← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 48

Sashe 41

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wattpad @ouummey Ouummey 14 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Fourteen_ Daga aiki na taso a matukar gajiye, jiki na gaba daya ciwo yake min dan kwana biyu ina overworking kaina saboda gujewa tunanika ga kuma promotion din da ya matso sosai, yanzu haka gobe za'a sanar da sunayen wanda suka yi nasarar samun wannan cigaban, dukan mu ma'aikatan da muka san an yi nominating sunan mu cikin zulumi muke dan kuwa bama fatan list ya fito babu sunan mu, promotion abun farin ciki da so ne ga duk wani ma'aikaci, yanzu haka ji nake kamar in jawo gobe tayi tayi dan kawai in samu peace of mind. Mayafi na a hannu na shiga falon dan tun a kofar falo na cire shi saboda wani nauyi dana ji ya min, ba abinda nake bukata a lokacin kamar wanka da bacci ko naji daidai. Turus nayi ganin Hajiya Iya, kannen Salees Rukayya, Sadiya da kuma auta Hannatu se matar kanin sa Sani me suna Lubabatu, kanwar Mariya me suna Safiya, da yayar ta Safara'u se maman su Hajiya Ramatu. Ban san me yasa gaba na ya fadi ba ganin wannan taron sedai na daure na karasa falon ina kaiwa tsugunne na shiga gaida Hajiya Iya da bata amsa min ba se kare min kallo da ta shiga yi kafin ta karkata kai tana kankance ido "Wato yawon tambadewar da kike kenan kika fake da aiki, yanzu mayafin ma a hannu kike yawo dashi". "A'a a kofar falon nan na cire saboda gajiya". Na bata amsa kai a sunkuye "Uhmmm kowa dai yayi me kyau kan sa". Jin tayi shiru bata kuka cewa komai ba yasa na juya ga mahaifiyar Mariya itama na shiga gaida ta amma itama bata amsa min ba dan gara ma Hajiya Iya dan ita ko kallona bata yi ba se kau da kai da tayi tana jan tsaki. Lamarin ya daure min kai dan kuwa ba haka ta saba min ba, ko da ba haduwa muke yi masu wani frequently ba amma in dai na gaishe ta tana amsa wa ko da dai ba wani da tsayi bane dan iyaka ta da ita 'Lafiya' shine amsar gaisuwa ta d ita koyaushe. Cikin sanyin gwiwa na dan mike sannan na gaida yayar ta Safara'u, ban tsaya jin zata amsa ko kuwa ba na yiwa sauran magana wanda kannen Salees ne da matar kanin sa se kuma kanwar Mariya "Sannun ku da gida". Da sauri nayi gaba dan jiki na ba bani wannan taron bana lafiya bane, ga kuma kallon banzan da na lura duk suna bina dashi, wankan da nake dokin yi duk se naji ba zan iya ba, kawai so nake in San meke faruwa a gidan namu inda na shiga addu'ar Allah yasa ba shida alaka dani dan to be sincere tuni na gama gajiya da wannan tashe tashen hankulan, kwanciyar hankali nake bukata a yanzu. Kamar wanda aka karanta min se kalaman da kunne na suka jiyo min lokacin da nake bude kofar daki na suka dawo min cikin walwa "Hmmm, lallai mugu bashi da kama, kalli matar nan kamar wata saliha alhalin kungurmar munafuka kuma azzaluma ce, yanzu ban da mun san hali ai da se mu karya ta abinda muka ji da kunnen mu". Rukayya kanwar Salees me bi masa ta fada in da Safara'u ta cafe "Ke ni fa a wannan zamanin bana tantama kan duk abinda aka ce mutum yayi dan wallahi wani mutumin in zaki shekara goma dashi ba zaki taba sanin wasu bakin halin nasa ba se Allah ya ciyar dake, to balle kuma wannan matar da tun a baya bakin halin ta ya fito fil, kina zaton zata bar Mariya ne cikin kwanciyar hankali bayan Allah ya bata haihuwar da ita ta rasa?". "To wa ya hana ta haihun ita, aikin banza, Allah ne fa ya san nufin jaki da be bashi kaho ba, wannan da ta haihu ba musan me zata yi ba, a haka ma muna fama da ita, ai ni na godewa Allah da be Kaddara min hada jini da wannan bakar jarabar ba". Hajiya Iya ta fada tana wani tsuke baki, sauke numfashi nayi bayan na gama tunani na, lallai akwai wani abu, tabbas akwai sharrin da aka kulla min da har yaja min wannan bakaken maganganun sedai ina fata Allah yasa komai ya zo min da sauki ya kuma bani juriya da hakurin dauka. Da kyar na iya nayi wanka na canja kaya, yunwar da na shigo da ita kuwa tuni ta fece haka ma baccin da nake kuzun nayi shima duk ya yi nasa wajen, jira nake kawai in ji an doko min kira an fara tuhuma ta, dalilin tuhumar ne dai ban