauce na sauke idanu na daga kan fuskar sa saboda kwarjininsa da ya dake ni hakan kuma ya bani damar ganin gangar jikin sa. Dogo ne shi irin na sosai din nan, ba siriri bane dan a murje yake hakan yasa tsayin nasa zanowa me fasali haka kuma abin sha'awa, sedai duk tsawon sa a tsaye yake kyam alamun cikakken namiji haka kuma dukkan wata kirar maza ta bayyana a tattare dashi. Gaba daya wannan kallon a cikin sakanni nayi masa su ina mikewa da sauri dan girmamawa, ban san waye shi ba haka kuma nayi mamakin zuwan sa wajena dan in ma guest ne to bani ya kamata ya gani ba sedai na bar shi as ko an masa kwatance ya kuskure ne hakan yasa na mike dan girmama shi "Pls have a seat Sir". Na Yi amfani da kalman sir ne dan ban san sunan a ba a ganina kuma is not polite to call him Mr. Cikin wnai irin taku ya shiga heading to kujerar da na nuna masa lamarin da ya tilasta min sake kallon fuskar sa sedai wannan karon maimakon cikin idanun sa se na sauke duba na kan kyakkyawan sajen sa da yasha gyara yake kyalli da daukan ido shedar yana samun gyara matuka, wani irin urge nake ji na son kallon kan sa dan ganin gashin kan sa yaya yake sedai na danne da sauri ina ambata auzubillahi minash shaidanir rajim a raina. Wani irin zama yayi na ban mamaki amma se n share nayi kamar ban gani ba na koma na zauna nima kafin in a polite manner na tambaye shi "How may I help you sir". Shiru yayi min har seda na sake maimaita tambaya ta kan cikin wani tone me cike da kamewa hadi da tsare gida ya yi min wata bahaguwar tambaya "Your name?". Kamar in ki amsa masa se kuma na dan saki murmushi bayan nayi tunanin ko so yake yaji in ni yake nema "Khadeejah Ma'aruf Nasidi". Nan ma se da yayi shiru kafin kuma ya mike ya fita in da ni kuma kamar shashasha nabi bayan shi da kallo baki sake ina tunanin wane irin mutum Allah ya hada ni dashi yau ni kuwa?. Kusan minti uku ina zaune baki sake ina bin kofar da ya fita da kallo kafin na iya rufe baki na na maida hankali na kan system din sedai sa'i da lokaci na kan kalli kofar da tun da ya fita ya rufe min ita take a kulle. Karfe sha daya da rabi muka nufi hall gaba dayan mu inda a nan za'a yi meeting da general head da se yau ya sami zama da mu, baki na dauke da boyayyar sallama na shiga hall din, kujerun wajen adadin ma'aikatan dake ma'aikatar ne excluding irin masu share share da goge goge and the rest, kujera na samu na zauna ina aje yar ipad dina kan table din gabana. Se da aka zzzauna kafin muka ji gyaran murya with a matured tune hakan yasa duk muka sake shiga nutsuwar mu, for the second time wannna sassanyan kamshin ya sake kai wa hanci na ziyara, wannan karon lumshe ido nayi ina shaka dan yadda turaren yayi min dadi na dade ban ji bakon kamshi me dadin sa ba. Tattausan Muryar sa yet cike da bossing ya fara magana cikin welcoming din mu kana ya fara addressing din mu, shiru kowa yayi muna sauraren sa cike da nutsuwa, irin yadda turancin sa ke fita fluently with Fulani ancient dole ya burge kowa, awa daya meeting din ya dauka ya sallame su bayan ya bada damar kowa yayi introducing kan sa hakan kuwa muka yi tare da fadar post din da yake kai. Ko da na koma office na dade ina mamakin me ya kawo general head office dina, hankali na be kwanta ba se da naji ashe ba office dina kadai ba ya shiga office din duk wani sabon zuwa. Ranakun da suka biyo baya aiki muke tukuru dan kuwa boss din mu ba shi da wasa kan aiki, in kuna jin workaholic to shine, ina zaka aiki, daga ina kake aiki, me kake yi aiki, me zaka yi aiki, komai aiki, ni har mamaki nake in yana da lokacin wani abu bayan aiki, Allah ya dasa min shakkar wannan bawa ta yadda har bana san abinda ze hada hanya ta da tashi dan kuwa kwarjinin sa ba karamin duka na yake ba. Yau ma dan ba yadda zan yi na hada files din da dole se na kai masa na fit heading to his office, kamar me tsoron duka haka nake sanda a corridorn har na kau gaban office din inda aka rubuta boldly "IBRAHIM ABDALLAH MAIDOKI". A fili na karantawa sunan na sake maimaita wa kafin na tabe baki kana na maza na gyara sannan na shiga knocking, kasa kasa na ji muryar sa na amsa min da "Yessss". Irin yadda ya fadi yessss din kamar wani wanda yayi aikin karfi ya gaji lilis, not minding hakan na tura kofar na shiga with