← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 48

Sashe 45

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wattpad @ouummey Ouummey 15 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Fifteen _ ____________ ____________ Zuba mata ido kawai Falmata tayi tana kallo ta rasa me za tace, she's totally speechless da wannan aikin na Farida, ta sani su din sun dade da zamar wa juna yan uwa, sun fi karfin a kira su aminai balle kuma kawaye, matakin alakar su ya koma tamkar blood relatives sedai bata san har haka Farida ke matukar kaunar ta ba se yau. A hankali ta kuma juya katin hannun ta wanda ba komai bane face passport, kana ta Kuma maida duban ta kan Farida da ita ma take bin falmatan da ido "Dan Allah maimaita min me kika ce Farida". "Wani abu na fada na daban ne?, Nace ga shi nan dan ki ya gama yi miki komai da ya kamata na tafiyar ki India, kuma insha Allah jibi jirgin ku ze tashi ke da harira saboda ta kula dake ni kin ga baze yiwu in bar su Hassana su kadai ba ga kuma Business din mu, amma tare zaku je da dan naki ya daidaita komai sannan ya dawo, nima kuma kafin ku dawo din zan zo dan jira nake ayi hutu su tafi gidan yayan nasu, a cikin wannan maganar me ne baki fahimta ba?". Fashewa Falmata tayi da kuka, kukan farin ciki da kuma takaici at the same time, cikin muryan kukan take magana ma Farida "Tun da muka taso da ke ban taba jin wai bani da dan uwa ko yar uwa ba a duniya saboda kin cike ko wane gurbi Farida, duk abinda kika san ina so yi kike kafin in furta, kome zan bukata aje wa kike kafin na ambata, ban san dame zan saka Miki ba Farida, ban san me zan Miki ba in biya ki, a kullum roko na Allah ya kara miki budi da daukaka, Allah ya jikan iyayen mu in basa raye, Allah y raya Miki zuri'a yasa masu amfani ne, Allah kuma ya bar ni dake har karshen nunfashi na. Yanzu dai dubi Alhaji da nake karkashin sa, hakkin neman lafiya ta ke rataye a wuyan sa amma ya nuna lafiyar tawa bata gaban sa, ya tattara ya zuba min ido yaki yin wani hobbasa kan neman lafiya ta bayan babu rashi balle kuntata a tare dashi face zallar son zuciya da rashin adalci, b azan yi masa mummunan fata ba Farida amma tabbas da sannu se hakki na ya kama Alhaji in har ya zalunce ni". Kwalla Hajiya Farida ta shiga gogewa tana duban Falmata emotionally, "Ni ya kamata in Miki wannan addu'ar Falmata, ke din macece me kyakkyawar zuciya, ba ni na fara miki alkhairi ba halaccin saka alkhairi da alkhairi kawai nayi, kome Hammad ya zama a yau kin san dalilin ki ne?, Ko wace daukaka Hammad ze samu a rayuwar sa kin san kece jigo, ban da kuma tarin alkhairan ki gare mu tun Alhaji na da rai, Falmata kin so ni tun ina abin ki da gudu wajen jama'a, kin kusance ni yayinda kowa ke gudu na, kin tallafe ni lokacin da na rasa wani mataimaki, shin in ban Saka alkhairi ba me kike so a kira ni, balle kuma ni ina miki kallon yar uwa ce da muka fito daga cikin mahaifa daya, ko kin manta kece.........". Da sauri Falmata ta sa hannu kan bakin Farida tana girgiza mata kai hakan yasa Farida ta cire hannun daga bakin ta "In har ba kya san in tuna Miki to ki bar maganar dan in ance za'a ayi tone tone to kuwa kece kika yi sadaukarwar, ni kwatanta wa kawai nake, shi kuma Alhaji kamar yadda kika fada Allah ze Miki sakayya tabbas hakane, a da nayi niyyar in kin tafi can India nikuwa in shiga in fita har se na rama miki abin da aka miki sedai yanzu tsakani na ga Allah na fasa na bar shi da Allahn kamar yadda kika fada, ina kuma fatan ace an yi aikin nan cikin nasara". "Allah yasa Farida, in har kuwa akayi Nasara ki rubuta ki aje se na rabu da auren Usman domin kuwa bashi da wani amfani gare ni ta kowace fuska". "Allah ya kai mu, nidai fatana a dace in ga kin dawo gare ni lafiya lau, wannan shi ze samar min da kwanciyar hankali da nutsuwa". "Allah ya yarda, in Kuma bani da rabo...". Wani irin atuwar harara da Farida ta balla mata yasa bata karasa a binda zata fada ba ta kyalkyale da dariya tana dagewa Faridan gira cikin tsokana lamarin da yasa suka tuna baya su ka kuma sake darawa sosai... ____________ "Yaaya na fadawa Haanah ai kar ace za'a sama min mata a bar ni in zaba da kaina". Cikin son kwantar