Sashe 3
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
yadda zan masa, ni yadda yake yi ne ma yafi bani tsoro kalli kaga se wani mi ewa yake kamar ze shide". Ai oga se ya nemi ha e ran da ya an yi ya rasa ya kai hannu cike da hanzari ya karbi dan ya shiga riritawa, kamar abin shiri yaro maimakon yayi bacci ko yayi shiru ba se ma karawa kukan sa karfi da yayi hakan kuma ya sake dugunzuma hankalin uban duk yabi ya tashi dan Allah ya zuba mishi so da kawa zucin yaya, ko dan ya dade kafin ya same su ne?. Iya shaka na shaka domin dai a yau na gaza yiwa mariya da Salees uzuri, ba dan komai ba sedan saboda ba yau hakan ya fara faruwa ba, abin kamar ya zame mata sabon da take jin dadin sa ni kuma ya zama sabon da ke ta a zuciya ta da sani cikin acin rai. "Amma dai kasan wannan shiga hakki ne ko, yaya muna kwance kawai zaka bude wa wata daki hakan kuma duk be yi ba se an hana ni bacci, shin shima hutun nawa ya zama abin bakin ciki da hassada ne ko kuwa me?. Wani kallon Salees ya shiga yi min me kama da na mamaki ko kuwa na zallar takaici ne, kafin kuma yayi magana tayi caraf ta riga shi "Kiyi ha uri Khadijah, Amir ne ban san me ke damun sa ba kwana biyu, ko kuwa har ya gane uban sa ne oho, kinga har mun kwanta amma yaron yace be san zance ba kuka har na rasa yadda zanyi dashi shi yasa na kawo masa ko ze yi shiru dan mama tace yawan barin yaro yana kuka ba lallashi na jawo masa matsalar walwa da kuma ciwon zuciya". "Kinga dan Allah dakata ba dake nayi magana ba ki bari shi da nake dashi ya amsa min, zuma naaa da kai fa nake magana". A irin fusacen da Salees ya kalle ni abin seda ya girgiza ni dan kallo ne me shaida Allah ya soki bana kusa da ke "A sani na dai ke ba kurma bace kin ji me tace ko?". A yadda nakai geji nima hakuri na ya kare dan haka na bashi tawa amsar da fusatacciyar murya kamar yadda ya min "Shine nace ina bu atar sanin me kake nufi da ni ne dan wallahi sedai ko ta fita da yaron daga dakin nan ko ni na fita dan ba za'a dinga hanani bacci ana samun ciwo a banza ba". "Aikuwa sedai ke ki fita dan da dai dakin uban sa ne cikin gidan uban sa, kinga kuwa maganar a fitar dashi ma ai bata taso ba". Kuriii na masa da ido ina kallon sa yadda ya fadi abinda ya fa a hankali kwance, ban san me yasa murmushi ya zabi wanzuwa a fuska ta ba a lokacin duk kuwa da tsananin acin da rai na yayi "Amma dai kasan nima ina da gidan uba ba daga sama na fado ba ko Salees, so ba daga daki ba ko gidan kace in fice ma yanzu se in tafi ai". "Mtsww, Ni dai ban ce ki fita daga gida ba sedai in Kuma ke kika so, daki dai nace ki fita dan yaro na ba inda zeje, ke ban da ma rashin imani kina kallon irin kukan da yaron yake yi ko tausayin sa ba kiji ba balle mahaifiyar sa da duk hankalin ta ke tashe se wani soki burutsu kike yi, ko da yake ai baki san ya rainon da yake ba tun da baki ta a yi ba dole ki ga kamar karya ne". A wannan ga ar kam tuni idanu na suka tara ruwan bakin ciki, acin rai da kuma wani irin rauni dake tasowa tun daga can karkashin zuciya ta, ban kuma cewa komai ba na sauko daga gadon tare da arasawa inda na aje jakata na auka ina nufar hanyar fita daga dakin dauke da alwashi me girma cikin raina. Kan bed na fa a ina sakin kukan da nayi dauriyar ri ewa, wani irin kuka me fitar da sauti sosai jikina na rawa, kallo aya me imani da tausayi ze min yaji zuciyar sa ta motsa, Allah ya sani na dade da gajiya da zaman auren Salees, ba dan na daina son sa saba, ba dan bana son cigaba da rayuwa dashi ba, sai dan in aka cigaba da tafiya a haka lallai zuciya ta na gab da bugawa, in Kuma haka be faru ba na tabbata jinina se yayi yawan da saukowar sa se Allah, yanzu haka ina mamakin yadda ko yaushe nayi gwajin bp nake samun negative result dan a irin damuwar da nake ciki hawan jini shine cuta mafi kankanta da acin ran gidan Salees ka iya haifar min...................!. _*Ba zan gaji da fada muku ba haka ba zan gaji da tabbatar muku da ba gazawa ce ta sa Allah ya kaddare ku da rashin haihuwa ba face jarraba irin tasa da yake yi dan gwada karfin imanin duk wanda yace yayi imani, da zafi, da ciwo, da damuwa, da rauni amma in akaa daure tabbas rabon me girma ne kamar yadda Allah da kan sa yace yana kunyar matan da basu ta a haihuwa ba, Allah ya bada masu albarka inda rabo, in Kuma babu Allah ya azurta ku da dauriya da karfin iya jure wannan addara*_. Comment, share and follow. Ouummey Ouummey 02 {4/28/2023 }