my little sallama a baki na, ban jira jin ya amsa ko be amsa ba na karasa gaban table din sa na ajiye files din hannu na na koma gefe ina jiran ya gama phone call din da na same shi yana yi dan na masa bayani "Dada is sorryyy, no I'll be coming back today insha Allah". Ya fada can kasa, "I missed you more Haanah, where's my Meerah and pretty?". "Is okay, I'll be back today, I promise". "I love you more dearies, byee". Kaman dole haka na tsaya ina sauraren sa har se d ya gama wayar da yake yi wanda tsabar yadda yake magana yayi baya yi ba se da nayi kusan minti biyar a tsaye ynaa fadar iya wancan sentence din na sama. "Here's the list if files you asked for sir". Gyada min kai kawai yayi lamarin da yasa takaici ya cika min ciki, yanzu duk tsayuwar da nayi dama gyada kai ne kawai amsa ta, lallai mutumin nan karshe ne. Fita nayi ina tafe ina kunkuni abina har na kai office, daga nan kuma wani abu be kuma hada mu ba. __________ Watan mu hudu kenan da kama aiki a garin Bakwarni, matsaloli kamar sun tafi ashe wanda suka fisu na gaba, a zaman da muka yi a nan har na manta da damuwoyi na na saki jiki dan babu Mariya babu Hajiya Iya babu kuma su Amir an hada husuma. Sedai tashi daya wai se ga wani sabon zance, ba'a kawo maganar ba se da muka je Darma yin hutun sallah, cikin farin ciki nake bin ko ina da kallo da tunanin zan je in ga Ummi na in kuma zagaya dangi, aikuwa haka nayi din dan naji dadin sallar ba kadan ba, na gama zagaye na kana muka hau shirin komawa dan hutun mu ya kare se kuma ga wani sabon tsari daga Hajiya Iya. Wai ai ni a nan zan zauna Salees ya tafi da Mariya dan baze yiwu yaje ya tare da ni ba alhalin babu abinda na aje ban da in ci in kasayar so wannan karon ni zan zauna da yara su kuma su tafi, gaba daya am confused jin wata magana kuma, wai shikenan ni mutanen nan ba zasu bar ni in samu kwanciyar hankali ba. Duk yadda naso in fahimtar da matar nan taki dan rantsuwa tayi ba za'a bar Mariya ba a gida, nima kuma a wannan karon nayi rantsuwa ba zan zauna ba dan ba abinda ze sa na zauna nan alhalin aiki na yan can, wannan ma bame yiwuwa bane. Haka dole Salees ya tarkata mu muka tafi mu uku, ni dashi da Mariya se kuma Amir, Sahal da Ilham kuma aka bar su wajen Hajiya Iya saboda karatun su. Base nace muku komai ba kan zaman dan kuwa rayuwa da Mariya kun san se hakuri kawai, ana dai malejin rayuwa kawai, yau dadi gobe akasin haka har muka kuma shafe wasu watanni biyun, anan ne kuma Kaddarar mu ta tsaya. Tun zuwan su Mariya d sati Uku Amir ya fara rashin lafiya sama sama, da farko Mariya bata dauki abin da wani mahimmanci ba ta rin ga bashi magunguna batare da anje asibiti ba, wasa wasa ciwo ya fara karfi a jikin yaro hakan ne yasa ta sanar da baban sa nan suka tafi asibiti, bayan series of test likitoci suka ce basu ga komai ba amma suka ba su magani aka dawo aka cigaba da sha, maimakon sauki ya samu se ciwo ya cigaba da gaba, gashi kuma duk asibitin da suka je se ace ba'a ga komai ba lamarin da ya daga hankalin Mariya da Salees tun bare ganin yadda yaron ya kare ya tsiyaye, hakan yasa suka buga waya gida suka fada aka fara yawon neman na Hausa aka aiko kanwar Mariya ta kawo, ta bangaren Hajiya Iya itama Hannatu ta kawo sedai duk a banza. A lokacin ne suka fara rade radin ai nice na kama yaron tun da ban so dawowar uwar sa nan garin ba dama ni mayya ce, hakan yasa aka koma karbo maganin maita sedai kwana biyu da fara amfani dashi aka tashi ba yaro, YA MUTU!. Anan ne cikakken tashin hankali domin kuwa ba su Hajiya Iya da Hajiya Ramatu ba, wannan karon har da Salees a masu yarda ni na kashe masa da, a farkon maganar ban famuyba sanin shi wanda ya aje ni yasan wace ni sedai awanni kadan kafin Amir ya mutu Salees ya same ni a daki na dawo daga aiki dan duk abinda ake ban fasawa zuwa aiki na ba dan na sawa raina akan su ba zan yi asarar means of earning dina ba, so ranar na dawo na wuce su a falo, Mariya da Hannatu da Safiya suna ta kokarin ganin sun durawa Amir maganin dan baya iya sha da kan sa, daga sallama ban sake ce musu komai ba dan ko nayi magana basa amsa min, ina aje jaka ta kan gado se gashi ya shigo a fusace yana buga min kofa, dan turus nayi ganin yadda ya shigo a fusace yan huci kamar wanda ya hadiyi garwashi so se