Sashe 47
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na dakata daga kokarin cire kayan da nake yi na zuba masa ido dan nasan akwai Magana a bakin sa. "Shin a zuciyar ki babu imanin da zaki ji tausayin wannan dan jaririn da be san komai ba a duniya, me ye hadin sa da fadan ku da mahaifiyar sa balle kice zaki huce a kan sa, shin Khadijah ko dan ni be kamata ki kyale yaron nan ba ya huta, eye". Gaba daya na daburce na kasa accessing inda maganganun sa suka nufa, to cut the drama short se na fada masa kawai "Ban fahimci zancen ka ba, nayi wani abu ne? Wane yaron kuma kake magana ?'. "Dan Allah ki daina wannan pretending din naki alhalin na san kin san kan me nake magana, a rayuwar ki ki rasa wa zaki cutar se jina na saboda duniya babu amana, is okay bari in fito Miki a mutum ki sakar min kurwar yaro da kika kama dan ina bukatar ganin sa a raye, in zaki yi kwadayin ki kar ki kuma sauke idanun ki kan yayana". Yanayin da na shiga alokacin baze bayyanu ba dan kasa magana nayi, baki na da zuciya ta suka yi min nauyi se idanu na da suke zubar hawaye Masu tsananin radadi da azaba. Ko a jikin Salees se ma wani uban tsaki da ya ja yana nuna ni da yatsa "Bar ganin ina cewa ina son ki a kan yayana na sha fada Miki zan iya komai, tun muna mu biyu ki saki yaron nan ya mike, na baki awa biyu zan je na dawo, wallahi in baki sake shi na se kin hadu da mafi munin tozarci dan se na tabbatar na sanar da duniya wace ce ke bakar muguwa, green snake under green grass, kina zaluntar mutane da wannan innocent fuskan da kike displaying alhalin bakar kumurci ce ke, banda kaddara me ze hada rayuwa ta da taki, wallahi i curse the day I met you". Da kyar na iya daga kai na kalli lokaci wanda ya nuna min na ci awa daya da mintuna cikin awanni biyun da Salees ya diba min, hannu na karkarwa na janyo waya ta daga jaka na shiga call logs dina, akan number Ummi na tsaida idanu na kafin na danna mata kira, bata dade tana ringing ba kuwa ta dauka da sallama cikin dattijuwar muryar ta kamar yadda ta saba "Ummi kizo zan mutu, zasu kashe ni Ummi dan Allah kizo, innalillahi wa inna ilaihi rajiun". Abinda na dinga maimaita wa kenan wanda ya tashi hankalin Ummi, ina ji tana kiran suna na amma na kasa amsa wa hakan yasa ta kashe wayar, kifa wa nayi kan bed din Ina sauke wani irin numfashi da duk wanda yaji yasan ba lafiya ba, kwakwalwa ta ta daina tunani ta tushe, kaina yayi wani dummm. Ina nan a haka Salees ya dawo, a lokacin kuwa tuni Amir ya bar duniya domin a yadda naji kururuwar Mariya da yan uwan ta ko awa da fitar Salees ba'a yi ba lokacin, irin yadda take fadar ta shiga uku ta lalace na kashe mata da shine ya shaida min ya rasu, tun lokacin da naji haka na tashi na kulle kofa ta na koma na zauna ina jiran tsammani, ganin hakan ba ze min ba ne yasa na kira Ummi na. Kamar sun manta dani ba wanda ya kuma bi ta kaina aka shiga kokarin mika Amir gidan sa na gaskiya, se bayan an kai shi an dawo sannan Salees yayi lokaci na, irin yadda yake dukan kofar yana kiran suna na tare da zagi da munanan kalamai yasa gidan ya rikice, wanda basu san abinda ke faruwa ba ma aka dinga tsegunta musu, ni kuwa hankalin tashe ta ciki na daga kai na dubi agogo se naga ko awa uku ma ba'a yi ba da kiran Ummi na, alhalin tafiyar awanni goma sha biyu ce daga garin Darma zuwa Bakwarni, so se na saddakar dan nasan kafin su zo maybe sedai gawata dan yadda Salees ke dukan kofar ya na tabbatar min se ya kashe ni abin ba magana, ga can kuma taron mata makwabta da suka shisshigo suma suna fadin a fito da ni se sun yi maganin na. A firgice na mike tsaye lokacin da Salees ya sami nasarar balle kofar dakin, yadda ya koma kamar wani mahaukacin zaki shine y sake rudar dani na fara girgiza masa kai ganin yana nufo ni "Na rantse da girman Allah Salees ni ba mayya bace ban kashe maka da ba, ka kawo Kur'ani ma dafa wallahi bani na kashe shi ba". Ina Salees da alama baya ma fahimtar me nake cewa dan wani irin shaka yayi min kamar me shirin raba ni da duniya, take na fara kakari idanu na na juye na shiga kokarin fisge kai na amma na kasa, a yadda nake sha e a hannun sa ya shiga kashe fuska ta da maruka yana zagi ta uwa ta uba, hanci da baki na suka fashe suka dinga jini amma bawan Allahn nan be yi imanin bari na ba, can sama sama nake jin wasu muryoyi