Sashe 30
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
da tsananin farin ciki da jin dadi, se kuma nayi saurin yin baya jin sautin yaran na fadin "Oyoyo Daddy, oyoyo". Se lokacin na kula tare suke da maman su, yo Ina na kula, ganin miji na ya mantar da ni kowa, daya bayan daya ya daga ya'yan suna dariya yana amsa musu sannun da suke mishi, daga karshe ya karbi Amir a hannun Mariya muka taka cikin falon gaba daya muka yi masauki kan kujerun wajen. Sannu da zuwa muka shiga sake yi masa yana amsa wa cike da walwala haka kuma muka dora da hira gaba daya wadda sa'i da lokaci Mariya ke kokarin zare ni cikin su sedai yaki bayar da kofar hakan, ko akan yan uwan ta tayi magana se ya sako ni nima kuma bana gwale shi zagawa nake na amsa shi, na kula hakan ba karamin batawa Mariya yayi ba, wanda dama tun da taga yadda muka dinke da Salees yake gudun bacin rai na kamar farkon shigowar ta cikin mu shikenan ta rasa walwala. Yanzu ma tashi tayi ta tafi daki ta kwanta wai bata jin dadi kan ta na ciwo haka kuma tana ganin jiri, sannu duk muka yi mata yaran suka bi bayan ta nikuma na wuce dakin Salees ya biyo ni dan yin wanka da kuma samun hutu. Duk yadda nake son kwalliya ta seda Salees ya bata min dan dagewa yayi tare zamu yi wanka, haka ba yadda na iya na biye masa, muna fitowa na wuce dining na kwaso abinci na kawo masa saboda yadda yake ta kiran yunwa yake ji, ashe fitowar da nayi Mariya ta gan ni, zuciyar ta ta kuma cunkushewa da bacin rai na gani na da towel kai na a jike, ita a tunanin ta wani abu ne na daban niku wa ba da gangan nayi ba kaya na ne ya jika min wajen wanka gashi kuma ya ruda ni da kiran yunwa shiyasa ba shiri na dauro towel na fito. Cikin annashuwa nake kallon sa yana cin abinci a nutse, irin yadda nake farin cikin zaman lafiyar mu wallahi ba zan iya kwatanta wa ba, ganin yadda na tsare shi da ido yasa ya dago kai ya kalle ni tare da dage min gira daya "Ya dai yan mata, irin wannan kallon haka kamar za'a cinye ni?". Murmushi nayi me fadi da yasa ha ora na bayyana "Kawai inq tunani ne". "Tunanin me kunq bayan gani a gaban ki". "Tunanin rayuwa zuma na, irin yadda muka samu kwanciyar hankali se nake jin ba abinda ya kai hakan dadi". Seda yayi dariya kafin ya kashe min ido cikin tsokana "Ke dai fadi gaskiya, kina tunanin rayuwa babu ni ne, uhm fada min". Nima dariyar nayi "To meze raba mu balle har in yi tunanin rayuwa ba kai?". "In ba rabuwa fa akwai mutuwa Khadijah, kin san wannan?". "Na sani sosai Salees sedai ina fatan Allah ya dauke ni kafin kai dan i can't imagine a life without you, beside haka kana da wasu rayukan da kai ne jigon su ba kamar ni ba da ban aje komai ba, rabuwa kuma, hmm bana zaton akwai wannan kaddarar a tsakanin mu". Aje spoon din hannun sa yayi ya zuba min ido har na gama magana kafin cikin serious tone yace "Rabuwa tsakanin mu itace zata zama mafi munin kaddara da bana fatan kasancewar ta a gaske, dan Allah kar ki kuma kawo wannan maganar a ran ki ko da kuwa a mafarki ne". Kallon sa kawai nake zuciya ta na bugawa saboda tuno wani incident da ya faru shekaru tara da suka wuce, wani irin faduwa gaba na yayi kamar a lokacin abin ya faru, irin yadda na runtse ido tare da dafe kirji yasa Salees saurin riko hannu na a rikice "Lafiya kuwa Deejah, me ya same ki?". Seda nayi dan sakwanni kafin na bude ido na kalli Salees murya ta na rawa "Shekaru tara da suka wuce, salees anya......". Da sauri ya rufe min baki yana girgiza kai kamar shima ya rude "Kar ki karasa, a wancan lokacin na sharrin zuciya ne da kuma zuga, bayin kai na bane ba Deejah, dan Allah ki daina tuna min da mafi girman kuskure na". A hankali na cire hannun sa daga baki na ina gyada masa kai alamar toh. Gaba dayan mu jikin mu yayi sanyi amma muna kokarin ganin mun danne komai mun nuna ya wuce sedai har lokacin bugun zuciya ta ya kasa sasssaitawa balle ya daidaita. *BURAIMA QUARTERS, BAKWARNI STATE* Plat e din da ta gama cin abinci dashi ta dauko zata kai kitchen, tsaya wa tayi ganin yadda yake sanda zai fice kamar wani barawo, takawa ta shiga yi har ta kai bayan sa daf sannan ta tsaya kana ta ambaci sunan sa cike da mamaki "Dada". A firgice ya juyo yana kallon ta ido waje se kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da sa hannu a bakin sa ya mata alamar tayi shiru, seda ya kalli babban falon ya ga babu kowa sannan yaja hannun ta da sauri suka shige kitchen din ya bude kofar suka fita compound ta cikin kitchen din. Ajiyar zuciya ya sauke kana ya sake mata kyakkyawan murmushin da bacin ya'yan sa da iyayen sa ba wanda yake samun alfarmar ganin sa balle ace shi a ka yi wa. "Dada lafiya kuwa?". "Where's pretty". Ya fada da dakakkiyar muryar sa yet kuma me taushi "Tana shirya wa ne Dada, wani abu ya faru ne?". "Wa ita nake wannan sandan, bana so ta ganni dan kin san rigimar kanwar ki, da kyar tayi bacci da dare wai ita a kai ta Maamah". Ya karasa sunan in a bitter tone haka itama matashiyar take yanayin fuskar ta ya canja daga mamaki zuwa alhini da damuwa...................... Ouummey