masa da hankali ta yadda ze amince wa kudirin ta ta shiga yi masa bayani "Kar ka damu kan ka Ibrahim, duk abin da za'a bukata a wajen mace Saratu na dashi, halin ta kuwa base na ce maka komai b adan kasan daga gidan d take, fatana kawai amincewar ka dan ba zan maka dole ba". "Amma yaya bakya tsoron a maimaita yar gidan jiya?". Da sauri ta shiga girgiza kai "Insha Allah ba abinda ze faru, bana fatan in maimaita kuskuren da nayi a baya shiyasa ma ban yi maka magana ba se da naji t bakin ita Rahinatun kuma alhamdillah tayi na'am dan yadda take walwala ya shaida min tana farin ciki da lamarin". Shiru Dada yayi dan daga jin yadda Hajiya Yaaya ta ambaci sunan sa Ibrahim kai tsaye yasan ta kai makura wajen son hadin nan ta yadda komai daze fada ba zata gane ba duk kuwa da tace wai amincewar sa take nema dan haka se ya shafawa kan sa lafiya kawai "Shikenan Yaaya, Allah ya sa hakan yafi alkhairi". "Ameen, ko kai fa, insha Allah wannan karon se mun ce gwara da akayi". Shidai be Kuma cewa komai ba har ta gama maganganun ta ya mata sallama ya fice, sedai fa a fili yake ya amsa mata ne kawai dan ba yadda ze yi dan ya kasa boye hakan a ransa, sanadin bacin da ran sa yayi ranar a gidan ya bar su Haanah suka kwana abinda ba ya iyawa se an kai ruwa rana dashi, jikin Hajiya Yaaya yayi sanyi ganin hakan se dai kuma wani bangaren zuciyar ta na fada mata ta share shi da sannu da kan sa ze dawo yana gode mata. To abu kamar wasa karamar magana na neman zama babba dan kuwa sati biyu kenan babu Dada babu labarin shi, shi be zo gaishe da Yaaya ba kuma be zo dibar su Meerah ba, a kuma tsukin lokacin har an yi maganar sa da Rahinatu an karbi komai na aure in da saura kwana biyar a daura kasancewar ta bazawara. Ba wanda ya kuma ganin Dada se ranar daurin aure wanda shima ya je ne dan kar ya kunya ta mahaifiyar sa cikin jama'a, haka yabi dangin amarya Rahinatu da ke ta masa barka da zuwa dan cewa Yaaya tayi wai yayi tafiya. A ranar amarya ta tare inda Yaaya ta rike su Haanah wai zasu yi mata sati in da a fakaice ta bawa Dada da amaryar sa damar sakewa ne, dan a ganin ta yaran zasu takura su sedai bata san tayi wa amarya bukulu bane dan kuwa Dada tun da aka kai amaryar be kuma komawa gidan ba se bayan sati shima se da Haanah ta kira shi a waya cewar sun koma gida. ___________ Wata daya kenan da kwana biyu da fara aikin mu yau, shirin da muka yi yau na musamman ne dan tsawon lokacin da muke ma'aikatan yau din ne zamu fara ganawa da shugaban mu gaba daya don haka kowa ka gani cikin shiri yake tun bare da muka sami labarin he's a non nonsense Man, he's very strict and concentrated kan aikin sa. Moroccon gown ce a jikina light purple in color se dark purple veil da nayi using, jaka na da takalmi duk dark purple, a rayuwa ta ina son purple dan lokacin da ina secondary school da miss purple ake nicknaming dina. Gaban mota na hakim ce Salees ya shiga owner's corner ya tuka mu muka bar gidan zuwa ma'aikata, ko ina was very very neat though kullum gurin is neat but na yau is extra + special neat, hatta flowers an yi trimming din su t a good level ta yadda suke bad sha'awa and the silence of the environment is just so wow. Muna fita daga mota muka rabu kowa yayi bangaren sa dan office din Salees na admin block ne ni kuma nawa na bangaren normal offices ne, se da na gama arranging table dina tare da kara extra scents sannan na zauna na fara aiki cikin nutsuwa. Karfe tara daidai aka hau knocking kofa ta, still working na amsa tare da bada izinin shigowa idanu na kafe kan screen din system, sassanyan kamshi me shiga cikin gabban jiki suna kassara su ne ya fara kaiwa hanci na ziyara kafin kuma in ji gaba ki daya iskan da nake shaka ya zama shi, a hankali na dago kai na na sauke kan being din da na tabbatar shi ya kwankwasa kofa ya kuma shigo. Kan kyakkyawar fuskar sa ma'abociyar haiba, tarin kamala da matukar kwarjini na sauke idanuna, fatar sa wata irin kala ce me daukar hankali, ita ba fara ba haka kuma ba za'a ce baka ba, manyan idanu ke gare sa da ya ya rage musu girma ta hanyar lumshe su, hancin sa dogo ne zit yayinda bakin sa yake nan madaidaici da ya dace da
Chapter 45 · 0% Book details