na fadin ya sake ni kar ya kashe ni sedai ban tantance na waye ba na sume a hannun sa. _____________ Ko da ta suma be fasa dukan ya ba seda kyar aka samu aka kwace ta a hannun sa ana fadin ya bari kar ya daukar wa kan sa masifa, ruwa me sanyi Hajiya Iya da basu dade da zuwa ba dan ma jirgi suka biyo tasa aka watsawa Khadijah dake kwance helplessly sedai ko motsi bata yi ba, ruwa cikin bokiti ya sa aka watsa min wannan karon amma duk a banza, a nan ne hankalin ta ya tashi dan tunanin shikenan Salees ya kashe ni shima za'a kashe shi dan tafi kowa sanin dangin Khadijah ba zasu zuba ido ba, gashi in maganar kudi ake yi ko alfarma da hanya ne sa ba kusa ba su din ba sa'an danta bane. A daidai lokacin Ummi mahaifiyar khadeejah tare da yayyen ta maza biyu Hashim da Hashir da kuma autan su Hisham suka shigo, gaba daya hankalin Ummi a tashe yake ta yadda bata tsaya kallon kowa ba ta shiga nema na "Khadijah, Khadijah, ina Khadijahn take". Se kuma aka rasa wanda ze bata amsa inda tashin hankalin Hajiya Iya ya ninku haka ma Mariya, ga tashin hankalin rashin da ga kuma wani na miji yayi kisan kai, ja baya Ummi tayi jin kafar ta ta taka mutum ya kai duba se kuwa idanun ta suka sauka kan fuskar mafi soyuwar yar ta Khadijah, fuskar ta kumbura da shatin hannu haka kuma tayi kacal kaca da jini, wani irin juwa ce ta dibi Ummi yasa tayi taga taga zata fadi ya Hashim da shine babba kuma yafi kusa da ita ya maza ya tare ta, kwace wa tayi daga hannun sa ta kai tsugunne ta shiga tattaba fuskar Khadijah kana ta dube su cikin wani yanayi "Hashim, Hashir wannan khadeejah na ce ko, Deeje ce wannan ko?". Se lokacin suka lura dani suka kuma shiga rige rigen durkusawa waje na, cikin wani irin kururuwa Hashir ya mike yana bin jama'ar falon da kallo "Waye yayi mata haka, wane dan iskan me tsautsayin ne yayi laying filthy hands din sa kan kanwata, nace waye shi". Tsit falon aka rasa me magana kafin Salees cikin jin shima wani jan wuya ne ya furta maganganun da suka ja masa shiga wani hali "Ni ne nan na dake wannan asararriyar mayyar me fuska biyu, akwai abinda zaka iya....". Ko kafin ya karasa abinda yayi niyyar fada ya Hashir ya danke shi ya shiga sauke masa naushi a ko ina da hannun sa ya kai, idanun sa ya rufe kawai Khadijah yake gani a halin da take ciki da kuma zancen salees na cewa shi ya mata haka, se da ya Hashim da hisham suka rike shi da kyar dan Salees ya jigata ga kuma jin da mutanen falon ke yi, wani irin fincikewa ya Hashir ke yi yana fadin a bar shi ya koyawa Salees hankali be kuma tsaya ba seda Ummi ta daka masa tsawa "Kazo ka auke ya mu wuce asibiti su duba min in ta rasu ne". Ta fada directing to ya Hashir aikuwa ya taho da sauri tare da aukan ta gaba daya Hisham ya bi bayan shi ita kuma ta dubi ya Hashim "Kayi duk abinda ya dace kan shi dan ba zan bar digon jinin khadeejah ya zuba a kasa ba, ni da ku shege ka fasa wanda yace a zauna lafiya yaci uban shi, auren da ya ha a ma Allah ya tsine masa albarka". Ta fada tana kallon su Hajiya Iya ya fusace kana ta nufi kofar falon kafin kuma ta tsaya ta juyo "I'm coming back to you, zaku san kun taba jinin Ma'aruf Nasidi". Ta sa kai ta fice, shi kuwa ya Hisham tuni ya kira yan sanda, babu dadewa da fitan Ummi suka karaso aikuwa ya nuna musu Salees "Ku tafi dashi, kowa ye yazo kar ku yadda ku ba da bail din shi se da izinina, for now bani da lokaci amma daga baya zan shigo". Kamewa suka yi tare da sara masa suna fadin "Yes sir". Kana suka tattara Salees da be san inda kan sa yake ba suka watsa a mota suka fice ignoring all the kururuwar da Hajiya Iya da jama'ar ta ke yi. ________________ "Amma dai Aunty kin san bake na dafawa abincin nan ba, kalli yadda Miemie ke jin yunwa kuma kin hana maids su dafa komai yanzu kuma na dafa mata kin dauke, this isn't fair kin sani". Haanah ta fada rai bace sedai tana kallon Rahinatu dake amsa sunan kanwar maman su haka kuma matar baban su a yanzu, tsaki tayi tana cigaba da cin abincin wanda indomie ne da yaji hadi matuka, kifi kaman yayi magana a ciki ga kuma veggies da aka sa wanda ya sa abincin ya zama gwanin sha'awa. "To ki hana ni ci mana karamar mara kunya, yara duk an bata ku da iskanci da sangarta, kamar ku tula tula a gida amma an zube wasu masu aiki, abinci har kusan kala uku ake dafawa dan samun guri,