Sashe 29
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wattpad @ouummey Ouummey 10 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Ten_ Hajiya Falmata da Hajiya Farida sanannu ne a kungiyar saboda irin gudunmawar da suke badawa, ba wai sun fi kowa taimako d kudi bane, a'a irin matsalar da Falmata ke ciki da yadda take da jarumta da juriyar mai da komai ba komai ba yasa ka bata mukami dan na kasa suyi duba izuwa ga rayuwar ta su kuma yi koyi da tawakkali hadi da karfin zuciya irin nata. Kamar ko da yaushe yau ma cikin nasara aka gama gabatar da meeting din, inda yau taimakon nasu ya karkata ne kan wata mata da ke da matsalar karin mahaifa da ya hana ta haihuwa gashi kuma mijin da iyayen ta ba masu karfi bane hakan yasa jin labarin kungiyar da irin taimakon da ake yi a cikin ta yasa ta kawo kanta haka kuma aka saurare ta duk da bata kasance wata hamshakiyar me kudi ba, ba kuma wata celebrity ba haka kuma ba wata kusar gwamnati ba, motto din kungiyar shine mu'amala da kowa with equality, babu ruwan su da mai kudi ko talaka, abinda suka sani shine they all are one family and have almost similar problem so they'll come together in finding a solution. Miliyan uku da rabi ake bukata domin aikin dan abin yayi worsting ta yarda har ya fara neman lalata mahaifar hakan yasa ake bukatar aikin urgently, wani abin burgewa shine a wannan zaman da suka yi da kowa be san za'a iya kawo matsala ba se gashi tashi daya har an hada miliyan biyu da rabi, inda wasu suka karbi bank account na kungiya domin sending kudaden wasu kuma suka tura, abinda be isa ba za'a cika a asusun kungiya. Compound din building din tuni ya cika da kayayyaki, kayan masarufi, kayan amfanin mata kama daga kan sabulai da turarukan wanka, kayan sawa, mayukan gyaran fata da gyaran gashi, takalma, kai abubuwa dai da yawa da mace zata bukata na gyara daga wajen mijin ya, ba mutum daya ne ya kawo ba, kowannen su kan zo da abinda Allah ya hore mishi ne in aka hada se a raba, suna yin hakan ne dan ragewa mata takaicin namiji da wani baze iya bada kudin gyaran jiki ko wani gyaran gashi ba, musamman ma masu irin matsalar su da mata ke kallon basu kudin gyara ko wani abu as a waste of resource. Kowanne ka kalla fuska cike da farin ciki ana wasa ana dariya suka rabu, Falmata cikin ranta bata ji dadin yadda abun ya zo mata cikin rashin ku i ba sai dai taji dadin yadda yar uwar ta kuma aminiyar ta Farida ta rufa mata asiri domin kuwa ashe kayan masarufi ne cike damkan a bayan motar ta bayar da sunan Falmata. Gida ta mai da ta bayan sun zagaya gari duk saboda tayi lightening mood din Falmata wadda duk abinda Farida ke yi ta na ankare haka kuma zuciyar ta cike take da matukar godiya ga Allah bisa kyautar wannan rai mafi tsananin so, kulawa hadi da tausayi gare ta, bata san me yasa ba se take jin wani matsananciyar kewar Faridan tare da ita duk da gata a gefen ta suna tare. Har bedroom Farida ta rakata, duk yadda take fada mata ita fa lafiyar ta lau bata bar ta ba se da tayi wanka ta canja kaya gaban ta ta ci abinci sannan ta kwanta kana hankalin Farida ya kwanta har ta iya ta mata sallama ta tafi nata gidan. Kallon Hassana tayi dake zazzage karamar akwatin yan kunnen ta, wani babban saiti ta dauka me hade da awarwaro, zobe, sarkar kafa da kuma zobe, jujjuya su tayi kana ta dauka ta sa a handbag din ta dake gefen ta kana ta umarce ta ta maida ragowar, cike da dimbin mamaki Hussaina ke kallon ta wanda duk Farida na hankalce amma se ta nuna kamar bata gani ba ta mike tare da nufar bedroom din ta tana umartar Hussaina da ta bi bayan yar uwar ta su kwanta se kuma gobe, haka dole ba dan taso ba Hussaina ta yi dakin su ranta cike fa mamakin me maman ta zata yi da babbar sarkar auren ta, sarkar da iya rayuwar ta zata iya fadar so nawa ta sa ta saboda son da take mata. Washegari tana tashi Falmata ta fara kira, jin ta garau yasa hankalin Farida kwanciya sannan ta gabatar da ibada ta koma baccin da bata samu yi da wuri ba saboda tunani. A hankali na kashe datan waya ta fuska ta dauke da madaukakin farin ciki, a duk lokacin d nake kallon mutanen nan ta cikin waya ji nake kamar na budi ido na ganni cikin su, wata irin kaunar su nake ji kamar irin yan uwa