sani ba. Kwankwasa kofar da aka yi yasa na dan zabura kadan kafin na kurawa kofar ido, da kyar na iya mikewa naje na bude, kallo daya za'a min a san a firgice nake. "In kin ga dama ki fito Hajiya na magana". Hannatu ta fada min tana wani yatsuna fuska haka at the same time tana harara ta kasa kasa, tsabar kidima ko dankwali na da ya fadi ban tsaya dauka ba na bi bayan ta ina kiran Allah a zuciya ta. Wannan karon gaba dayan su ne a falon har da Mariya da Salees da kuma wasu mata biyu manya da nake kyautata zaton yan uwan ta ne dan ban san su ba cikin familyn Salees, kowanne ka kala fuskar sa a hade take babu alamun wani abu wai shi fara'a yayinda idanun su ke kara kaina a jiki na kamar zasu dauke ni da ido. Daga fuskar su zaka hango tsantsan hasssada da kishi ganin irin kirar da Allah ya zuba min, riga da skirt din jikina ya kama ni dam kamar yadda kayana suke dan faranta wa miji na, ban lura a haka na fito ba dankwali ba balle mayafi se da Hajiya Iya dai ta yi magana "Sannu isasshiya, hamshakiya mandiya, shima dankwalin kina jira yaron naki ya je ya dauko miki ne?". Gaba dayan su suka kuma watso min na mujiya lamarin da yasa naji na takura matuka, na mike da sauri dan daukowa se ta kuma dakatar dani "A'a koma ki zauna dan na tabbatar da kina sane kika fito, koma me kike so mu gani mun gani sedai Allah wadaran irin wannan kyan na dan maciji". Komawa nayi na zauna jiki na kamar an min duka, wai shi dai wanda baya sanka kome kayi se ya kushe, kome kayi baka iya ba, kuskure a wajen sa ganganci ne, Allah ka rabu mu da wahala Ameen. "Dago ki kalle ni nan Khadijah, ba na tsoran ki bana tsoran fada miki magana dan ba zan zuba ido ki cigaba da cutar min da da matar sa tagari ba uwar ya'yan sa bayan ke ko kara baki aje ba. Na dade da sanin ke din ba karamar muguwa bace munafuka kuma azzaluma tun lokacin da kika nemi raba ni da dana sedai Allah ya fiki ya tankwabar da mummunan nufin ki, sedai ban san rashin imanin ki har ya kai ace ki karbi maita dan cutar da matar Salisu ko yayan sa ba, kin yi asara, wallahi kin yi asara Khadijah dan kin dade da kwashe kayan ki daga gaban Annabi". Wani irin dam kunne na yayi, walwa ta ta dakata daga aiki, kwata kwata kaina ya toshe, gaba daya na daina ganewa d fahimtar komai da suka cigaba da fada se aikin kallon bakin su d ana cigaba da yi dan tun da Hajiya Iya ta ambaci maita na dago kaina daga sunkuyar dashi da nayi. Fiye da mintina biyar kafin walwa ta gama accessing all she've said, maita, na karbi maita, meaning suna nufin ni din mayya ce, mayya fa, innalillahi wa inna ilaihi rajiun. A lokacin wani irin Hajijiya nake ji cikin kaina, kaina ya shiga juyawa kamar wanda ake wujijjigawa, dakin ya shiga juyawa dani kamar zan kife yayinda kalman maita ya shiga yawo a kunne na, lamarin da ya tilasta min saka hannaye na toshe kunnuwa na tare da runtse ido na da sauri haka kuma at the same time Ina girgiza kan tare da furta kalman a'a, a'a da karfi cikin wani irin yanayi me ban tausayi ga masu zuciyar imani. A lokacin da na budi ido se gani na nayi kwance kan gado na Salees tsaye a kaina ya jingina da bango, nauyin da naji kaina yayi ya tilasta min mai da ido na rufe kafin kuma in a blink of an eye na sake budewa lokacin da tiryan tiryan abin da ya faru a falo ya dawo min kaina, a gigice na fara kokarin mikewa wanda hakan ne ya ankarar da Salees cewa na farka, da saurin sa ya matso ze rike ni na goce na nufi kofar da ke rufe wadda ake kan bugawa tare da kiran sunan sa, da sauri ya riko ni na shiga kokarin kwace wa "Ina zaki je haka a gigice, ki tsaya kar ki je ki fadi". "No, sake ni, ka sake ni in je in fada musu ni ba mayya bace, ka sake ni in ji me na musu da zafi da zasu hada ni da kalmar maita, dan Allah ka bar ni naje na musu bayani ko zasu fahimta suyi withdrawing wannan mummunar kalmar daga gare ni". "Naji zan sake ki, but first ki tsaya ki nutsu kar ki jiwa kan ki ciwo". Duk yadda Salees yaso dakatar dani naki, so nake kawai na fita na fada musu ni ba mayya bace, so nake in ji sun ce Khadijah wasa nake muke miki ke ba mayya bace. Kubcewa nayi na nufi
Chapter 41 · 0% Book details