← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 48

Sashe 12

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

sanyin kanshin da baya tashi sannan na dau waya ta da karamar purse dina na fita, basa falon hakan yasa na fita compound bayan na rufe kofar falon. A tsaye na hango Salees jikin motar sa wadda ina fitowa ya bude ya shiga, takawa na shiga yi zuwa wajen su sedai kafin na karasa ya ja motar sa yana yi wa maigadi horn ya bude gate tsayawa nayi kallon ikon Allah se kuma na bar shi as tun d ta kusa dani zai wuce maybe ze tsaya in shiga, "Motar ya cika, ki biyo bayan mu a naki tun da kina dashi". Sakatoto nayi ina bin shi da kallo kafin kuma na kau da mamaki da sauri dan wannan kadan ne daga halin shi, shi in har kuna fada to fa ba zaki kuma jin dadin sa ba, duk yadda ze bata wa mace rai to se yayi so tuna haka se kawai na saki murmushi me kyau na gyada kai na alamun toh na juya zuwa wajen mota ta. Farin ciki na daya , kamar yadda yace ina da motar, mota kuma ba karama ba domin suna gogayya da tasa a wajen kudi, bangaren tashe kuwa har ma tawa ta zarta tasa, ina tsananin so da kaunar motar domin kuwa Abban mu da hannun sa ya bani kyautar motar lokacin da Mariya ta haifi Amir wata shida da suka wuce. Cikin tuki na na natsuwa na fitar da motar daga gidan tare da hawa titi na nufi babban gida kamar yadda suke kiran family house din su inda nan ne iyayen Salees suke. Gefe da tasa motar na aje parka tawa sai dai ban fito ba sai da na gama addu'o'i na na samun rinjaye kan makiyi dan kusan zance makiyan nawa ne mutanen da zan hadu dasu. Bakin babban falon Hajiya Iya nayi sallama tare da daga labulen na shiga bayan na sabule takalman kafa ta, a duk cikin mutane takwas dake zaune a falon ba'a sami ko daya da ya iya amsa min sallamar da nayi ba wanda hakan ba bakon abu bane a waje na, gefen one sitter na samu na zauna kana na shiga gaida Hajiya da ta nuna kamar bata san da shigowa ta ba tana yi wa Amir dake hannun ta wasa, seda na maimaita gaisuwar sannan ta amsa min a watse. Daga Lafiya lau din bata kuma cemin komai ba nima kuma naja baki na nayi shiru, sai da ta gama da shalelen ta sannan ta mikawa Hannatu kanwar Salees dake zaune a wajen Amir kana ta fuskanto mu gaba daya. "Uhm, kace mene?". Dan muskutawa Salees yayi ya fara rattabo zance kamar me karanta labari "Hajiya karar khadeejah na kawo miki, ban san meke yawo a ranta ba, ban san wake zuga ta amma gaba daya ta birkice, gaba daya ta canja halaye da dabi'un ta ta kwaso mugayen akidu da ra'ayi ta orawa kan ta. Babu damar naman Amir tayi wani abu yanzun nan se ta hayyako ta fara fadin maganganu marasa kan gado, kwata kwata bata neman zaman lafiya kamar yadda ita Mariya ke son su rayu cikin salama, a kullum burin ta ta kuntata min ta bata min rai. Duk ma kuma ba wannan ne babbar damuwar ba, kin ga yaran nan wallahi khadeejah yadda ta tsane su bana jin ko makiyin ta ta tsana haka, daga ni uban su har ita mahaifiyar su bamu san me mukai mata ba da take neman saukewa kan su. Shekaranjiya iIlham d zazza i ta kwana me zafi saboda yadda ta fasa mata baki ga kuma kunnen ta da ta murde saboda wai tayi mata rashin kunya wanda zan iya rantsewa baby ba zata yi haka ba sedai yarinta, wai kuma daga uwar ta ce ta dinga sassauta hukunci shikenan ta dau fushi da ita da yaran har tana tafiya wajen aiki ta bar baby bata je makaranta ba saboda tana tutiya da tinkahon baban ta ne ya sai mata mota, Hajiya Iya fa abubuwan da zan iya fada miki kenan kuma akwai wasu bayan su sai dai in zan zauna lissafa miki wallahi zamu wuni ba mu gama ba, shiyasa na kawo ta gaban ki ta fadi meye matsalar ta da ni, Mariya ko yayana".............. Ouummey Ouummey 05 {4/30/2023 }
Chapter 12 · 0% Book details