na ne na kusa kusa, na san ba komai ke sa min wannan feeling din ba se dan ya kasance matsalar mu iri daya ce dasu, damuwar mu iri daya ce sedai wata tana fin wata samun kwanciyar hankali. A duk sanda nake kallon su wani irin kwanciyar hankali nake samu da nutsuwa sanin ba ni kadai Allah ya jarraba da wannan addarar ba muna da yawa haka kuma ina karuwa da shawarwari da nasihar da ake yi a karshen meeting din. A kalla shekara goma sha daya kenan da nayi joining kungiyar NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS, yaya Salima ce ta ga sunan kungiyar a facebook lokacin bata bunkasa haka ba se kuwa ta fada min tana yabon yadda suke gudanar da tsare tsaren su, aikuwa ban yi sanya ba bayan tafiyar ta nayi searching sunan kungiyar na kuma gan ta, ban gushe ba se da nayi wa daya daga cikin admins din magana privately ita ce ta fada min dukkan procedure din da zan bi wajen yin register haka kuma nayi. Takaici na daya da ya zama kungiyar tana garin Bakwarni ne ni kuma ina garin Darma ne so ba ta yadda zan dinga attending meetings din su, lokacin da aka kawo shawarar yin live vedio yayin meeting din ba karami dadi naji ba, tun daga lokacin kuma ban taba missing ko daya daga cikin meetings din ba, haka kuma sanadiyar watsapp group da kungiyar ke da mata da yawa sun kulla zumunta tsakanin su, nima akwai wata Zuhra da muke so close da ita saboda yanayin yadda naji Kaddarar ta kamar tawa har kuwa irin dangin miji da surukar da Allah ya bamu. Numfashi na sauke tare da tashi zuwa kitchen bayan nayi offing data na, yau girki na ne gashi kuma me gidan yayi tafiya se yau ze dawo shiyasa zan shiga kitchen da wuri dan sama masa abin tarba. Kusan wuni nayi cikin wajen ina aiki, dishes kala kala na hada wanda nasan miji na na so kuma ze yi farin ciki in ya gani, seda na jera komai a dining tare da yin decorating sannan na tafi daki dan yin wanka. Staright gown na saka na wani dark purple material da ya sha wani azababben dinki, ko ta ina jikin rigar stones ne sune shining suna daukan ido, yadda rigar ta kamani kam yasa na tabbatar eh nayi kiba fa dan last sawar da nayi mata bata kama ni haka ba. Light purple head nayi anfani dashi na kafa a kai na ta yadda ya zauna sosai kai kace a haka yake tun ainahi, turare kuwa kamar wadda nayi wanka dan bana iya kirga adadin turaren da nayi wa kaina feshin, kawai duk wanda naji kanshin sa ya min dadi orawa nake kan na baya. Falo na dawo na zauna ina dan girgiza kafa ta tare da taunan cingum a hankali, duk wannan kwalliyan fa ba komai a face na ban da powder da kohl se mascara kawai, ba dadewa kuwa naji shigowar motar da driver ya je dauko shi, cike da madaukakin farin cikin da na kasa boyewa na tashi zuwa bakin kofa na tsaya dan na kasa tsayawa jiran sa, kwana ukun da yayi baya gida se naji tamkar mun shekara uku ne bamu ga juna ba, ni kai na wannan zumudin nawa akan Salees na bani mamaki, sedai na fi dangan ta hakan da yadda muke zaune lafiya kalau cikin kwanciyar hankali tun bayan alkawarin da yayi min wanda kusan two month kenan yanzu baya, daga Salees dai ban kuma ganin wani abin bacin rai na azo a gani ba se wanda ba'a rasa ba na yau da gobe wanda shima mostly akan ya'yan sa ne dan Allah ya jarraba Salees da mugun so da gudun zuciyar ya'ya wanda nake jiye masa wataranan da idanun su shida mahaifiyar yaran ya rufe basa hango ta. Daga wajen Hajiya Iya da yan uwan sa ne kan nake Fuskantar Matsala dan sun matsa min a kwanan nan, har gidan nan suke zuwa su ci min mutunci yadda suka so, ba yadda zan yi haka nake shanye wa nake kuma hana kai na damuwa tun da dai muna zaune lafiya dashi. Maybe ku ga rashin zuciya ta akan nacewa zaman gidan Salees sedai ba naci bane, sanin ciwon kai ne da kuma biyayyar iyaye domin a kullum Ummi na na fada min babu suturar da ta kai ta aure wajen ya mace, gidan miji shine bigire mafi daraja a wajen mace haka kuma shi mijin shine rai mafi girman biyayya, taya kuke tunanin zan biye wa zafin zuciya da bacin rai wajen yin fatali da nasihar uwar da na tabbatar tafi kowa so min kwanciyar hankali da zaman lafiya.....?. Rundunar da Salees yayi min ce ta dawo dani hayyaci na, ban yi wata wata ba nima na bude hannaye na na zagaye shi dasu cike