← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 48

Sashe 33

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

lallai sun tayar masa da hankali, hakan yasa tayi saurin dakatar da kukan ta ta shiga lallashin Meerah har tayi shiru, jakunkunan su ta dauka ta kai bedroom ta dawo taja hannun Meerahn zuwa bathroom din da ta ha a mata ruwan wanka, se da ta shiga wankan ita kuma ta fito mata da kayan sawa sannan ta fita. Kan kujera ta tadda shi zaune ya dafe kan sa ga Meemah a kan shi tana birgima da kuka, da gudu ta karasa tana kokarin daukar ta wanda se lokacin ya bude ido ya girgiza mata kai a hankali sannan ya dago Meemah daga jikin sa "Shhhhhh, is okay pretty". A hankali ta fara reducing volume din kukan ta har ta daina gaba daya se ajiyar zuciya da take yi a kai a kai "What's the problem pretty nah?". "Dada Maamah". Ta fada a shagwabe da muryan kuka, seda ya hade abin da ya tsaya masa a makoshi sannan ya iya daurewa ya kakaro wani busasshen murmushi yayi mata yana riko yan mitsi mitsin fingers din ta "Maamah tayi tafiya na fada Miki sweery". "Yaushe zata dawo?, Ni dai akai ni wajen ta". Ta fada tana neman fashewa da wani kukan sedai be bari ba yayi saurin tallafo habar ta "Look ta kusa dawowa, taje can aljanna ne fa, kin san aljanna akwai dad'i ko shiyasa Maamah bata dawo ba amma zata dawo". "Da gaske tana paradise Dada?". "Eh mana princess". "Yanzu tana can tana cin fruits din aljanna? Su Apple, banana, orange, pineapple, mango, strawberry and...se me ma Adda Haanah?". Ta fada directing the Question to Haanah, murmushi ta mata trying to karasa calming nata tare da dauke mata hankali "Eh mana dear, har dasu pawpaw fa, ga kuma su plantain and more". "Allah yasa zamu shiga aljanna irin na Maamah mu ma muje mu yi ta cin dadin mu". "Ameen pretty jeki Adda tayi Miki wanka a canja uniform ko". Tura baki tayi tare da girgiza kai "No Dada, yau kai zaka yi min, ka manta ka ce min zaka min wankan so biyar in naje school ban yi kuka ba, and kuma ban yin ba ko". Gyada mata kai yayi yana yake ya mike da ita dauke a jikin sa ya wuce dakin su Haanah na bin su a baya, ita ta ha a ruwan wankan shi kuma yayi mata, ana yi tana wasan ta tare da bashi labarai kai baka ce yar shekara uku da rabi bace, seda ya shirya ta cikin jeans da riga sannan ya nufi fita se kuwa ta daga murya tana magana irin wai ita tayi masa yadda ze ji ne tun da yayi nisa "Kar kace wa Maamah ta dawo da Dada, ka bar ta a paradise din ta tayi ta cin dadin ta amma ka fada mata kar ta cinye duka ta rage min". Wannan karon kam ba yake bane sahihiyar dariya yayi jin wani shirme amma se shima ya dan daga muryar sa kadan ya amsa mata da "Okay princess bari in je in fada mata". Da "toh Dada" ta amsa masa tana kwanciya kan dan Karamin gadon ta me kyau shi kuma ya fita, "Je ki sa a shirya mana table Meerah, lemme take a shower nima". "Okay Adda ". Ameerah ta fada itama tana ficewa saura Haanah da Meemah "Kar ki je ko ina ko da kuwa falo ne har se na fito, and kar ki fara yi min barna if not". Ta fada tana mata kallon gargadi sosai, cike fa biyayya ta gyada kan ta tana sa bmhannu cikin baki, shigewa bayin haanahytayi daure da towel yana saurin tayi tai wanka kafin Meemah ta bata matsala. _____ Yana shiga dakin sa ya fada ka bed hannun sa biyu dafe da kan sa da yake jin kamar ze rabe masa biyu, wani irin ciwo kan ke masa na tsananin damuwa da rashin bacci ga kuma yawan tunani dake addabar sa. Da kyar ya iya mika hannu ya bude drower ya debo maganin da be tsaya duba na mene bane ya afa a baki batare da ruwa ko wani abu ba ya shiga taunewa, dacin da ke ratsa bakin sa be kai wanda zuciyar sa ke masa ba, jiki ba kwari yasa hannun ya sake dafe kan yana rurruntse idanu "Me yasa Maryam, me ye laifi na, me muka yi miki da zafi da kika zabi yin nesa da mu bayan kin san muna tsananin bukatar ki?, Me yasa kika zabi barin yayan ki da mijin ki cikin wani hali?". Dan juyi yayi kadan a gadon se kuma ya cigaba "Na sani laifi na ne ko, shikenan am sorry Maryam, am really sorry but pls do believe that I so much love you Maryam, Ina matukar son ki mairo na, dan Allah ki dawo gare mu ko dan ya'yan mu, kin ga kullum se pretty tayi kukan ki, pls Maryam ". Kamar kuma wanda ya farka daga bacci se ya bude idanun sa wal wanda suka yi jajir kamar wanda jini ya kwanta "Astagfirillah, forgive me ya Allah, astagfirillah ". Se kuma ya sake dafe kai "Ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagees"....... Ouummey Ouummey 12 {5/11/2023 }
Chapter 33 · 0% Book details